ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 31 to 40

   *SHEKARUN BAYA*

_LABARIN MASARAUTAR TAMBARI BUZU_

  

   _Ashekarun baya Anyi wata Masaurata Akasar Niger a yanki Agadez,awannan yanki anyi wata masarauta mai Dimbin Tarihi,Tun Ada Masauratane datafito daga tsatso mai Asali,tsatsoce ta jinin sarakai,tunkan zuwan Addinin musulunci,Mutane dadama sun mulki Garin,Adalai masu kaunar talakawa da kawoma Masarauta cigaba,Wannan Masarautan Sunanta MASARAUTAN TAMBARI BUZU,Sunanta ta samo Asali ne,daga sudin buzaye ne gaba da baya,kuma sunkasance dukkansu Farare ne,dogaye masu zati da haiba,suna da jarumta uwa uba kuma Masarautane mai Dimbin Tarihi na Kudi da Arziki ko ada chan,suna da hadin kai da Sanin mutumcin juna,ba”ta samun Sabani ko Rabuwan kai ba,sai da Manya suka Fara tafiya Mulkin yafara komawa hannun kananan_

  _Masarautar ta samo Asali ne Daga mulkin Sarki ABDULGANIYU D’AN HASHIM,wanda ya mulkin Garin na Tsawon Shekaru arba”in da wani Abu kafin Allah ya dauki Ransa,bayan mutuwarsa aka Nada babban D’ansa Wato BADAMASI D’AN ABDULGANIYU,amtsayinsa na babban Dansa,kuma ya chanchanta da zama Sarki bisa la”akari da duk Abunda ake bukata ya mallakesu,Kuma yakasance Shikadai ne Namiji Awajen Sarki Abdulganiyu,Sauran Duk matane_

  _Shekaransa goma ne akan karagar mulki Ya rasu,Bayan Mutuwarsa Anyita Rigima kafin Anada Wani sarki Wato YAKUBA D”AN BADAMASI ,Jika ga ABDULGANIYU D”AN HASHIM,Wand Shibashi daga cikin wadanda suka nemi Sarauta alokacins saboda baya Ra”ayinta kwata kwata,kuma Shine na hudun ajerin mazan,kuma duka yayyin nasa su uku ba wanda bai Nemi Sarauta ba,ammh basu samu ba sakamakon basu chanchanta ba,kwatsam sukaji an nada YAKUBA bisa chanchantarsa shi yakasance yana da ilimin boko har matakin masters,duk da bai yawaita ba awanchan lokacin,sabaninsu na Arabi”an kadai garesu,sannan yafisu sanyi Hali,duk dayake karami acikinsu Adai komai ya chanchanta Toh wannan al”amari Shine tushen komai don Shima yasama Sauran yan”uwansa hassada da kyashi Aransu,acikin yayyin nashi akwai IDRISA, sai KAMALLUDEEN Sai NASAR Sune manya kuma sune suka nemi Sarautan aka hanasu,kuma gabadayansu ba ya”yan mutum daya bane,Tunda alokacin matan Sarki hudu,Mahaifiyar yakuba ne karama_

  _Su aganinsu yaya za”ayi Adauko Yakuba abashi mulki,Alhalin gasu,an nuna musu yan ubanchi,daga wannan lokacin Zaman lafiya ya kare awannan masarautan inda su Idirisa sukasha alwashin ganin bayan wannan mulki na Yakuba,bayan an Nada Yakuba,Talakawa na jin dadin mulkinsa,sakamakon yayi gadon mahaifinsa akyawawan dabi”u,ba yadda baiyi ba don ya sansanta da Yan”uwansa ammh ina Abu yaci Tura,Har Sarauta yaso ya ijiye, yatarama manya masu ruwa da tsaki a masarautar,su suka nunamai Ahir dinshi,saboda shima bayason Abunda zai kawo Rabuwan kai shida yan”uwansa,mahaifiyarsa akullum Addu”arta Allah ya tsaremata da’nta toh Ana wannan Hali Allah yayi mata Rasuwa mutuwar data girgiza sarki Yakuba yazama maraya gida da waje,toh daman yana da matansa ,uwargidansa UMMUKHAIRI yar wani tsohon Wazirin Sarki Badamasi ne,sai GIMBIYA KILISHI yar wani Sarki dake gaba da yankinsu,bayan An danashi Sauratane Yacike da MASHASHATU itama yar sarki ce sai takarshensu yar wazirinsa ne ya Auramasa ZULAIKA_

  _Allah da ikonsa Da”n sa Namiji kwara dayane tak Duka haihuwan da Matansa keyi wabi suke Uwargidansa UMMUKHAIRI ita ta Haifasa masa Shi Wato ABDULNASEER,sarki yakuba ya dauki Son duniya ya dorama Abdulnaseer,kuma hakan ya samo Asali ne daga soyayyar dayakema mahaifiyar Abdulnaseer din,girman Yaron ne aka gane babu inda Hallayar mahaifinsa Yakuba Natsuwarsa da son Talakawa Shine dalilin dayasa mutane suke kiransa da MAGAJIN SARKI,toh wannan shiya taso da Wutar kiyayyar Dake tsakanin Yakuba da yan”uwansa,akan bazasu yarda Wani dan yakuba yazo ya mulkesu ba,suka dora daramar Kwatar mulkin kota halin kaka,awannan yanayin Masarautar Tambari buzu tatashi da wani Firgici na Mutuwar Sarki Yakuba,an kwanta dashi lafiya kalau Akatashi akaga gawarsa Bisa binciken likitoci sun gano cewa ta hanyar Filo aka kasheshi tunda gayinan akokarin kasheshi da Filon har sun jimai ciwo awuya alamar sai da sukayi kokuwa da makashin_

