ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 1 to 10

Tsab suka cinye tuwon kafin su wanke hannuwansu,Baba nata santi yana yaba girkin Azeema yana fadin”Uhm,diyar Albarka ta iya girki fa,zan yima mijinki albishir da yagama yin dace indai ta barayin girki ne..”Dariya take,tana jin dadin yadda Babanta ke yabonta tashi tayi ta kwashe kwanunkan takai kichen,bakin rijiya ta nufa zata jawo ruwa ya kwalamata kira yana fadin”Bar zuba ruwanan Azeematu,na hanakin zuwa bakin rijiya da dare,maza ki bari ki zo ki zauna nan mgana zamu yi..”Yafada fuskarsa ba alaman wasa,ganin haka yasa ta ijiye gugan tazo tazauna kusa dashi tana fadin”Gani Baba..”kallonta yayi kafin yayi ajiyar zuciya yana fadin”Yanzu daga gidan Baba Ade nake tace na gaisheki..”Washe baki Azeema tayi tana fadin”Kawata kenan,ina amswa Baba meta baka kakawomin..? Yar dariya yayi yana fadin”Bata bada komai ba,sai gaisuwa,aike yakamata kije ki kaimata.”Daganan sukayi Shuru,Dan gyara zama Mallam Lawal yayi yana Fadin”Azeema…”Ta dago ta amsa Tana fadin”Na”am Baba..”Cigaba yayi da cewa’Kiyi hakuri Azeema nayi miki katsalandan na yanke hukunci batare da shawaranki ba,duk da ina da tabbancin Na Isa dake,kuma bazaki taba watsamin kasa a ido ba..”Dagowa tayi idonta ya ciko da kwallah,tace”Baba wacece ni agareka..”Yace’Ke diyatace…”Azeema tace”To meyasa kake cewa haka,Tun tasowata bansan kowa ba sai kai,tun bayan rasuwar mahaifiyata baka barni nayi maraici ba ka wahala dani,kayi hidima dani,niko wacece ni da bazan zama baiwa gareka ba Baba.!koda fansar dani kayi zuwa wata masaurata domin bauta Bazan bijiremaka ba,ballatana,don ka bada Aurena ga yaya captain Da ga Goggo wacce ta kasance makwafin uwa gareni,ashe ko in naki bin umarninka na zama butulu,kuma ban cika y’a ba..”Tafada tana fashewa da kuka.

Gabadaya jikin Mallam lawal yayi sanyi,tsausayi tare da kaunar yarsa,da girmama Kaifin hankalinta suka taru,sukaima yawa,dafa kanta yayi wanda ta cukwikwiyeshi cikin hijabi tana kuka yana fadin”Kiyi Shuru Azeema,dama nasan bazaki bijiremin ba,Tashi ki shiga daki ki kwanta Allah ya albarci rayuwarki,dana Aurenki,Allah kuma yajikan mahaifiyar fatima da Rahama..”Da Amin Amin Azeema take amsawa tana share hawaye.

  Inna Ramatu dake tsaye kofar dakinta tanajin duk Abunda suke fadi,taja wani dogon tsaki kan tace”mtsewwwww…Diyar so,an saka miki albarka,nikuma tawa wacce baka so ka tsinemata,dayake kwadayine,kazo kana lallabanta wlh mallam kaji tsoron Allah,ko fifinko dake nunawa kan ya’yanka Allah ya kamaka bazakaji dadi ba..”Ko kallonta baiyi Ba Azeema ta dago tana kallonta ranta na kuna ta shige daki tana fadin”Sai da safe Baba…”Allah ya tashemu lafiya..”yafada yana mike  kafarsa ko kallon Inna dake tsaye tana jijjiga jiki bai yi,ba don ya lura sam Ramatu bata darajasa a mtsayinshi na mijinta,ta riga Tagama Rainsa,so take kullum su dinga hayaniya makota naji,shiyasa yake banza da ita,intagaji ta wuce,tunda ita ba karya bace.

         #Commet,share, like and Vote..#

         #Janafty ce….#

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA .S. ZARIA(MMN USWAN)*

  

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

           *Chapter7*

   

Koda gari yawaye har sukaje massllaci suka dawo,Aliyu bai ko kalli barayin da Jabir yake ba,shima kuma bai tankasa ba,Suna dawo daga sallar asuba Aliyu ya shiga Hada kayansa cikin wata katuwar jakar baya,mai kalan Uniform dinsu na yaki,Jabir na kallonsa,ammh kanzil bai cemai ba,don ya lura sarautar tashi ta motsa,yana ji sanda Haisam yakiraasa suna gulmansa suna dariya,ammh sakamakon yau baya cikin mood din,nunamusu yayi baima san dashi sukeyi ba,ballatana ya tankamusu.

