ALIYU GADANGA Page 1 to 10

Arazane kawu bala yace”Haba Ranka yadade wani irin mgana ne,haka baya da uba daga sama ya fado,kaga mubar wannan mganar,adaura Auren Allahbarshi bayan angama sai muyi mgana..”Yafada cikin alamar roko,kani ga kwamishina yace”Sam wannan mgana bamai yuyu bane,bazamu bada Auren diyanmu ga bara gurbi ba,matukar wani daga halin mahaifinsa baizo ba,to an fasa Daura Auren kowa ya watse..'”Ai sai waje ya kaure da hayaniya tawagar Kawu bala sunata maganganu Mallam lawal ya rike kafadan bala alamar lallashi.
Kawu bala yakalli kwamishina yace”kar kayi haka Ranka ya dade ka duba girman jama”an daka tara,dawanda ni na tara,da wanda Shi yaron ya tara,kabari adaura auren nayimaka alqawarin koma miye daga baya sai muyi mgana,don Allah na rokeka…”Yafada harda hada hannu,ammh sai kwamishina ya girgiza kai ya mike,liman dake zaune yana fadin”Subhannallah wai mike Faruwane,kada kubari Shedan yayi Tasiri akanku,yahanaku kullah Alheri mana..”Ammh ina Tuni kwamishina da kaninsa da nasu tawagan sun Fice daga massllacin kawu bala ya bisu da kallo kamar ya zubda da kwallah,babu wanda yake Tunani sai *SUWAIBA* yazataji in tasamu wannan lbrin ta Aliyu mai sauki ne.
Tuni Su Jabir dake zaune suka fara Fahimtar Abunda ke faruwa,tun sadda su kwamishina suka mike,arazane Haisam ke kallon Aliyu wanda yayimai kuri da ido yana kallonsa kafin yace cikin wata murya mai cike da amon tashin hankali..’Haisam meke Faruwane,fata dai ba Abunda nakeji bane ko? yafada yana kafesa da ido,bai samu zarafin bashi amsa ba kawu bala ya kalli jabir yace”Ku sanar da jama”a anfasa Daurin Aure,kowa yakama gabansa…”
DAM!zuciyar Aliyu ta buga Kuri yayima kawu da ido kafin yayi mgana Mallam lawal bature yace”A”a bala,baza’a yi Saurin sanar da haka ba,Duk wanda yake kokarin tonama wani asiri Allah bazai barshi ba,yanzu za”a Daurama Aliyu Aure anan wajen Insha Allahu..”Dukkansu ido suka samai kafin Kawu bala yace”To dawa,lawal?kana ganin fa wulakancin dasukayi mana..?”
Mallam lawal yace yana kallon Aliyu kai tsaye yace” Da..,Da.. *AZEEMA* za”a Daura in ka yarda,saboda babu dadi atara wanan jama”ar kuma ace musu anfasa Daurin Aure,hakan bai dace ba,shiya…’.Zuruf Kawu bala ya mike kafin ya damko hannun lawal yana fadin’Ku zauna mu dawo..”Yafada yana kallon jabir,ficewa sukayi zuwa kofar mallacin,nan suka ga yadda rabin mutanen suka watse,ammh wasu sun tsaya sai sunga kwal uwar daka,gefe kawu bala yajasa kafin ya ciro wayarsa yana fadin”bari na kira Suwaiba..’yafada daidai lokacin dayake kiran ta.
*************
Biki yayi biki,gida babu masaka tsinke,tana zaune *MADINA* ta shigo da waya ahannunta tana fadin” *GOGGO* gashi Daddy ne ke kiranki..”amsa goggo tayi tana fadin”Kila An Daura auren ne,kai Allah na godemaka gadanga yazama magidanci yau..”Tafada tana dariya lokaci daya tana daukan kiran da fadin”Assalamu Alaikum yaya…”dagachan bangaren ya amsa mata da fadin”,Suwaiba…”Yadda yakira sunan natane,sai da gabanta ya fadi ta amsa bakinta na rawa kafin tace”Lafiya kuwa yaya? kowani Abun ne ya samu gadanga…? ajiyar zuciya ya sauke kan ya cigaba da zayyanamata Abunda ya faru cikin sauri yace”Za”a Daura mai Aure da AZEEMA diyar mallam lawal yan….”KU DAURA YAYA YANZU NAN DON ALLAH….”Ta fada cikin kuka kafin tacigaba da cewa cikin Fushi..”Ni dana ba Shege bane, yana da tarbiyar da diyarsu bata dashi,ku gudanar da komai haka Allah ya rubutu…”Tana gama fadin haka ta katse wayan tana share kwallah.
Basu tsaya bata lokaci ba,suka koma cikin massllacin sukayi mgana da liman cikin minti kadan Kawu bala ya fito da sadaki ya mika ma liman yana fadin'”Kayima Azeema walicci..”Babu bata lokaci akace amatso za”a Daura Aure,kafin kace me Tuni an Daura Auren *CAPTAIN ALIYU ABDULNASSER TAMBARI BUZU DA AZEEMA LAWAL BATURE* Akan sadaki mafi daraja,nan da nan maroka suka fara Shedan suna fadin”Allah kenan baya tsallake Abun da ya rubuta,Daurin Aure dai ya chanza,maimakon Ni”imatullahi yanzu Azeema ce mai sa”a Domin itace ta kasance mata ga Dan matashin Sojan,Allah kenan komai ya faru da saninka,kuma da izininka..”Suke fada suna shela,tuni waje ya hautsine kowa tambaya fal cikinsa,tun lokacin da tawagar kwamishina suka wuce batare da Dan Daura aure ba.
