ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 1 to 10

Suko Anasu barayin Jabir na yanke wayar yafada wanka,Shiko Aliyu agurguje ya Shirya cikin wasu riga da wando black and white,kafarsa ya sanya wani bakin takalmi booth,sai kansa ya sanya wata bakar p-cap,ya dau katuwar jakarsa ya rataya yana Daura agogonsa na kamfanin Rado baki ahannunsa,Jabir ya fito,ganin Aliyu atsaye yasa shima ya shirya agurguje,shima yayi shigan Riga da wando,ammh nasa Neavy blue ne,shima jakarsa ya rataya suka dumguma suka fito,makulli Aliyu ya sanya Ya rufe shashensa,suka fada barayin goggo wacce ke kichen tana kokarin hada musu Abun kari,taji sallamarsu Fitowa tayi tana amsawa fuskarta na bayyana farincikinta data ciki.

  Ganinsu tsatsaye kuma ga kaya yasa tatsaya Tsurus tana fadin”Lafiyanku naganku da wata uwayen jaka..”Dukawa Sukayi dukkansu Aliyu na fadin”Ina kwana goggo,zamu koma kaduna ne,bakin aiki..”Yafada yana sunkunyar dakai,karisowa tayi tazo tazauna kan daya daga cikin kujerun falo tana fadin'”Kai ku kalleni nan bani son iskanci,ina zaku yanzu da farar safiya,kamar ana koronku,ina fa madafi Tundazu ina kokarin hada muku Abun kari ne,wlh baku isa ba,bazaku barni dashi ba..”Tafada cikin fada,Mirmishi Jabir yayi yana mikewa yace”Kwantar da Hankalinki Goggonmu basai kin bata ranki ba,zamu ci kalacin dakike Shiryamana kafin mutafi,medame dame aka Tanadarmana..”Yafada yana zama kusa da ita.

Washe baki yayi tana fadin”Yauwa Dan Albarka Kunun Shinkafane Sai Fanke danake soya muku,akwai Ruwan Tea wanda yaji citta,sai ku hada dashi..”Tafada tana kallon Aliyu dake duke,Mikewa tayi ta isa garesa tana fadin”Taso taso Gadanga,bar damuwa hakanan,ban hanaku tafiya ba,ammh ku karya tafiya da yunwa babu kyau,tunda gida kuke ba daji ba..”Tana fadi tana rikosa,mikewa yayi yana kallo goggo kafin yace”Karki cikamin ciki goggo,nakaasa jagorantan Bataliyan yaki na gaba..”Sajensa ta shafa tana fadin”Da”n nema kaida yakamata sai sati na sama zaka koma,tunda kana cikin Hutun amarci ne”,bata rai yayi yana fadin”Soja baya Daukan Hutu goggo,koda yaushe burin sojan nageria kare dubban rayuwa daya rantsuwa wajen amsan kaki,saboda duk Abunda ya shafi kare hakkin kasata da al”ummata goggo bana jin son jiki a al”amarin…”,kansa ta dafa tana fadin”Nasara tana tare dakai Gadanga,insha Allahu sai kasarka tayi alfahari dakai kamar yadda take alfahari da Sardauna..”Amsamata yayi da Amin,kan sukarisa ta zaunar dashi kusa da jabir tana fadin”Bari na kawo muku kalacin.”Tafada tana fadawa kichen Jabir da Aliyu suka bita da kallon kauna da tsausayi.

Tana rawan jiki ta jera musu komai,basu ci da yawa ba,ammh goggo sai da ta dura musu kunun shimkafanan cikin wani karamin Flaks,sai Fanke ta zuba musu cikin wani karamar kula ta basu,tana fadin ko ahanya sukaji yunwa su tsaya su ci,amsa sukayi jabir na dariya,shiko uban gayyar yasan hali mirmusawa kadai yayi,sallama suka mata,Aliyu yaba goggo 10k dakyar ta amsa,wai yaya yabata kudi,har waje ta rakosu Aliyu ya Shiga garejin ya fiddo musu da motarsa 4matic baka,Suna kokarim Shigane sai ga mallam lawal ya fito daga gida,da hanzari Aliyu ya dakata bayan ya saka jakarsa abayan motan ya nufi mallam lawal yana dan Sakin Fuskarshi yana zuwa kusa dashi ya rankwafa yana fadin”brka da safiya Baba.”Rikosa Mallam lawal yayi bakinsa washe yana fadin”Tashi Tashi gadanga,Lafiya kalau,ya katashi,yakuma kwanan goggonka..”Mikewa yayi yana fadin”Tana lafiya baba,dama zan wuce saboda ankira bakin aiki akwai wata bataliya da zan jagora zuwa yankinnan na zamfara ne,shine nakeson mu shiga kaduna da wuri..”Gyada kai mallam lawal yayi yana fadin”Eh gaskiya to Allah ya taimaka Allah ya doraku bisa kansu,kukuma Allah yayi musu albarka..”Da Amin Amin Aliyu ke amsawa kafin yamikama mallam lawal hannu sukayi musabaha,yana fadin”Zan Tafi baba,..Arrrm *AZEEMA* tacigaba da zuwa mkrantanta both islamiya da boko,in tana bukatar wani tashiga wajen goggo,Don Allah Baba ayi hakuri da yanayin aikinmu sai na dawo sai munsan Abunyi..”Girgixa kai mallam lawal yayi yana fadin'”Ah babu komai Aliyu Fatanmu Allah yabaku nasara,sai ka dawo..”Da haka suka rabu cikin mutumci,yana tsaye har motansu Aliyu ta bace Alayin,kafin ya fara share inda zai basa kayan gwarinsa,yana yi yana girgiza kai in ya tuna tijaran da Ramatu tayi yau da safe,Abun sam babu dadin ji.

