ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 1 to 10

  Aliyu nada Shekara uku aduniya babu inda baya zuwa yayi wayau haryafara Tafiya,alokacin ne kuma Bala yayi Aure da matarsa Umaima yar kadunane Haifaffiyar Kabala ce,mahaifinta shima tsohon dan siyasa ne,tunda shine tsohon mataimakin gwamna a gwannatin data sauka,Akwai girmamawa tsakaninsa da Bala,tun mahaifisu na raye yasan mallam,tunda yace sunyi karatu wajensa,to shigowar Bala harkan Siyasa ne,yasa suka sanjuna,kuma shida kanshi yayimai tayin Auren diyarsa tasa Umaimah,anyi biki lafiya amarya tatare agidanshi dake Anguwan Dosa,gidan yana da girma wanda Bala yadau tsawon lokaci yana ginashi,bayan Aurensu da wata biyu ya dauketa yakaita gombe don ta gana da Kanwarsa Suwaiba,hakika Umaima ta tsausayama Suwaiba ganin inda takoma da rayuwa daga ita sai Da”nta Aliyu wanda yana girma wayonsa da kwazonsa da Karfinsa tare da kamaninsa da mahaifinsa suna kara bayyana,awannan zuwan ne Bala ya sanya Aliyu awata mkranta da”a ke kira MATRIC INTERNATIONAL SCHOOL GOMBE..,Mkrantace mai tsada domin sai ya’yan wane da wane,kowani kusa agwannati ko yan siyasa,Cikin nasara da hazaka Aliyu yafara karatunsa Koda akayimai interview Malaman mkarantan sunyi mamakin kaifin basiran yaron,duk da ance baitaba hallartan mkranta,ammh dayake Suwaiba bata wasa zama take dashi takoyamai Dak da iya Abunda tasani na boko dana Arabi,Nursery 2 aka sanyasa saboda yadda sukaga yaron da kaifin kwakwakwa,kafin Aliyu ya rufe shekara sunansa yayi Tambari a mkranatar nan saboda yadda Allah yayima yaron baiwan karatu Shiganshi Shashen primary yasa sunanshi yakara fitowa domin koda yakeda kankantar shekaru ana zuwa dashi gasan mkranta.

   Watan Umaima tara ta haifo santalelen Danta mai kama da ubansa sak,Ranar suna yaro yaci sunan HAISAM,wanda tsakaninsa da Aliyu shekaru hudu ne,bayan shi tazo tayi yan biyu, MARDIYA DA MADINA,Daganan bata kara haihuwa ba, haihuwar Haisam dai Suwaiba bata samu zuwa Kaduna ba saboda mkranatar Aliyu,sai haihuwar yan biyu ne taje kaduna saboda lokacin su Aliyu sun samu hutun mkaranta,sati daya sukayi akaduna kafin Su dawo gombe,Suwaiba tasan yarda take da Aliyu,tun yana yaro,yana da kiriniya da kuma son wasa,ammh bata bari yana Fita,sai dai in zai fita wajene ya zauna wajen mallam lawal,kokuma Fatima tatafi dashi gida,ammh kuma baya zama,da fari ta sanyashi a islamiya anan anguwan ammh sai yaran mkranta suka fara kyamatarsa da kokarim kiransa da wanda bai da uba,Kullum da kuka yake dawowa,yana fadama Suwaiba Abun na damunta,tana tsoron kada su sanyama yaronta wani banzan Tunani,sai kawai ta cireshi ita takoma malamarsa tunda daidai gwargwardo tana da ilimin Addinin harda na boko,sai takoma tana koyar dashi agida,tun yana yaronsa Suwaiba ta fahimci Danta yana da bala”in zuciya gashi tun yana karaminsa yake da bala”in karfi kamar doki,shiyasa take binsa ahankali,Abu dayane yake cimata tuwo a kwayar irin sunan da yan anguwa suka sanyama Danta wai DA’N MACE,tun Abun bai damunta harYafara damunta,shiko Aliyu tun yana dukan yara in sun kirashi da sunan haryakura yafara amsawa,saboda ya yarda shi din Da’n mace ne,ammh kuma macen ta bambamta da sauran mata saboda jajircewanta akan Rayuwar Dan”ta.

