ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 31 to 40

Aliyu najin karar Jiniyar motocin Kawu ya Fito da gudu,baima jira yakai ga Fitowa ba ya bude mota ya Riko hannunsa yana fadin”,Taho kawu kaga wani abu..”Yafada yana Jansa zuwa cikin gidan,da hanzari ya Bishi yana kara saba babbar rigarsa Suna shiga cikin Falon kawu yaci karo da Umar zaune yana mai mirmishi Zaro ido kawu yayi yana bin Umar din da kallo,Kafin kuma yakoma yana bin Aliyun da kallo,Kawu yayi tsaye kafin ya Durkushe kasa kawai yana Fadin”Sarki ya tabbata ga Allah Shugaban kowa da kowa..”Yafada yana kai goshinshi kasa yadade kafin ya dago,koda yadago hawaye ne sharkaf bisa Fuskarsa,Aliyu ne yadagosa yana Fadin”Kaima kayi kuka ko kawu,wlh nima nayi,banta zaton zan yi Farinciki irin na yau ba,kawu kaga kamana dashi ko,kuma muna using da Surname iri daya His Name is Umar Abdulnaseer Tambari buzu…”Hannunsa Kawu ya riko ya karisa ga Umar yariko hannunsa ya hada dana gadanga yana Fadin”Ka sanar dani wani Abu game da mahaifinku Shin Abdulnaseer na raye acikin Duniyar nan”?Mikewa Umar yayi yana Fadin”Tabbas Maimartaba na Raye,ammh kuma yana rayuwa da mafarkin dakuma damuwarku,koda da darana daya Abbah bai taba Fidda rai da Allah zai bayyanamai Sirrin boye ba..”Ido Kawu ya zaro yana Fadin”Naji kace maimartaba kuma? dariya Umar yayi kafin yace”Eh Shine Sarkin dake mulkan *MASARAUTAR TAMBARI BUZU DAKE YANKIN AGADEZ..* Baya kawu yaja yana Fadin”Allah mai hikima da kari,babu wanda ke tsarawa kuma ya zartar lokaci daya sai Ubangiji..”Ya fada yana jinjina kai,kafin ya zauna sukoma suka sakashi atsakiya Kawu ya kalli Umar yace”Kabani wani lbri game da Abdulnaseer…’Nan Fa Umar ya basu lbrin Abunda ya sani game da mafarkin da maimartaba keyi,dakuma fadamai dayayi yayi Rayuwa A nageria ammh bazai iya Tuna awani gari bane,ako awani yanki bane,Shidai lokacin da Hankalinsa ya dawo ya Tsinci kansa ne awani gari,ammh kuma har mutumin daya taimakamai ya kawoshi har masarautarsu bai fadamai awani gari bane alokacin,ammh kullum cikin mafarkin wata mata da Danta yake,suna ahalin neman Taimakonsa…”

  jinjina kai kawu ketayi yana fadin”Kaji hikimar ubangiji ko Aliyu,Ai bakowa Allah ke Nunamai ba Sai Suwaiba dakai,Allah mai hikima” Kawu ke Fada Haryanzu yana mamakin al”amarin Jabir Shima na gefe yana Jin Abun kamar amafarki,Umar yasaka hannu a aljihu ya zaro wayarsa yana Fadin”Bari na kira waya zuwa gida..”Aliyu ya mike da hanzari yana Fadin”Kawu zan Sanar da goggo..”Rikosa kawu yayi yana Fadin”kyaleta ba yanzu ba,kasan Suwaiba bata iya Rudewa ba,kabari mufara ganin Abdulnaseer din mugani ko zai Shaidamu…”Yafada daidai Lokacin Zafira ta daga kiran Umar hoton ta ya bayyana Tana Fadin”La yaya Soja sai yau zaka Tuna damu ko,Safaratu taho ga yaya Soja ya kiramu daga Nageria..”Da gudu ko tataho tana Murna tana Fadin!”La yaya Sojan mutan Nageria,take fada daidai lokacin da hotonta ya bayyana Yanmatane,daya nada Shekara sha takwas daya kuma nada Sha biyar,Dukkansu kammansu daya Sai dai su suna da dan jiki,ammh yadda kaga Umar haka suke,Sai dai su yanayin idonsu da karan hancinsu yafi iri daya dana Ali zaki 

Mirmishi yayi musu yana Fadin”Aiki ne yamana yawa Shiyasa ban kiraku ba,ya gida,ina ummah mai babban daki,kucemata nayi kewarta ina mommy nayi ta kiran wayarta bata daga ba..”,Bata Fuska sukayi suna kallon Juna ganin haka sai hankalinsa ya tashi ya mike yana tambayansu”Lafiya meyafaru kowani Abu yasamu mommyne?Saurin dakatar dashi sukayi Suna Fadin”A”a yaya dama Abbah ne fa…”Afusace yace!Me Abban yayi me..? ganin yadda ya daka musu Tsawa ne yasa Zafira tayi Saurin cewa”Bafa wani Abu bane yaya Dama Abbah ne Tun Shekaran jiya bayi da lafiya,su mommy ma dasu Ummah chan Shashensa suke wuni..”Kai ya dafe yana ambatom Sunan Allah,su kawu dasuka koma gefe sukayi Tsuru suna binsa da kallon mamaki,Aliyu kuwa kamar ya warce wayar yaga Yaran dake mgana domin Sosai muryansu ke saukarmai da wani Farinciki,ammh jin Sun Ce Abbah bai da lafiya sai da yaji Faduwar gaba 

