ALIYU GADANGA Page 31 to 40

_________________
Kawu da wannan lbrin ya isa gida yadda Ummah ta ganshi yana Fara”a tasan akwai Abunda yafaru,bai tsayama amsa sannu da zuwan datakemai ba yashiga kwararamata lbrin Abunda ya faru,tagumi Ummah ta saka tana kallon Kawu bala,tana jin Abun kamar al”amara,lokacin dayake Fadamata Mahaifin gadangan yanzu Sarki ne,garin Agadez,mikewa Ummah tayi ta saka hannu bisa hanci tana Sakin guda harda rawa da juya tana Fadin”Allahu akabar Suwaiba Matar sarki dole mu kiraki gimbiya,Shikuma gadanga yazama yarima Allah yakaimu wannan Masarauta muma mu nuna tamu Rawar…”Tafada tana dariya kawu kallonta kawai yake yana girgiza kai,bai Fadamata zuwan Maimartaba din sai da yaga ta natsu kana ya sanar da ita gobe Maimartaban zai iso gombe,so dukkansu zasu Tafi gombe,ta kira Ya”yanta awaya ta Fadamusu,yanzu Shima zai kira Haisam hardashi ataho,Nan yake Fadamata Goggo batasan Abunda ke Faruwa ta gargadi ya”yanta kada ta kirasu ta Fadamusu su kira goggo taji mganar daga sama,ai Saboda murna goggo ko Sauraransa batayi ba,ta Runtuma daki tan laluban Madina awaya,ita tafara Fesamawa Ihu tasaka tana Fadin”goggo a palace wow…”Take Fada kafin tace”Yaya captain kuma yarima,and kuma Azeema She is now a princesss…”Take Fada tana dariya,Ummah ta Shaida mata sakon Mahaifinsu na Tafiya gombe gobe,tsalle ta saka tana Hango gobe taga yadda za”ayi Rumgumar yaushe gamo Tsakanin goggo da Maimartaba Sarkin Agadez,kafin su yanke sai da ta kwabe kan karta kira goggo,suna gama waya ta kira Mardiya itama ta Shaida mata,Guda mardiya ta saki tana Fadin”Ummah Ashe muma munada jibi da jinin Sarauta no wonder yaya captain keda wasu dabi”un jinin Sarauta ashe itace ke yawo ajikinsa Allah mun gode maka..”Itama din sakon Kawu bala ta sanar da ita,kafin kuma ta kwabe akan kartakira goggo don batasan meke Faruwa ba Tukun,Sun rabu akan yanzu zata kira maigidanta gobe da Safiya ita da yara zasu tanan sai su wuce,tunda ummah ta Shaida musu Mahaifinsu yace suzo gidane,don ajirgi zasu je gomben.
Koda Ummah takira Haisam,saima shiyafara mata murnan Abunda ke Faruwa yace,Tundazu Aliyu ya kirashi ya sanar dashi yanzu hakama yana hayar tahowa yasamu An barshi yazo,ammh kwana2 kawai zaiyi Shiyasa ya zabi ya taho yau gobe in sukaje gombe,jibi sai yakoma bakin aikinsa,Murna ummah tayi tana tamai Addu”an isowa lafiya,Ummah fa kamar tayi hauka ta kira wayar Aliyu yana dagawa ta Shigamai kirari da Fadin!”Allah ya taimaki yarima mai jiran gado,Allah ya taimaki dan Sarki jikan Sarki Takawarka lafiya dan Masaurata,…”Dariya Aliyu yana Shafa Kanshi,Amsata mata yake yana Fadin!Ummah duk nikadai..”Ummah tace”Eh don ma banda algaita ai da kaji busa,dariya kawai yayi Nan,ta Shiga mai murna tana Fadin”Sai goben in sun hadu agombe don ita zata so yin ido hudu da Sarkin Agadez din”Dariya kadai Gadanga kemata don indai Ummah ce yasan hali macece da babu Ruwanta wlh haka take So Simple,Suma su gadanga Adaren Ranar sukayi Shiri,domin gobe Tun Safe zasu dau hanyar gombe don su zasu riga su kawu isa tunda su Tafiyar mota ne,shiko kawu yafadamai Cewa Jirgin karfe goma na safe zasu biyo,suko suna saka ran Kafin goma ma suna Falon hajiya Suwaiba Goggo mai Shagalin Duniya.
****************
*WASHEGARI*
_Gombe_
“”Azeema Tun bakwai da Rabi na safe tatafi mkranta don yau suna da jarabawa,Pratical biology suke dashi, dakyar ta tsaya ta karya ,shima din sai da goggo tayi da gaske,kana ta iya tsayawa ta danci kwai sai Ruwan Tea datasha,donma takima goggo taso tasakamata akula wai tatafi dashi,in an Fito jarabawar taje massllacin mkrnatar taci,Abun dariyama yabata tace ma goggo”Kai goggo kamar wata yarinya..!dakuwa goggo tayimata Kafin tace”To dah ke waye in ba yarinya ba,mekika sani na game da Rayuwa, ai Shikenan tunda kin Raina kokarin danayi miki!”Goggo Tafada tana Tura baki kamar wata yarinya dariya Azeema ta saka kafin ta Rumgume goggo tana Fadin”Kai goggota kada kibata rai mana,Toh naji ammh ki ijiyemin in nadawo zanci..”Ko kallonta goggo batayi don wani lokacin goggo akwai kulewa,Azeema na dariya ta Fice da hanzari ta kusa makara.
