ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 1 to 10

Fadin irin tashin hankalin da wannan Ahali suka shiga bata baki ne,domin Suwaiba bataci bata sha sai kuka,bala ko dayaji,kallan mallam yayi yace”Kagani ko Baba wlh Abun na gudar mana kenan Tun farko nayi Tutsu a al”amarin..”Mallam ya gyada kai yana fadin”Har yanzu jikina yaki yardan Abdulnaseer zai iya aikatamin haka,zuciyata tafi karkarta akan WANI AL”AMARI NE..,Dabam yafaru dashi,ammh babu komai Koma miye Mucigaba da gayama Allah..”

Wata daya kenan Babu lbrinsa tun ana cigiya har akagaji aka zubama sarautar Allah ido,an samu saukin damuwar ta suwaiba,sai da kuma yanzu ciwo ne ya tasota gaba,kullum da zazzabi take kwana,ga shi komai taci sai ta amayar dashi ta rame ta lashe..ganin Babu yaki ci yaki cinyewane yasa Bala daukanta zuwa ABU CHIKA binciken farko aka gano dan karamin ciki na tswaon wata biyu da kwanaki,iya razana bala ya Razana,haka mallam yaji sanda lbrin yazomai,indo batayi mamaki ba sai dai Fargaban Abunda zatafadama mallam takare kanta,haka mallam ya tasa suwaiba agaba yana tambayabta waye yayimata ciki,don shi bai kawo Abdunaseer bane,Suwaiba na kuka tace Abdulnaseer ne,da mamaki Mallam ke kallonta kafin yace mata waye Shaidanta Daga ido tayi ta saukesu kan indo,Mallam dayaga haka sai yamaida kallansa kanta yana tambayanta meta sani game da hakan,cikin kaskastan dakai indo tamai bayanin Abunda yafaru takara da cewa yayi hakuri boyemai datayi,Mallam yayi Shuru yana jinjina al”amarin,Domin basu dawani Tsumi ballatana dabara sai na barma Allah..

  Mallam ya kwantarma Da Suwaiba hankali inda yace tayi kokarin kula da kanta da Abunda ke cikinta,Hankalu sunfara kwanciya har cikin suwaiba yakai wata biyar tafara zuwa awo,akuma lokacin Bala ya kamallah degree dinsa harya daura masters dinsa,sai kuma wani karin jarabbawan data bullo musu,domin mutane anguwa suka cha da maganganu na cewa Suwaiba diyar mallam tayi cikin shege,da mallam yaji batun sai da ya kwanta ciwo saboda damuwa,domin baya da ikon kare kansa da yarsa tunda kuskuren nashi ne,shaidun daya daura auren agabansu almajiransa guda biyun tuni suka koma garinsu abokinsa kuwa auren ba dadewa Allah yayimai rasuwa,baya da bakin da zaiyi mgana,karshe sai da fita ta garari indo domin duk inda taje ana tafe zundenta ana yada mata habaicin Yarta tayi cikin shege,Shiko mallam daina ma karatun yayi domin ko almajiran dayake ma karatun sun gudu,Tunda mganar ta fita,bala kuwa Shima lbri har cikin mkranta ana tafe yadawa kanwarsa tayi cikin shege,damuwa tare da tsananin ciwo ya rafke mallam kwance,dama Shine kwarin gwiwansu to shima ya kasa,Alokacin ne,kuma bala ya samu aiki a gidan Radion Nageria kaduna ashashen lbru,lokacin kuma Cikin suwaiba yakai wata na bakwai,Kwanan Mallam bakwai yana jinya jikinsa ya rikice suka daukesa suka kaisa asibitin al madina,sai dai kash kwana daya yayi mallam Shehu Akarami ya amsa kiran mallacinsa,ammh ko da ya rasu yafadama iyalansa kada su kullaci Abdulnaseer domin haryanzu zuciyarsa tana fadamai bada gangan bane ya aikata musu haka,akwai wani boyayye Al”amari,Mutuwar mallam ta girgixa mutane dadama ciki harda indo da bala da Suwaiba,wanda sukayi kuka,kamar zasu mutu saboda rashin bango agaresu,Ranar da mallam yayi bakwai kuma sai ga wata mgana wai Suwaiba ta kashe mahaifinta da bakin ciki,abu goma da ashrin gata da ciki,ga mutuwar mahaifi ga bacewar miji,ga Zunde mutane dawanne zataji,indo ko dama tuni tayi rauni dare daya Hawan jini ya fadeta ta mutu,tsakaninta da mallam kwana 70 ne,topha ta faru ta kare,maraici ya lullube Suwaiba da bala,lokacin yana gabda kammallah master dinshi,shiyasa yazama uba ga Suwaiba,shike lallashinta batare da shawara da kowa ya saida duka kaddarorinsu ya biyama mahaifansu bashi,ganin zaman zaria bazai yuyu dasu ba yasa ya saida harta komai nasu gidan dasuke ciki kadai yabari,dakanshi yahau mota ya tafi garin gombe,inda basu da kowa ya siyama Suwaiba wani dan matsikacin gida da taimakon dilallai,Koda ya dawo yafadama Suwaiba hukuncin daya yanke bata damu ba,saima dadi dataji domin garin zaria ya fitarmata akai kwata kwata,ko fita tayi yara sun dinga binta kenan wasu harda jifa,.

