ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 31 to 40

  Ido take warewa taga daga ina muryan take,Maimartaba dayaga haka sai ya sanya hannu,ya yaye Rawanin dake kansa duka Fuskarsa ta bayyana Tuni fadawa suka Zube suna Fadin”Allah karama Sarki hakuri,Allah ya Huci Ran maimartaba Ayimana Afuwa munga Abunda baidace mugani ba kai tsaye wato Farar Fusjarka mai cike da haiba da zati,Tuba muke Ranka ya dade..”Goggo data kafe idonta kan Maimartaba Taja baya da Sauri Tana Nuna hannu,Maimartaba take Nunawa tana so tayi mgana takasa dakyar ta iya Furta”Ya..Yaa…Kassn wa…Na..Ke …Ganii….”Tafada idonta na Kafewa lokaci daya bakinta ya Subuce ya Furta… *AB…DUL….NA….SEEEEERRRRRRR…….”Kafin kawai ta Sulale zata zube kasa kafin Aliyu ya isa gareta maimartaba yayi Sufa zuwa gareta ta Sulale bisa jikinsa.

   *Janafty…*

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

     *Chapter..32…*

  “”Gabadayansu sukayi kan goggo wacce ta sulale bisa jikin maimartaba,dagota yayi yana jijjigata yana kiran Sunanta”Suwaiba..Suwaiba..”Ammh ina ko motsi batayi,gadanga ne ya Runtuma daki aguje ya dauko ruwa yana zuwa ya duka,maimartaba ya mikasa Tafin hannunsa yana kallonsa kai Tsaye ya tsiyayamai Ruwan ahannunsa yayarfe kafin ya Shiga Shafe fuskar goggo dashi,lokaci daya ta saki ajiyar zuciya kafin tafara kokarin bude ido,tana budewa taci karo da Gadanga,sai kawu sai Umaimah da Haisam,sai Jabir dake gefe,chan ga Mardiya da madina,sai Umar dake durkushe gefe,jin ta ahannun wani ne,yasa ta dago ido Fes ta saukesu kan Maimartaba wanda ke kallonta yana kara godema Allah…

Zabura goggo tayi daga jikin maimartaba tana Raba ido don ita azatonta mafarki take,Nunashi Tahauyi tana Fadin”Yaya kaga Abunda nake gani kuwa..”Da hanzari kawu bala ya karisa gareta ya rikota yana Fadin”Nagani Suwaiba ki Natsu kikuma godema Allah dayasan zaku kara ganin juna dukkanku kuna raye..”Fashewa da kuka goggo tayi tana lafewa jikin kawu,tamaki kara dagowa ta kalli maimartaba.

Aliyu ne ya Shiga daki ya Fito da wani kafet,babba da wasu manyan Tabarmu yazo su Haisam suka kamamasa ya Shimfida atsakar gidan,saman kafet din nan maimartaba yazauna da iyalansa sai Tabarmu su Kawu bala suka zazzauna wanda ke rike da goggo yana lallashinta,Da hannu Maimartaba ya yafito Aliyu,Jikinsa na rawa ya mike ya isa ga mahaifinsa Yana kokarin zama,Maimartaba ya rikosa yana Fadin”Aliyu…”Yafada yana shafa sumar kanshi,Ummah mai babban daki ta riko hannu Aliyu tana Fadin”,Sannu sabon megida..”Mirmishi ya saki yana binta da kallo,Kusa da maimartaba ya zauna yana kallon Su Zafira,wadanda ke dagamai hannu suna dariya,shima dagamusun yayi yana mirmishi gimbiya Razeenah ta Dafa kan Aliyu tana mirmishi tace”Sannu magajin Sarki..”Tafada tana kallon gefen gimbiya Fasilatu wacce ta cika ta batse kamar ta fashe 

Goggo ce ta dago tana kallon Aliyu,wani harara ta zabgamai kafin tace”Yana raye,ammh Shine yabarmu baitaba waiwayanmu ba tsawon wannan lokacin? Tafada tana Tsiyayan hawaye sai wajen ya dauki Shuru kukan goggo kadai akeji,Ana cikin hakane sai ga mallam lawal Shida inna Ramatu Sun fado gidan,domin inna ramatu na ganin Abunda ke Faruwa takoma gida ta sako mayafi tatafi kasuwa ta fesama mallam lawal,tatasoshi kuma agaba saboda in ba dashi ba,bazata samu damar Shiga gidan goggo ba balle hartaji mai ke Faruwa,kawu na ganinshi yatashi ya rikosa yana Fadin”Alhamdulillah barka da zuwa mallam lawal kazo akan gaba don kaima kana da jibi da wannan Ahalin..”,Yafada yana kariso dashi gaban maimartaba yana Fadin”Ranka yadade,wannan mallam lawal kenan uba yake ga matar da Aliyu yake aure,kuma uwa uba shi na damkama amanar Suwaiba tun bayan dana kawota garin nan,su sukayi hidima da ita har zuwa haihuwar Aliyu,mallam lawal kai kuma wannan dake gabanka Mahaifin Aliyu ne,kuma Sarki ne na Kasar Niger”Ba mallam lawal da”ake ma bayani ba inna Ramatu ce,wacce ke tsaye ta zabura tana dafe kirji da karfi ta Furta”Mahaifinsa? kuma sarkin Niger to ya akayi haka? Tafada cikin Rudewa..

