ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 1 to 10

        *Chapter 6*

          

    Jabir ya dade dakin Goggo suna hira sai wajen 10:00pm na dare,Goggo taga Aliyu baida niyyar bude kofar shashensa,fitowa tayi da kanta ta isa har kofar shashen tahau bugawa tana fadin”Gadanga kazo,ka bude kofarnan..”kazo ka bude nace ko?goggo take fada cikin fada.

  Yana kwance akan Daya daga cikin kujerun Falo,inda Allah ya taimakeshi lokaci da”akazo za”a yima Ni”ima jeren kayanta,hanawa yayi,saboda bazama zasuyi anan dinba,cemusu yayi kada su damu,ko gidanshi na cikin barikin akwai komai,so no need su wahalar da kansu,dayake dama already ya rigaya daya gyara barayinsa nasa bayan ya kawatashi dakayan alatun more rayuwa.

  Yanajin Buga kofan Goggo,da maganart,ammh yayi mata banza,yana kwance dagashi sai boxers kadai,babu ko riga ajiknsa,gashin kirjinsa yayi kwance luf dashi,Idanunsa suna lumshe ne,ammah ba barci yake ba,Damuwa tareda bakinciki ke mukurkusan shi,shi yanzu bama ta Ni”ima yakeyi ba,ta makomar rayuwarshi yakeyi,”Waye Mahaifinsa?inda  gaske Goggo takeyi shi ba shege bane,to ina mahaifinsa da Danginsa suke? Tambayar da haryau bai samu mai amsamai ba.

Goggo jin Shuru ya sata matsa jikin tagan kofan tana fadin”wlh ko kazo ka budemin,ko in kira gardawa suzo su balle kofan,na shigo har cikin naci maka mutumci,tunda kan mace,gadanga zaka dinga min kyaluwa ina mgana..”Tafada tana kwafa,Ajiyar zuciya ya sauke kan ya mike jikinsa asanyaye,bude lumsassun idanunsa yayi,bansan sadda na Furta subhannallah ba,saboda yadda idanunsa,suka chanza launi,sunkoma red sosai,Jikinsa babu kwari yazo ya murza key din kofar ta bude,bai bi takan Goggo da jabir dake tsaye ba,ya juya yakoma cikin falon yazauna kan kujera,yana kauda kansa,Shigowa dakin Goggo tayi tana fadin”Gadanga..Gadanga..Gadanga..”Saunawa na kiraka..”

Ko dagowa baiyi ba,yace cikin husky voice dinsa”Wai ni Goggo don Allah menayi miki ne?kamata fa yayi ki tsausayamin na rasa,love of my life,ammh kinzo sai fada kikemin..”Yafada yana wani kyabe fuska kamar zai yi kuka,Jikin goggo ne yayi sanyi ta karisa gareshi tana fadin”Yo ai kaine gadanga wani lokacin da ban haushi,ai ni na dauka bazaka wani damu ba,duba da yadda mahaifinta ya tozartaku gaban dubban jama”a,wlh indai kana da zuciya bai kamata kaji dacin Abun ba..”tafada tana zama kusa dashi kansa ya dauka ya kwanta bisa cinyarta yana fadin”koma miye,goggo i Love her,duk da Abunda mahaifinta yayi i knowa Ni”ima tana cikin wani hali yanzu cuz she luv me goggo i swear she can do without me..”Yafada yana damke hannun goggon

Dungure masa kai tayi da dayan hannunta tana fadin”Wai ban hanaka min mgana da wannan yaren Nasaran ba,sai na fara cin kaniyarka tukunnah ko”Tafada tana yar dariya,bai tankata ba ganin haka yasa ta hausha  shafa kanshi tana fadin”karka damu kanka Kaji,Allah yabaka mace tagari saliha,na tabbatarmaka Azeema zata zemamaka sanyin idaniya nan gaba,mganar mahaifinka kuwa mucigaba da addu”an gadanga inda rabon sake haduwa,Allah zai hada,ammh ina ji ajikina,Abdulnaseer bai mutu ba yana nan Araye,Ammh inda yakene,ban sani ba,Allah shiya barma kansa sani..”Tafada idonta na cikowa da hawaye,mikewa Aliyu yayi yana kallon goggo kan ya saka hannu ya shafa fuskarta yana fadin”To goggo,in bai mutu ba,yana ina,? ko yan”uwanshi ba wanda zaki tuna,ko yataba fadamiki..”Shuru goggo tayi kan ta sauke ajiyar tana fadin”Gaskiya baitaba fadamin ba,sai dai yana yawan Ambatan Agadez domin yacema mallam ko abaya daga yankin ya fito,ammh kasan Agadaz ba karamin gari bane,kuma shekaru sunja,gaskiya mawuyanci Abune,agano wanda ya sanshi sakamakon babu wata shaida da zata bayyana hakan,..,”Tafada muryanta asanyaye.”