  Bala da kansa yadauki kanwarsa yakaita garin na Gombe da kansa,ya damkata hannun makocinta wanda garun gidansu yake ahade wato Mallam lawal bature,wanda ya kasance yana da matar aure daya Fatima,ammh basu taba haihuwa,asa”a Lawal din zaiyi sa”an Bala haka itama matar nasa bata fi sa”an Suwaiban ba,Ganin yadda suka anshi amanar daya basu hannu bibbiyu ne yasa ya zaunar dasu ya karanta musu komai na tarihin rayuwarsu daga karshe yabar amanar kula da Suwaiba da Abun zata haifa awajensu Tunda shi zaikoma ne,Saboda aikinsa da kuma hada kan karatunsa,sunmai alqawarin kula da Suwaiba tare da riketa tamkar nasu,yaji dadi sosai anan ya kwana washegari yayi sallama dasu yakoma kaduna bayan ya jibgemata kayan abinci da kudi harda siyayyar haihuwa suka rabu tana kuka yana kuka,wayyo rayuwa kenan..

Yana komawa yamaida kai ga hada kwalin master dinshi,yana kuma cigaba da aiki a gidan Redio Nageria kaduna,gefe daya kuma yana harka da yan Siyasa tunda yana hira dasu,kuma yana musu tallace tallacen siyasa nan da nan Sunan Bala shehu Akarami yayi Fice kowa ya Sansa,duk bayan sati biyu yake zuwa gombe ganin Suwaiba,ana wannan halin ne ya siyamata waya saboda wata mtsala in tataso basai ansha wata walaha ba,yafadama su mallam lawal da tafara nakuda suyi kokarin kaita asibiti.

Haka akayi Watan biyu da komawa gombe wata ranar jumma”a da yammah tafara Nakuda Allah yasa Fatima na kusa da ita,tabazama waje ta kira mallam,dayake dan sana”ar saida kayan gwari yake,anan kofar gidan,da hanzari ya nemo mota suka kaita asibiti,Suwaiba tasha walaha don sai da ta kwana ta wuni kana ta haifo santalelenta danta mai kama da Ubansa sak,kato dashi wanda yana fitowa Duniya Bala yana karisowa asibitin,lokacin da aka miko masa Yaron kura masa ido yayi,yana ganin tsabar kama dayayi da mahaifinsa Abdulnaseer,yaron ko yana harba kafa,alamar karfi,nan da nan Bala ya rumgumesa yana fadin”Sannu da zuwa Duniyarmu  *ALIYU GADANGA…*

       #Comment,share and vote..#

      #Janafty#….

*ALIYU GADANGA..!*

   _(The Story of yuong soldier man)_

Wattpad:Janafnancy12

*Hakkin mallaka:Janaf*

*DEDICATED TO MY MOMMAH…,HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA???? Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent writer’s asso*✏

_*Special Thanks to Hussain80k???? and HassanATK…Sakallahu Filjannah Dudes????*_

 

*NOT EDITED*????

*Chapter4*

   “”Kwanan Suwaiba biyu a Asibitin kafin asallamota tadawo gida,Bala yayi Namijin kokari akan Suwaiba domin Duk Abunda uba ke ma da,da Abunda miji zai ma matarsa sai da yayimata shi,mallam lawal da matarsa Fati suma sunyi namijin kokari kan Suwaiba,Fatima nan take wuni sai dare take komawa gida,ita zata sanyama Suwaiba ruwan wanka ta juyemata,kafin tazo tayima Aliyu wanka wanda Sunan da bala ya sanyamai kenan,Suwaiba bata nemi komai tarasa ba na bangaren rayuwa,bangaren yar”uwa kuwa Fatima ta koremata dukkan kishirruwan su.

Kwanan Bala uku agarin Gombe yakoma Kaduna bakin aikinsa,Ranar suna tana zagayowa aka Yankama Aliyu raguna guda biyu,makota da yan”uwan Fatima dana mallam lawal sunzo tayasu murna,dayake suma din yan Asalin Yan gombe ne,Anyi Abun cikin Mutumci da jin dadi,Suwaiba tacigaba da kula da kanta tare da Danta,duk da mutanen anguwa sunata zunde cewa tazo anguwan da ciki ta haifeshi batare da nuna alamun tana da Aure ba,domin ada sun zata Bala ne mijinta,ammh sai daga baya suka Fahimci cewa yayantane ba mijinta ba,duk da haka Suwaiba ta toshe kunnanta bataji bata gani,ta dauki nasihan dan”uwanta daya cemata ta maida hankalinta wajen kula da kanta da Abunda ta haifa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button