Da hanzari Umar yace”Ku tashi maza ku Isa Shashen Abbah yanzu ku hadani da mommy”Dako hanzari kowacce ta mike dama suna sanye duka da alkyyabansu suka Fice suna ta mai Surutu,suna bashi lbrin ciwon Abbah ammh shiko jinsu bayayi burinshi su isa su mikama Mommy wayar,suna isa barayin na maimartaba suka isake Gimbiya Fasilatu da mahaifiyarsu gimbiya Razeenah sai Ummah mai babban daki wato kakarsu kenan wacce ta haifi maimartaba Suna zaune bisa Wani lafiyayyen Cafet,kowacce taci alkayabba takame,Ummah ce kadai ta sanya wani katon lullube,sai maimartaba dake kwance kan gadonsa idonsa biyu,kansa na bisa cinyar Ummah mai babban daki,suna Shiga suka isa ga Gimbiya Fasilatu sukace”Mommy ga waya yaya Soja nasan mgana dake..”Sukace suna mika mata wayar,Amsa tayi tana Fadin”Allah yasa baku Fadamai ba..? baki Zafira ta tura tana Fadin”,Tambayanmu yayi muka Fadamai gaskiya.”hararansu Tayi kafin ta maida hankalinta ga wayar inda taga hoton danta ya bayyana mirmishi tayi tana Fadin”Yarima mazan Fama..”Gimbiya Razeenah dake gefe ta yamutsa Fuska ta kauda kai.

Umar ya Shafa kanshi yana Fadin!”Mommy meyafaru da Abbah ne…? Dan muskutawa tayi Tana Fadin”Wlh bawani abun tada hankali bane Umar,kawai mafarkin daya sabayi ne tun Shekara jiya ya Farka yana ta kiran wani Suna,yana fadin wai matarsa ne,ammh ya manta awani gari take wai sanda ya bar gida ,a inda yajene ya aureta,kuma yafadi wajen,yakasa Shine fa Tun Ranar jiki yaki dadi,yakasa daina sakama kansa damuwa gashi har jininsa ya hau,baka Tunanin kawai Kwakwalrsane Bata samun hutu…!Tunda Tafara mgana Umar ya kafeta da ido,yayinda Aliyu yaji jinin jikinsa ya daskare,shiko kawu baki kadai ya rike yana kara tabbatar da ikon Allah.

 Bakin Umar na Rawa yace”Wa…Wani Suna yake kira Mommy..”Tabe baki Tayi kafin tace”Ko Saddiqa ko wama,kamar dai *SUWAIBA* ko..? tafada tana kallon gimbiya Razeenah wacce ke kallonta ta wutsiyar ido,banza da ita tayi,don ita akwaita da iko ne wani lokacin,jin Sunan da Tafada yasa Umar Saurin Fadin”Mommy ku tada Abbah ku basa wayar wlh Allah ne ya Turoni nan don na cikema Abbah ragowan Abun da ya Shigemai Duhu,ku basa wayar na gano wadanda yake nema..”Dayake video cll ne,kowa naji,ai maimartaba dake kwance kan ciyar Ummah sai gashi ya mike kan kafafunsa ya diro daga kan gado,kafin ma Gimbiya Fasilatu tayi wani Abu ya Fizge wayar Fuskarsa ta bayyana yana kallon Umar yace”da gaske…Da gaske Umarun Faruqu ka ganinmin Suwaibata..? yafada cikin muryan dattako ammh ta Shake saboda damuwa.

 Umar dake kallon mahaifinsa yaji hawaye sun kawomai,kai ya dagamai yana saka hannu ya yafito kawu bala yako zo da Sauri Wayar Umar ya mikamai Shiko yakoma baya yana Fadin”Abbah ka gane wannan dake tsaye..? Maimartaba dake tsaye, yayi Turus yana bin Fuskar kawu da kallo,wanda ke tsaye shima yana Bin Fuskar maimartaba da kallo,Kawu bala yakurama Abba ido yana kallonsa yaji hawaye sun kawomai komai Shekaru da dadewa bazai manta wannan Fuskarka ba,jikinsa na Rawa ya daga hannu yana Shafa Fuskar maimartaba yana Fadin”Abdul…Na…Naseer…”Bakinsa na Rawa Maimartaba dake tsaye,matansa da Mahaifiyarsa sun zagayesa tun sadda sukaji Umar na Fadin Ya gane wannan? Maimartaba ya Fashe da kuka yana Fadin” *BALA*.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button