    *********

*NIGER REPUBLIC*

  

  Awani babban masarautace dake yankin *AGADEZ* Da misalin karfe 3:00pm na silasailin dare ne lokacin adaidai lokacin acikin kayatattaciyar masaraurar wacce takwafa tarihin na tsawon shekaru hamsin da doriya ta mulkan yankin na agadez.,masauratace babba wacce take kunshe da tarihai masu dimbin yawa tunkam zuwan addinin musulunci,Yanzu da ilimi ya yawaita akasamu yan boko suka mulki masarautar ansamu chanje chanje masu dimbin yawa,ciki harda rushe masarautar zuwa na ginin zamani mai kayatarwaa,kana dumfaru masarautar gininta da yanayin tsarinta zai burgesa yakuma baka sha”awa,uwa uba yadda take da uban dakarin yaki da masu tsaronta,masaurautace babba mai cike da bayi da wadanda suka jibamceta.

A babban shashen dayafi kowani shashi girma da kyau da tsari Wanda ya kasance shashin Ranka ya dade maigirma sarki kenan,wanda yake kwance akan makeken wani mulmulallan gadonsa mai kyau da tsari,wanda yaji Shimfidu Na alfarma Adalin sarkin ne da kansa kwance yana barci kamar kullum mafarkin daya saba yine yau ma yakeyin irinshi na yau ma yaso ya bambamta dana koda yaushe domin Fuskar matar hartaso ta bayyana garesa sai kuma yayi Firgigit ya farka daga barcinsa nasa yana salati lokaci daya zufa na ketomai kota ko”ina,Gimbiya FASILA ce yau aturakar ta Sarki da hanzari ta mike tana kallonsa kan tace”Ranka ya dade Allah kara lafiya meya faru ne,naga ka mike afirgice kana salati..? tafada tana kunna hasken dakin wanda ya gauraye lokaci daya.

  Kallonta yayi baice komai ba,illah zuro kafafunsa dayayi ya sauka daga kan gadon ya zura wani takalmi mai gashi ya dumfaru wani dan daki da gefe,tabe baki tayi takoma ta kwanta aranta tana mamakin meke damun yallabai ne haka,duk kusan matan nasa ba wacce bata fuskartan wannan mafarkin nasa duk ranar girkinta,in baiyi wannan karon ba,wani zagoyowar zai faru,kuma ko kayi tambayan Duniyan  nam baya kulaki ballatana ya baki amsa,Tana kallonsa ya fito Fuskarsa da farin gashinsa na digan ruwa alamar alwarla ya dauro ko kallonta baiyi ba ya isa ga wani dan korido inda wani shimfidaddan cafet yake mai kyau da tsari gefe daya carbi ne,sai daga baya wani cabinet ne,mai dauke da qur”anai da sauran littafai,bai bata lokaci ba ya cire fararan kafafunsa cikin takalmin na sarauta ya isa ga cafet din ya daidai sahu ya tada sallar,sai da yayi raka”a goma sha uku kana ya sallame ya zauna yana lazimi tare yima Annabi salati,aransa yana fatan Allah ya bayyanasa komai miye yake so ya bayyanass masa cikin mafarki Aransa yanaji kamar wani nauyi ne,da hakkin akansa wanda ya rataya awuyansa shekara da shekaru baya saukewa domin da alamun matar dayake ganinta tana bukatarsa cikin mafarkin kuma Abunda yafi daure masa kai yaron dayake tare da ita,wnda kowani lokaci yaron yana so ya iso garesa ammh kuma nisa da tazaran dake tsakaninsu baya barinsu su iso garesu da zarar kuma haske ya bayyana garesa domin ganin Fuskarta sai ya farka daga mafarkin wanda ya dau tsawon shekaru Ashirin da biyar yanayinshi,dayake shi mutum ne mai riko da addini bai yarda da duba ba,babu abunda yasa akayimai ko masu fassaran mafarkin da Ummansa mai babban daki ta sanya ayimai hanata yayi,yace ta barma Allah koma miye Allah zai yayi duhu cikin haske.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button