   mirmishin karfin hali yayi yana kallon jabir dake tsaye yana kallonsu cike da tsausayi,kauda kai yayi yana cije lips dinshi ganin haka goggo ta dafa kanshi tana fadin”Aahhh..Haba Aliyu gadanga kusar yaki,Soja mazan fama,ko filin daka asan takunka,makiya da Abokan gabama tsoronka suke,kaga Saurayi na mamanshi uhmm,kaga Ango Azeema ka..”Saurin mikewa yayi yana dariyan Dole jabir ya tayashi,hanyar bedroom dinsa yanufa yana fadin”Sai da safe Goggo,plz go and sleep,nasan kin gaji dayawa..”ya fada yana  fadawa bedroom din ransa bace,babu Abunda yabatamai rai sai kiransa da Angon Azeema da goggo tayi,saboda bacin rai kamar ya kunduma zagi,ammh sai ya tuna goggo ce,ita baikamata azageta ba,uwace,uwa kuma tanada matukar muhimmanci,balle tashi data kasance na mussaman ne.

  Goggo batai gaddama ba,ta mike tana ma jabir sai da safe,tasan ko banza ya sauko daga muguwar bakar zuciyar da yahau,barayinta takoma tana yan wakewakenta ko ajikinta,domin ita wannan Aure yayimata daidai,sai alokacin ma ta tuna da Azeemar wanda tun da rana tace mata zata gida,tayi wanka ta dawo ammh Shuru bata dawo ba,bata damu ba sanin halin Azeema da rashin son mutane da hayaniya yanzu haka Rashin sakewan yasata kin dawowa,alwala goggo tayi tazo ta kabbarta sallar,bayan ta sallame issha”i tayi shafa”i da Wuturi,bayan nan ta dukufa rokama Aliyu fatan nasarar rayuwa kafin ta gangaro,kan Allah yayima Aurensu da Azeema albaarka tadau tsawon lokaci tana addu’o’i kafin ta kwanta,zuciyarta fess.

Aliyu yana Shiga bedroom dinshi yafada wanka,ya dade aciki bayan ya Dauro alwala ya fito,yana daure da tawul akwankwansonsa,daya kuma yana kansa,yana tsane ruwa da jabir ya cikaro wanda yayi dare dare bisa lafiyayye gadon dayasha wani ubansu bedsheet,kallo daya yayimai ya kauda kai Aransa yana fadin”Dan iska,ba don Tsohon dan Sandan nan,yayimin cikas ba,ai da yanzu nine bisa gado na ina biyan ladan kudina..”Yafada yana wani Runtse ido,kamar yana Kallon Tanadin dayayima yau din.

Gaban Derressing mirrior din dake Dakin ya isa yana kokarin bude wani lotion na kamfanin OLIVE yana shafawa kallonsa Jabir yayi kafin yace”Hy Dude wai duk wannan Shariyan namiye ne? bafa ni bane kwamishina Ahmed Sidi na iya ba,balle ka huce akaina,kuma Dude wlh Seriously Azeemar dakake kumburi don Ka aureta,yasin tafi Ni”imar taka komai,kai infact ma itace matar Rufin asirinka,don ta rufamaka lokacin da Uban Ni”ima ya tona maka,so Ni banga Abunda damuwa in kayi duba da komai MUKADDARI NE..”yafada yana yar dariya,wani kallo Aliyu ya wurgamai ta madubi baice komai ba,ganin haka Jabir yakara cewa”am wlh Dude ta hadakomai dakake bukata wajen mace,i know kaima aikana ganin yarinya,so quiet da ita,gaskiya kana da sa”a Dude..”Wani Takaichi ya kulle Aliyu baisan sadda ya waigo yana fadin”Nagode Shehi jabiru da Tunatarwa,buh juz give me 5 minutes,..”yafada yana jan Side drower din dake gefen gado,ya fiddo da wani Memo da pen,ya yagi daya ya dora zai fara rubutu Jabir ya kallesa yace”Mezakayi…”ko kallonsa baiyi ba,yace”Sakinta zanyi…!kwalalo Ido jabir yayi kan yace”what are u mad..”?ka saketa,kai Dan iska ne..? yafada yana kama baki,wani dirty look Aliyu ya sakarmai kafin yace”yap,yo ai naga kafini bukatarta,Tunda har ka iya kwatanta tana Abun bukata na more rayuwa gata She iz quit ko?sai na sakar maka ita,tun kafin kafara tunanin binta da Aurena akanta..”yafada yana wani hade rai.

Tsaki jabir yaja kan yace”Buraouban ka,banza kawai sakarta manq,wazai hanaka..”yafada yana ballamai harara,dariyan yake Aliyu yayi kan yace”Kai ne Babban Da’n iska,in ba Da’n iska ba,gaban mijin mace ka hau suffanta ta,ai kai ne banza,ajawo gara kawai..”yafada yana wurgamai takardan da pen din afuska yana fadin”Take ur eyes away from my Wife,i Swear zan iya kashe mutum in yakara suffata Iyalina..yafada cikin kakkuasan murya,yana wani buga kafa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button