Captain Aliyu dayayi mutuwar zaune kansa aduke har akagama Daurin Aure bai dago ba,sai jabir ne,ya riko kafadansa yana fadin”Captain kayi ha…”Bai karisa ba yadago kansa idanunsa sun chanza kala jijiyoyin kansa sun Fito radau yace” Sunce baza su bani ba ko? bani da uba ,kamar yadda suke fadi…”Yafada kamar zai kifa saboda yadda kirjinsa ke tasawa,bai kara mgana ba,ya mike da sassarfa ya fice daga masallacin Da hanzari Haisam da jabir suka rufamai baya,yana Fitowa yan jarida sukayi cha suna watsamai tambayoyi wanda suke kara tunzurashi ai yana daga dago kansa ya daka musu tsawa yana fadin”Get Way from my Side…”Yafada afusace yana buga kafa kamar afilin daga,kamar mazari haka sukayi baya suna rawan jiki sojojin dake wajen da hanzari suka kame,ko kallonsu baiyi ba,ya nufi motarsu da suka zo acikinta Ya fada,ko kafin su Haisam su kariso yajata ya fice da wajen dawani mahaukacin gudu,dafe kai Jabir yayi yana fadin”Innalillahi..kada fa Aliyu ya kashe kansa,in yayi irin wannan Fushin fa sai Allah..”Haisam ya damke hannuwansa duka akirji yana fadin”Allah kawai ya kiyaye,ammh ina tsoron Fushin Aliyu kam..”Juyawa sukayi suka koma cikin wajen suna gaisawa da bakin da suka tara,haka suma su kawu bala cikin Farinciki da mura suke gaisawa da mutane suna musu godiya kamar babu Abunda yafaru,yan jaridu ko Haisam ya sallame su dole suka tafi,tunda bazasu samu Abunda sukaso suji ba.
Cikin wani Fushi yake Driving din Allah ne yakaisa *KAGARAWAL* lafiya Da wani banzan taka burki yafaka motar akofar gidansu dake cike da jama”a yan biki cikin Fushi da Wani karfi ya ture murfin motar ya fito yafara taku zuwa cikin gidan jama”an dake waje suka bisa da kallo,Azeema dake kokarin Fitowa zata koma gida,batama kalli gabanta ba,sai ji tayi anyi baya da ita an maidata zauren gidan,Cikin Tsoro Ta bude baki zata yanka ihu ya dakamata tsawa”Ke Shout up…”yafada yana zare mata ido,jin muryansa yasa jikinta yafara zikiri Bude ido tayi tana binsa da kallo yadda naman kirjinsa ke dagawa,ai sai Azeema taji wani Fitsari na neman kubcemata saboda tsoro cikin Tsawa yace”Ina Goggo take…? Dakyar bakinta na rawa tace”Ta..Tana..dakinta…”Tafada wasu hawaye sun zubomata sakinta yayi bayan ya tureta gefe ya wuce fuu kamar kububuwa.,Saura kadan tafadi sai ta ta dafa bango kafin ta tsaya da kafarta,tana ganin ya wuce ta rumtuma da gudu ta fice daga gidan,tana sauke ajiyar zuciya domin daman Duk duniya babu wanda take tsoro irin *YAYA CAPTAIN*
Shiko yana Shiga gidan akayimai chaa ana fadin’Ga angon Ni’imatullahi nan,gadanga kusar yaki,Ba gaba da gaba ba,ko ta bayan sai gwarzo…”Wani haushi ya tokaresa bai bi takansu ba yafada dakin yana fadin”Goggo..Goggo..”Goggo dake cikin daki tayo falo tana fadin”Gani Gadanga lafiyanka kakemin wannan kiran? tafada idanunta sun kada alaman tasha kuka,baiyi wata wata ba,kawai ya zube gabanta yana fadin”Don Allah goggo kifadamin wayeni?,da gaske nidin Shege ne bani da uba,goggo don Allah ki fadamin kota haramtattaciyar hanya kika same….”KAYI MIN SHURU ALI…”Goggo ta katseshi rai bace tana huci kallonta yake yaga yadda ruwan hawaye ke zubomata tace”Ka tashi kafice kabani waje..”Tafada tana nunamai kofa,Tsam yayi yana kallon goggo kan yace”ammh gogggo…’Ka ficemin daa gani nace ko Ali..”Tafada cikin wani Fushin,Baiyi gaddama ba,ya mike tsam yana wani mazari kafin ya kalli goggo kamar zaiyi mgana sai kuma ya fasa kawai sai ya kada kai yafice daga dakin,ya fada nasa dakin bayan ya rufo kofan yanaji kamar ya dauki gidanan akansa ya dinga yawo dashi saboda yadda wani zuciya tare da karfi ke zuwarmai lokaci daya.