Kowa kallonta yake,yana mamakin kalamata,su Maimartaba ma sun zata mahaukaciyane,ganin yadda ake kallonta ne,yasa Tayi Saurin dukar dakai tana Raba ido,Fadawa ne suka dakamata tsawa suna Fadin”Hattara dai Diyar talakawa ba”a mgana indai sarki bai bada izini ba hattara Dai…”Inna Ramatu da jikinta ke rawa ta duke ta kyarma ganinsu da bulalai,kawu ne yasa baki yace”Ku kyaleta maidakin mallam lawal ce”Shiko yana gaban Sarki durkushe kamar ya kwantamai,idanunsa sun cika da kwallah,Mikasa hannu maimartaba yayi yana Fadin”Mu gaisa Tukunnah…”Kasa mikamai hannu Mallam lawal nokewa yakeyi yana Fadin”,A”a Ranka ya dade,Talaka kamata baidace na yi hannun dakai ba,Allah yakarama yawan Rai..”Mirmishi kadai sarki yayi yana Fadin”Ina Surukata take..”Yafada yana kallon goggo,wacce kanta ke duke tana Sharan kwallah.

Azeema dake Gefe tana Raba ido,Kowa yasama ido ganin yadda suke kallonta ne yasa duk taji kunya,sai tahau Sunne kai,Hannu maimartaba yadaga yana Fadin”Taho diyata taho nan ki zauna..”Jikin Azeema amace tamike ta isa gaban maimartaba ta durkushe kanta ya Dafa yana sakamata albarka,nan Ummah mai babbar daki tajawota tana Fadin”Taho nan kishiyata,dani zaki zaman kishi don kinganni nan,inba Aliyu ba sai Rijiya mai gaba dubu..”,Dariya aka saka,itama Azeemar yar dariya tayi Kusa da gimbiya Razeenah ta zauna ta Sunne kai,itako gimbiya Razeenah ko ajikinta ta Rumgume Azeema tana mata rada akunne,tsam naga tatashi takoma kusa dasu Zafira wadanda ke gefe sun kame,Su jabir dake Facing dinsu su suka kurama ido suna yaba tsari da kyan yan matan,Washe baki sukahau yi Suna Fadin” Our princess daya tilo A masarautar Tambari buzu..”Dan ware ido tayi tana kallonsu kafin ta Shiga tambayan sunayensu suna Fadamata tana gyada kai… 

  

Kawu Bala ne yayi gyaran murya yana Fadin”Ranka ya dade zamu so muji meyafaru ne,Tun bayan aiken da mallam yayi maka baka dawo ba,munyi nemanka har ba Adadi har muka cire da cewa baka da rai ne..”Maimartaba yayi Shuru kafin ya gyara zama yana Fadin”Ko baka Fadamin ba, Nasan cewa Allah ya karbi Ran mallam da inna..”,Gyada kai Kawu yayi yana fadin”Dalilin Shiga damuwar Batanka da bullowar ciki ajikin Suwaiba Shiyayi sanadiyar Jininsa har ya hau,bai dade yana jinya ba,Allah ya karbi Abunsa itama inna bata dade ba tabishi Tsakaninsu kwana 52 ne..”Yafada yana Share kwallah,don ji yake kamar yanzu Abun ke Faruwa..

Goggo ma kuka take sosai,domin mutuwar iyayan nata sun dawo mata sabuwa,Maimartaba daya dukar dakai ya dade bai dagoba yana dagowa Sai ga hawaye shar suna zuba Fadawa keta kirari suna Fadin”,Allah huci Zuciyar maimartaba,Allah ya sanyaya zuciyar Adalin Sarkinmu..”Hannu ya sanya ya share kwallar yana Fadin”Hakika munyi Rashi,Allah yajikan mallam da Inna Allah ya sanya sun Huta..”Da Ameen aka amsa,wajen yayi Shuru kafin Maimartaba yayi gyaran murya yana Fadin”

  “Kamar yadda kuka sani Nazo garin nan bani da kowa,nazauna a hannun mahaifinku har na tsawon wasu Shekaru,kafin yarda da aminci yasa ya dauki Auren yarsa yabani..” yadanyi Shuru kafin ya Numfasa yacigaba da Fadin”Tabbas koda nazo garinnan bani a hayyacina sakamakon kurciya da”akayi min,kuma aka hadamin da Sammu,wanda zan manta Asali na ,banda sunana ba”a barni na Tuna komai ba..”,Gabadaya suka zubamai ido suna kallonsa,bai wani damu da kallonsa da sukeyi ba,har goggo wacce ta maida hankalinta kanshi,tayi tagumi da hannu bibbiyu,Ya cigaba da Fadin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button