ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 1 to 10

Ramatu kuwa ya tsaneta saboda rashin kirknta baitaba gaisheta ba ko zasu bangaji juna kuwa,shiyasa itama bata kaunarshi,duk inda ta zauna bata da mgana sai nashi dana mahafiyarshi,tasha kawo karansa wajen Goggo tama danta mgana baida tarbiya,sai dai Goggo tabata hakuri tace zatamai mgana,ranar data faramai mgana,cema goggo yayi”in batayi hankali ba duk randa ta shiga gonarshi sai ta zagaya anguwanan tana tsallen kwado..”dakuwa goggo tamai tana fadin”Tunda kasata nima zaka iya sakani kenan”Ko ajikinsa saima cema Goggo dayayi”Shi dai bai ce itaba,so karta sa kanta aciki..

Goggo macece mai fada,da shiga Abunda babu ruwanta,indai akan Da’ntane Aliyu,wanda takema kira da GADANGA,Tana da yawan barkwanci da son wasa,shiyasa ya maidata kakarsa,in kaga yadda ake daru tsakanin Gadanga da goggo sai cikinka ya kulle,in yadade baizo ba,tadinga kira tana fadin”Gadanga ko amun yaji ne? saboda kullum da tsiya suke rabuwa,Dakuma yazo ko kwana ba”ayi za”a tsiyace,goggo kenan da Aliyu gadanganta.

   Aliyu mutum ne,mai yawan karfin sha”awa shiyasa tunda ya fahimci haka,sai ya rika azumin litini da alhamis,Ammh duk da haka Abu yaci tura sai ya yanke hukuncin fara neman Aure,koda kuwa da yan”matan dake haukan Sonshi ne,yafara neman wata mufida yar kaduna ce,Soyayyarsu batayi nisa ba,suka rabu,sakamakon mahaifinta yace bazai bata shiba,saboda yayi bincike ba”asan asalin sa ba,abun bai dameshi ba ya rabu da ita,bayan ita ya nemi Ummi yar katsina ce  Itama itace ke mutuwar sonshi,ita harmgana tayi karfi,su kawu na Shirin zuwa komai ya rushe,bayan ita sai da akayi biyu,duk karatun dayane,Abun ya soma damunshi,duk matsayinshi ace anamai Wulakanci wajen neman Aure ana tozartashi kan baida uba,tun daganan ya watsar da komai ya cigaba da azuminsa kwatsam suka hadu da Ni”imatullahi akaduna wajen Dinner wani abokinsu shima Soja itakuma kawartace ai Tunda ni”ima ta hanga ido,taga Aliyu ta mutu akanshi,sai da tasan yadda tayi kafin tabar kaduna ta kafa gwannatinta.

Ni”imatullahi Ahmed Sidi na iya,diyace ga kwamishar yansanda na jahar gombe,kuma ya’ce daya tilo da iyayanta suka haifa,yar gatace ta karahe,wayayyiyace domin duka digeree dinta harzuwa master dinta ba A Nigeria tayima ba,yar kimanin Shekara ashirin da biyu aduniya,Fara gajera ammh itama babu laifi tana da kyau,Lokaci daya son Aliyu yayimata reshe harda rassa,tun bayabi takanta haryafara saboda yadda take gigitashi da salon soyayyarta,lokaci daya suka afkama juna da soyayyah mai zafi,ba”a dauki wani lokaci ba ya gabatar da kanshi wajen kwamishina zuwan farko duka iyayyan nata sun yaba da zabin diyar tasu ammh sai dai kash,kwamishina na bincikawa sai aka cemasa don makusa Captain Aliyu baida makusa,sai dai makusan guda dayane,rashin takamammen waye mahaifinshi,da kwamishina yaji haka yaso ya butse,ammh sai diyarsu ta nuna,in ba Aliyu ba sai mutuwa,dole aka yarjemai ya turomai magabantashi,kawu bala da mallam lawal sukaje,tun farkon mganar Auren sune jagoran komai har zuwa aka saka ranar Aurensu wata uku,murna wajen Ni”ima ba”a mgana,ta bangaren Aliyu dai laba”asa,donshi babu mai gane yanayinsa.