Aliyu nada shekara Tara Aduniya Fatima ta samu ciki,wanda ya kasance yana bata wahala,farinciki wajen mallam lawal d Fatima ba”a mgana,ita kanta Suwaibar tana murna da hakan,don ita da Fatima tamkar yaya da kanwace,Saboda laulayin data fama dashi mai zafi ne,yasa mahaifiyar Fatima BABA ADE Tadawo nan gidan tana zaune da ita,tana bata kukawa,duk da itama Suwaiban data gama aikin ta zata rufo gidan tashiga gidan mallam lawal tana taimakama baba Ade dawani Abunda ba”a rasa ba,Cikinta yayi girma sosai kuma yabata wahala,wata tara nayi ta haifo yarta mace santalele da ita,bayan bakar azaban dataci asibiti,wanda Bala shi yayi wannan dawainiyar saboda alherin Mallam lawal da matarsa Fatima garesa dashi da kanwarsa,harta hidiman suna da Kayan babby dana maijego Duk bala yayi su,ranar suna kuma ya yankamata katon ragonta yarinya taci suna AZEEMA..,Sai da tayi arba”in kana Baba Ade takoma gida tabar Fatima nakara kula da yarta,Tare da taimakon suwaiba,wacce tadauki son Duniya ta dorama diyar Fatima,sabida suwaiba na son Diya mace arayuwarta,ammh Allah bai bata ba,sai yabata namiji,Saboda Amintakar dake tsakanin Fatima da Suwaiba ne,yasa Fatima tayima suwaiba tayin Auren mallam lawal,mganar data kawo rudani sosai,suwaiba taki yarda.hartayi ikirarin barin garin gombe,Bala ya shiga mganar yace Fatima tayi hakuri suka cigaba da zumuncinsu,tunda Suwaiba taki,dole Fatima tabar mganar ammh harga Allah tana kaunar suwaiba aranta.

Shekaran Azeema biyu Aduniya Fatima tafara wani ciwo,daga ciwon nono,shikenan sai cancer ciwon Daji,Tun ana ganin abun dawasa har babbar magana tazama babba,mganin gargajiya aka fara ammh Abu yacitura nono sai zagayewa yake,harya harbama dayan ma,Suwaiba da kanta takira bala ta fadamai kan yazo ya taimaki,Fatima koda yazo yaga halin datake ciki sai da ya zubarmata da kwallah,nan da nan aka dauketa zuwa babban asibitin jaha,sai koda sukaje likitoci kin amsanta sukayi,suna ta fada suna fadin sai da ciwo yagama cinyetane za”a kawo musu,bazasu amsa ba,ran Bala yabaci yace adawo da ita gida washegari sai sutafi da ita kaduna,Allahu Akbar Allah yaga Abunda yagani ne,ya takaitama musu wahala Karfe 3:00am na dare Fatima ta karbi kalmar shahada tarasu agaban mahaifiyarta da mijinta mallam lawal bayan ta bayyana amanar diyarta ahannun Suwaiba,wanda Aranar sai wajen sha biyu takoma gidanta,itada Aliyu da Azeema wacce keta kuka,shiyasa ta dauketa suka tafi gidanta takwana awajenta,alokacin mallam lawal ya bugama Suwaiba kofa dayake Bala na nan shi ya fito,nan yake shaidamai rasuwar Fatima,sanda Suwaiba taji sai da ta suma gau,saboda jimami da sabo,Tayi kuka kamar ranta zai fita,babu Abunda take tunawa sai irin sabon dasukayi da Fatima da zaman amanan da sukayi,tunda take da ita bata taba batamata da gangan ba,macece mai hakuri da sanin yakamata,balle mallam lawal dayayi kuka rasa nagartattaciyar mata irin Fatima,ita kanta Azeemar ta fahimci rasuwar mahaifiyarta nata,haka ta wuni kuka,Suwaiba na lallashinta Aluyu ma yasan lokacin da”akayi rasuwar,saboda yana da shekara 12 alokacin Domin har yakammallah karamar primary dinsa sai wucewa gaba,Baba Ade ma takoka domin itakadai ne yarta gashi Allah ya amshi Abunsa,Anayin bakwai Baba ade tatafi da Azeema wajenta,dayake basu da nisa saman anguwansu,shiyasa kullum sai Azeemar tazo wajen Suwaiba,wanda ko Azeema batajeba Suwaiba take wanke kafa taje ganinta Haka kurum Allah ya doramata son yarinyar da tsausayinta,shiyasa komai zatama Aliyu tare take hadawa da Azeema.

  Fatima tayi Arba”in da Rasuwa Bala yazo yatafi da Aliyu zuwa kaduna domin hallartar mkarantan daya neman masa Wato COMMAND SECONDARY SCHOOL KADUNA..,Makarantar sojoji dake kaduna,Babu yarda Suwaiba zatayi Tunda Aliyun yanuna yana son mkranatar na Sojojin,dole tanaji tana gani ya hada kayansa yabi kawunsa zuwa kaduna,wanda awannan karon yayan nata yaso tabiyoshi sukoma kaduna ammh suwaiba taki,tace tafi sabawa da Gombe bazata iya barin garinba,shikuma bayason takuramata sai ya rabu da ita,ammh duk Abunda zata bukata sai da ya barmata kafin su tafi,Da shi da Haisam aka sakasu amkranatar dayake anyima HAISAM din jamping din aji shiyasa sukayi Daidai akaratu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button