Karfe 8:00am su Aliyu gadanga suka baro kaduna,Gudu sukayi tayi amota kusan Tafiyan maza ba daya dana mata ba,suna Shigowa garin gombe sai da suka fara biyawa wani hotel suka kama ma Umar daki,suka ijiyesa har sai su maimartba sun kariso,wanda Shine zai sanar dasu anguwan dasu Aliyu suke bayan sun sanar dashi,basu dade anan ba sukayi mishi sallama suka Shigo cikin gari.
Karfe 10 da wasu mintina motarsu tayada zango akofar gidan goggo,tana tsakar gida tana Tsingan zogalenta don yau miyar zogale take sha”awar ci, taci kwalliyarta cikin wata Atamfa Super,wanda Aliyu ya dinkamata riga da zani,tadaura dankwalinta Ram akanta ga karamin Radio ta agefe tana jin daya daga cikin Fm dake gombe Aliyu dake gaba ya rafka sallama Jabir na biye dashi,dukkansu suna sanye da Farar shadda riga da wando,dukkansu dinki muhammed,kana aikin jikin Shadda baki ne,hakama Zanna bukar din dake kansu,ga kuma wani ubansu Sawu ciki na fata,hatta da agogon hannunsu na Fata ne,wanda kamfanin Rado tayishi.
Goggo na ganin Aliyu ta mike tamusu maraba bakinta har kunne,Rumgumeta Aliyu yayi bakin har baka yana Fadin”Gimbiya goggo…”Bayansa ta dan buga tana Fadin”Oh ni Suwaiba wai kuma wani sabon suna na samu,Jabiru sannunku da zuwa kunsha hanya fa..”Tafada tana Sakin gadanga,har kasa jabir ya duka yana gaida goggo ta karba tana tambayanshi iyayansa,ya amsa da suna lafiya,daki ta nuna musu tana Fadin”,Ku Shiga bakin Sassafe,koda yake shifa gadanga ko shaho nan ya barsa da sammako,in zai taho yadako sammako,in zai tafi ma haka,to fa sai dai ko shayi zaku sha don,munciye komai na Diyata kadai yarage kuma namata alkawarin Zan ijiyemata hartadawo..”Jin Abunda ta ambatane yasa Alliyu tsayawa cak kafin ya waigo yana Fadin”Goggo wai kina nufin pretty? ina taje hala? yafada yanayin Fuskarsa na chanzawa,Kallonsa goggo tayi adage kan tace”Meye kuma Furata? dariya takama jabir yanayi yace”A”a goggo ba Furata ba,pretty yake nufi,wai Azeema…”Tsaki goggo taja tana Fadin”Mtsewwww kaji iskancin banza yarinyar tanada sunanta na musulunci kamaida mata na Kafurai,wai Furata,A”a kwarota ne ba Furata..”Tafada tana Shigewa daki ta barsu nan ba jabir ba hatta Aliyu sai da ya dara,dakin suka Shiga suka zazzauna kan kujera,kichen goggo ta Shiga ta daukomusu Flaks din Ruwan zafi da kayan Tea din,sai takoma takara Soya musu kwai ta hado musu dashi,Aliyu ya riga yasani goggo bazata taba basu wanda tace ta ijiyema Azeema ba,haka akidan goggo yake tanada kafiya wani lokacn ,nan suka baje suna karyawa ita kuma goggo tana waje tana cigaba da aikinta,Shiko Aliyu kurban tea din yake ammh gabadaya Ransa da zuciyarsa suna ga Tunanin Azeema,toh ina taje,? donshi baizata sun Fara jarabawar ba,tunda ba lissafi yake ba.
karfe 11:00am Azeema ta Shigo gidan duk agajiye,hannunta cike da leda ta Siyo goribanta,Tana Shigowa da sallama su Aliyu dake daki sukajita,goggo ma dake tsakar gida ta amsa tana Fadin”Har kin dawo..”Saboda yadda tagaji,gakuma halin data ke ciki,don yauma arike ta dawo Akasa tazauna tana yamutsa Fuska goggo ta bita da kallo tana Fadin”Tsiyana dake rashin jin mgana Azeema..”Tura baki Azeema tayi tana Fadin”Me kuma nayi goggo..? kai tsaye tace”har saunawa zance kidaina zama akasa? zaki sha takaichi ne sanda sanyi ya shigeki wlh,bazan hana gadanga yo miki kishiya ba,tunda sakarcinki yajamiki..”Jin Abunda goggo Ta Ambato na sunan gadangan datayi yasa Abun yayomata shar arai,Tuni taji idanuwanta sun cika da hawaye,aranta tana Fadin tafi kowa bukatar yaya captain,adaidai wannan lokacin don Tafara gazawa,haka hawaye suka zubomata Shar,Goggo dake aikinta taji Shesshekan kukanta ta dago tana kallonta haba ta rike tana Fadin”,Oh ni Suwaiba daga wasa sai kuka,toh maza share hawayenki,dake kadai gadanga zai zauna ke daya tilo kamar Fitilar Besfa..”Dariya takama su jabir dake ciki ita kanta Azeemar sai da ta dara hijabin jikinta data cire,ta mike ta daureshi a kugunta kanta ko dankwali babu taja ledar goribanta ta Shige daki tana Tura baki,tsabar rigima ko takalman dake wajen bata lura dasu ba.