   _Topha wannan al”amarin yasa Jama”a Dadama acikin Rudani,Ummah tayi kuka sosai,ita da tilon da’nta kai ba ita kadai ba kaf Masarautar Tambari buzu sai da ta girgiza,balle talakawan dake Yanki na Agadez,Harga Allah Ummah ta zargi wani Abu ammh sai ta boye,wanda Tun sarki yakuba na da Rai akecemata Ummah mai babban daki,sakamakon itace uwargidan sarki kuma mahaifiyar Yarima Abdulnaseer,Bayan mutuwar Sarki Yakuba aka Fara mganar Nadin sabon Sarki Alokacin Nagama Digree na akan political Science,karatun Addini kuwa Tuni nayi nisa_

   _Azama na Farko An tabbatar dacewa anine mutum na farko da”aka  kawo wanda ya chanchanta abani Sarautar masauratar Tambari buzu,domin na gaji mahaifina,wannan Shiya kara harzuka su Idirisa,wanda sun kara neman mulkin akaro na biyu,Manazarta da magabatan Zauren wakilai na zaban Sarakai basu tsaya bata lokaci ba suka Fitar da sunana amtsayin Sarkin Garin Agadez,harga Allah bani so,kuma mahaifiyatama bata so,Saboda tana zargin mutuwar Mahaifina yana da nasaba da Sarautar garin,Abisa wannan dalilin aka Fitar da Ranar daza”ayi min Nadin Sarauta amtsayin Sarki,sai Aranar Nadin Sarautar aka wayi gari da magajin Sarki an nemi ko sama ko kasa ba”a ganni ba,har angaji anfidda rai,dalilin an kwashe wajen wata biyar bani ba lbrina yasa aka Nada IDIRISA Masaurata tazo hannunsu sai yadda sukaga dama da ita_

    _Bacewata ta girgiza Zuciyar mahaifiyata wanda na kasancemata Da daya tilo Aduniyan nan rashi biyu alokaci daya,mahaifiyata tadauki dangana tare da maida kukanta ga Allah,tana Fatan in ina raye Allah ya karematani,ya kaddara saduwarmu,wannan Shine dalilin barin gidana,zuwana Nageria da Fadowata hannun Mallam duk banda masaniya akansa,Nasan dai na zauna daku,kun rikeni tamkar dan”uwanku har zuwa bani Auren Suwaiba da Mallam yayi_

   Gabadaya wajen aka sauke ajiyar Zuciya,Kawu ne yayi Saurin cewa “Ranka ya dade ka yanke wani Abu daga cikin lbrin,yaya akayi sammun da kurciyan suka sake ka har ka iya komawa gida,har tsawon wannan lokacin..? Daman tambayan dake zukatan mutane kenan.

Maimartaba yayi mirmishi yaciga da cewa………”

   _Daman Na fadamuku kurciya sukayimin  na barin gida,tare da sammu bazan Tuna asali na ba balle har wadanda zasu tsinceni suyi Tunanin maidoni gida,Bayan mallam ya aikeni da kudi nakai sako,nidai nasan na hau mota har nasauka,sai dai kafin na karisa cikin kasuwar wani al”amari yafaru dani,naji kamar Amciremin wani Abu atsakar ka,na zabura ina bin ko”ina da kallo,lokaci daya ina kallo kaina,kaina ya Daure,meyakawo nan,nan dai ba garinmu bane,nan ba Masarautarmu bane,kuma sannan wadanan mutane ban garinmu bane,kuma suma din ba Ahalina bane to ina ne nan?Tambayan dana dinga yima kaina kenan,ammh bansamu wanda zai bani amsa ba,inda Abun ya sakeni,daganan bankara daga kafata ba,tsaye nayi ina ta zare ido,kana ganina zaka Fahimci bana cikin hayyacina ga damuwa data bayyana zahiran acikin idanuna,wani bawan Allah ne yazo wucewa sai yaganni kamar cikin damuwa,koda ya tambayeni meke damuna ina zani? ban iya mai mgana ba illah FasheWa da kuka danayi,hankalinsa ya tashi ya Shiga tambaya Abunda ya faru,bazan iya maida komai illah na sanar dashi ina Tunanin Sato ni akayi,domin ni dan Niger ne,ayanki Agadez,jin wannan lbrin nawa yasa yatafi dani gidanshi da alqawarin Taimakamin nakoma gida,kwana biyu nayi agidanshi,kuma har nagama kwanakina banta tambayansa wani gari bane,kudin da mallam yabani na aike dashi mutumin yayimin kudin mota zuwa niger bayan na tabbatarmai da zangane gida,Sauran kudin kuma na dankamai,Tunda ni duk Atunani daga Masarautarmu aka satoni da wannan dukiya,Allah bai basu sa”ar cinma burinsu akaina ba,cikin dare na isa garin kai tsaye masarauta na dosa,ina kuma Shiga sashen mahaifiyata nafara isa,wacce na isketa tana tsayuwar dare,ganina datayi bata razana ba,takamani ta Rumgume tana kuka tana godiya ga Allah,tace tasan cewa zan dawo ko bajima ko badade,bawanda yasan lbrin dawowata gida sai washegari da safe,kuma adaren Ummah na Tafadamun duk irin mulkin kama karyan da IDIRISA Yake aikatawa Tare ta taimakon yan”uwansa,da irin yadda suka lalata komai na Masarautarmu,koda ummah tatambayeni ina naje,kuma awani gari na zauna,Abu daya na iya gayamata Cewa mutumin daya tsinceni ya sanar dani ina Nageria ne,ammh bayan nan bazan iya dora komai ba game da barina gida ba_

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button