Da Azeeza taji lbrin Auren da Aliyu zaiyi sai da ta kwanta asibiti saboda firgici da damuwa,Duk iyayanta suka damu,kamar Azeema taji lbri,duk irin diban albarkan da Azizar take mata bata damu,tanajin yar”uwan nata har ranta sabanin ita Azizar datake zaune da Azeemar don bata da yarda zatayi ne,ammah har aranta take jin ta tsaneta batasan dalili ba,kodon hudubar mahaifiyarta akanta ne,ohoabunda kawai tasani bata ma kaunar ganin Azeema cikin Farinciki tafiso ita da uwarta suyi farinciki,itakuma ta dauwama cikin kunci,ayanzu haka shekarun Azeema 20 ayayinda Azeeza take da 15 ammh dayake tana da girman jiki,in akace shekarunta kenan wasu ma basu yarda,dauka suke ita ke gaba da Azeemar.

Ganin gabatowar Biki yasa Aliyu yafara gyaran gidansu,kusan dai Aliyu bawani mai kudi bane,Baya da burin tara arziki,ko yau adinga lbrinsa,amtsayin shi wanine,shidai burinshi ya taimaki kasarsa da lafiyansa da kwazonsa,kodon watarana in ya mutu atuna dashi,yana da Rufin asiri daidai gwargwado,Saboda baidawani dawainiya akansa,goggo ce haryanzu kawu baidaina hidima dasu ba,hatta shi Aliyu,son duk kudadansa,suna kammalle abanki ne,gidan nasu dama dan madaidaicine mai yalwar dan tsakar gida gefe wajen zubda ruwa,sai Famfo,daganan yammah akwai wani daki,ciki daya,nan ne dakin Aliyun,sai daga gabas dakuna guda biyu,daya goggo naciki,daya kuma tana ijiye kayan Abinci da sauran karikice,yana tashi gyaran ya bude dakunan goggo ya hadesu waje daya yayi mata babban falo da Dakuna barci guda biyu da tailot yazubamata kayan more rayuwa sai daga waje yayi musu katon madafin girki,sai barayinsa,dayake buge dakin,yayi ya hade musu Falo da two bedroom da kichen da Bayi,saboda nan zasu fara zama kafin su wuce kaduna,Tsakar gidan ma yasa aka kankare,aka saka interlock,Daga wajen kuma aka fitar da garejin mota,saboda motarsa,baya ma zuwa da ita gomben,saboda ba wajen adanata,yafi hawa motar haya Abunshi,don shifa Babu ruwansa bai dauki Duniya da zafi ba,akayi fenti mai kyau da kayatarwa daga wajenma an gyarashi sosai,tundaga nesa kana hangoshi yana daukan ido..

Tunda biki ya matso yan bani na iya suka damu kwamishina da tsegumin Aliyu,har mgana takai ga kaninshi wanda zai bada Auren Ni”ima,tun kafin Daurin Aure yaso adakatar da mganar,ammh kwamishina yaki yarda saboda yadda mahaifiyar Ni”imar da rike wuta,saboda sanin yadda diyarsu ke mugun Son Aliyu,Ni”ima kuwa tayi rawan kafa,kamar mene,duk da danginta sukaje mata jere,suka dawo suna raina inda Aliyun zai ijeta,harda uwarsa,uwa uba harda anguwan suka raina,sunce ta yaku bayi ce,ma”ana ghetto area ce,Da fari Ni”ima tayima Aliyu mgana,ammh sai ya numata shidin bawani bane,in zata zauna dashi ahaka,Final,in kuma tanaganin tafi karfin nan,To door iz open babu lalle ba dole,shi bazai dau wannan Rainin ba,don baicemata shi wani ne,ba,Shi kawai Sojan Nigeria ne,mai bama kasarsa gudummmuwa.,Dole Ni”ima tai ta bama Aliyu hakuri,domin zaga zaga yayimata,dakyar tashawo kanshi,ya hakura,tasan halinshi sarai baida wasa,shiyasa take kafkafa dashi kada ta balloma kanta Ruwa.

Ranar Daurin aure kiran da Kanin kwamishina yayimai kenan kan su bazasu bada diyarsu,ga wanda baida cikakken Asali ba,Sai yaga Dangin Maihaifinsa,tukunnah inko basu,to sai dai yayi hakuri bazasu basu diyarsu ba,Kwamishina baida yadda zaiyi dashi,dole ya bashi goyon baya,wannan Shine musabbabin Abunda yafaru awajen Daurin Aure,da yadda Daurin Auren yakoma kan AZEEMA, da duk Abubuwan da suka biyo baya…

*Karshen Asalin Tushe*

*Yanzu muka Shiga gabar,ku biyoni don ji yazata kaya gadai gwarzo nan Captain Aliyu  Abdulnaseer Tambari buzu,dakuma zaratan matan Azeema,Azeeza,da Ni”imatullah..*

         #Comment,share and Vote..#

         #Janafty…#

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…,HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA???? Ladingo yar Mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

*NOT EDITED*????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button