Misalin karfe 8:00am na safe,Wayarsa tana kara tana neman Dauki,ammh Da Aliyu ya dago yagamai kiran,sai ya kife wayar yana sakin Siririn tsaki,shi kadai Jabir yana kallonsa,yana so yagano waye ke kiran Aliyun ammh ya kasa ganowa,mikewa yayi daga kan gado yana mika yace”Dude wai shirin Tafiya ina kakeyi ne?Ko kallonsa Aliyu bai yi ba,illa kokarin zuke zip din jakar dayakeyi Dariya Jabir yayi yana fadin’Haba Dude don Allah warware jaka kada muje bariki ayi damu,kai zaka tsaya shan amarci sai nan da 2weeks zaka dawo bakin aiki..”

Wani Banzan Kallo Aliyu yayimai kafin yace”Ubanka ne zai sha Amarci ko? “Yafada cike da fusata baya jabir ya matsa yana fadin”Ah..No..No maida wukar daga Taimako Allah bada sa”a..”Kada kai Aliyu yayi kafin yace”Better Tunda barikin ba gidan Uban mutum bane,sai ya hanani komawa..”rike baki Jabir yayi yana yar dariya,Shiko Aliyu Tailet yafada Fuskarsa ahade babu alamar fara”a ko kadan,jabir bai damu ba,cos inda sabo yaci ace ya saba da Kala kalan Fuskar Aliyu.

Yana Shigewa Tiolet din ya Sufa zuwa ga wayarsa kirar iphone 9 yana Dauka Daidai kiran nakara shigowa *MUNEERA* batare dawani Tunani ba yadaga kiran ajiyar zuciya Muneera ta sauke kan tace”Hello Captain…”

  

Kansa Jabir ya shafa kan yace”Ya is captain buh not Captain Aliyu am Captain Jabir how can i help u…”Da Sauri Ni”ima ta karbi wayan tana fadin”Jabir don Allah kamin rai,ka hadani da Sojana,wlh zan mutu in banji muryansa ba..”Tafada muryanta na rawa,cikin alaman jin jiki.

  Gyara tsayuwa yayi kafin yace”Am So srry Ni”ima bazan mezancen miki ba,buh u already know Aliyu in yayi inrin wannan kafewar to sai Allah saukowanshi,koda kuketa kira yana gani yaki picking yanzu ma he iz inside d toilet dat why ma na samu daman Daukan kiran,am srry to say buh Abbanki mai kyautama kanshi ba wlh..”Yafada yana cije baki kuka Ni”ima ta fashe dashi tana fadin”Oh ya Allah help me..Na shiga uku wlh zan iya mutuwa indai banji muryan Sojana ba”..Sai dai ko ki mutu…”Jabir yabata amsa Aranshi,yana yar dariya daidai lokacin da Aliyu ya fito daga tiolet daure da wani karamin Towel akugunsa,daya yana kansa yana tsane Ruwan dake diga daga kan nasa,yana ganin jabir da wayansa,ya tsaya cak yana jifansa da wani dirty look,shiko yana ganin haka,sai yayi hanzarin bude wayar a sepeaker,daidai lokacin da Muneera ta amshi wayar tana fadin

  “Don Allah jabir do ur best wlh Sweetheart she seriously Sick yanzu haka muna Hopt tun jiya dataji Abunda ya faru,ta samu heartfailure,kabashi hakuri is not her Fuilt,yazo ya ganta ya lallasheta ko tabar kuka,wlh Tun data farfado take ta kuka tana kiran Sunansa plz Jabir…”Jabir yayi kasake yana bin Aliyu da kallo wanda ke rollin din idonsa yana wani cije baki,takowa yayi sai da yakusa gabda jabir kana yace da dan karfi..”Plz Dude tell dem to stay away From me…”Yafada muryansa na rawa,kallonsa jabir yayi sai yaga idonsa yayi ja,jijiyoyin kansa sun mike,Ajiyar zuciya ya sauke kan yace”Kunji ko,plz karku sake kira,sai na nemeku don Allah,kubarsa Abun ya sakesa tukunnah,Ni”ima may Allah (SWA) Shifa u Ameen…”Yana fadin haka ya datse kiran,dagachan bangaren Ni’ima tanajin muryan Aliyu sanda yake mgana,batama gama jin Abunda jabir ke fadi ba,takara tsananta kukanta,kallonta Muneera tayi kan tace”Don Allah Sweetheart kibar kukannan hakanan,kiduba halin dakike ciki,in Mami tadawo ta tarar dake cikin wannan Halin u know bazata ji dadi bako? so plz Wipe ur tear don Allah ba karshen rayuwa ba kenan,kuma da yardan Allah zaki auri Aliyu..”Idonta jawur ta dago tana kallonta kafin tace”Are U sure…”Gyadamata kai Muneera tayi kafin tace”100%Sure Sweetheart…”Share hawayenta tayi kan takoma ta kwanta ta kurama Drip din da”ake sakamata ido tana kallon yadda yake diga sannu ahankali,lokaci daya ta runtse idonta kwallah na zubomata,ta rigaya data sani tayi bankwana da dukkan wani Farinciki Tunda Aliyu ya bar Rayuwarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button