ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 31 to 40

Lalle Azeema kina Ruwa????Toh duk cikin gadanga ne ya jawo haka,ai shi gadanga in yaji lbri Kakarshi tayanke saka????????

    •°•°•°••°•°•°•°•°••°•°•••°

   _Babbar headquater yan sanda na garin gombe_

Ababbar Headquater su na nan garin gombe aka kai Azeema aka sakayata,babu fada ba zagi,ba duka sai dai zaman waje daya da Takura,sai kuma Rashin samun barci ga Sauro kamar mutane,ga kudin cizo ga kwarkwata,da suke bin jikin mutane,sai Rashin abinci mai kyau,watarana ma sau daya ake bata Arana,Tun Azeema na ganin Abun Wasa har ya wuce Tunaninta bata yi Nadamar Soyayyar yaya captain datakeyi ba,ammh tafara Nadamar mugun halinta Da Zigan Shedan gareta,domin Tunda aka kawota take Fama da wani ciwon kai mai Tsanani,ga Nauyi da kirjinta keyi,saboda yadda Abubuwa sukayimata yawa,bata da wani aikinyi sai kuka,Tanaji Aranta indai bata samu captain ba,toh sai dai Tarasa rayuwarta don Tun yanzu Tafarajin Alamun Rashin Captain gareta Abu ne da zai iya sawa tarasa rayuwarta.

Haryau da”a kawota aka sakayata bawanda yakara lekota,balle abi ta kanta batama kara ganin kowa ba,sai Wadanda ke kawomata abinci,basu cemata uffan,itama bata ce musu iyakarsu su ijiye Abinci su Rufeta su kara gaba,Abincin ma sai yazamana ba kullum take ci ba,sai dai tatasa Abinci agaba tana tsiyayan hawaye,Tabbas Azeema tafara Nadamar Abunda ta aikata,ammh wannan Soyayyar datakema Captain babu Abunda yaragu saima karuwa.

   ****************

_Kaduna_

 Yau dai yawon Umar yakaishi har Wajejen da gidajen su captain suke zaune,hakika wajen ya burgesa balle yadda aka Tsara gidajen ajera komai iri daya babu bambamci,kamar wani Estate,wajen yamatukar burgesa sosai Shiyasa yake ta Daukan Gidajen hoto,Yaji yana kaunar Sojojin Nageria domin Sun Fisu moran Abubuwan yaki da Sauransu,Yau din sanye yake da kayan gida,riga da wando black and white,sai ya sanya bakar jaket kansa babu hula sai Nannadaddan gashinsa daya murde waje daya,kana kallonsa zaka san wannan Buzu ne na gaba da baya.

 Ta bayan gidajen ya bullo,shiyasa bai Kawo gidan Aliyu ba,sai da ya wuce na Jabir,gidan Aliyu yana Jerin Farko ne,don Shine No5,yazo ta wajen kenan yana Daukan Hoto,tare da video,tsaye yayi cak yana bin wajen da kallo,lokaci daya yaji yanayin jikinsa ya canza,tsayawa yayi yana waige waige kafin kuma ya dawo ya cigaba da Abunda yakeyi.

 Aliyu dayake sanye da kayan Jc Riga da wando ya bude kofa ya Fito,kafarsa sanye cikin wani Farin takalmi,domin duka kayan jikinsa Farare ne,yana Fitowa yaci karo Da Umar ya juya baya yana Daukan Hoto,ta bayanshi Aliyu ke kallonshi ammh sai da gabansa ya Fadi,yayi baya yana laluban wayarsa Jabir ya Turama Text da cewa”,_Dude come out..I think na kama wani dan leken Asirinmu_..”

   jabir dake kokarin Fitowa Jugging yaga sakon Aliyu da hanzari yakoma daki ya sako karamar bindigarsa ya cogeta abayan wandonsa Ya fito,yana Fitowa yaci karo da Umar,wanda yagama Daukan baya ya juyo ta gaba ta wayarsa yana Dauka karaf ko ta cikin Wayar ya hango Fuskar wani kamar Fuskarshi,mamaki yakamashi sai ya zata ko yamaida Abun Hoton ta gabane,ammh kuma wannan ai ba Kayan jikinsa bane,Kara ware ido yayi yana kallon Aliyu wanda ke Dago kai yana So yaga Fuskar Umar din,Da hanzari Umar ya Jaye wayar Hannunsa Fuskar Aliyu ta bayyyana Azahiri agabansa.

 Aliyu dayake leken ganin Fuskar ko waye,Umar na jaye wayar ya Daskare Atsaye yana binsa da kallo daga sama har Kasa,Zuciyarsa na lagude,mai kama dashi yake gani,ammh kuma sanye da wani kaya dabam,Umar ma Kallonsa yake Yana kuma kara Bin kansa da kallo,kamar yadda Aliyu keyi,Jabir Tunda ya Fito idonshi ya Sauka kan Umar,yazata Aliyun ne,yafara Taku zuwa gareshi sai kawai ya hangi Aliyu akofar apartment dinshi,ware ido yayi yana bin kowannensu da kallo bakinsa na Rawa yama kasa mgana,sai ya kafe Aliyu da ido na Tsawon Lokaci sai yakoma ya kafe Umar da ido,nan take ya Fahimci Abokinsa na gaskiya ammh fa sai da ya Sha kallonsu dakyau.

   Aliyu da Shiga mamaki yafara daga kafarsa yana takowa zuwa ga Umar,wanda Shima yake takowa zuwa ga Aliyu dukkansu sun kafe juna da ido,kowannen Zuciyarsa na bugawa Jabir dake tsaye gafe sai kawai ya saki baki yana kallonsu sanda suke kusanto juna,bala”i wannan wace irin kamace komai nasu iri dayane hatta da Gashin kansu Wlh hatta Fuskarsu iri dayace babu bambamci,sai dai Shi Umar yafi Aliyu jan Fata sosai,sakamakon Mahaifiyarsa Buzuwa ce,shiko Aliyu ya surka da Fatar goggo shiyasa sai yayi Duhu kadan,Kana Aliyu yafishi Tsawo da murdewar jiki,duk da Shima Umar din ba baya ba.

 Da gudu Jabir ya karisa ga Aliyu yana Rikemai hannu yace”Shine Dude wlh Shine…”,Da mamaki Aliyu ke kallonsa yana bin kuma inda yake Nunamai da hannu kafin ma yayi mgana Jabir ya rigasa da cewa”Shine nagani Ranar,na zata kaine wlh Shine…”Aliyu bakinshi ma yakasa mgana Illah kurama Umar ido dayayi Shima Umar din agaban Aliyun yaja ya tsaya yana kallonsa kur ko kiftawa bayayi,atare kowannensu yanuna dan’uwansa yana Fadin”Waye kai…? Suka Fada bakinsu na Rawa atare.

  Mirmishi kowannensu ya saki ganin sun samu Gamuwar mgana atare,Jabir dake gefe yayi tsalle gefe yana fadin”Wlh Allah Dude har mirmishinku iri dayne,wai kodai Ku yan biyu ne,baka sani ba..”Yafada yana Rike haba Abun fa yabashi mamaki,hannu Aliyu ya saka a aljihu yana Fadin”I don”t Think so Dude ai da goggo ta Fadamin,ammh kuma meyasa nakejin wani Abu game dashi,inajin zuciyata na wani Rawa in ta kalleshi..”Yafada yana kallon Umar din.

 Umar yayi ajiyar zuciya yana Fadin”Nima haka nakeji Araina,zuciyata tana gayamin Kai din wani ne agareni,ka taba zuwa Niger ne..?Kallonsa Aliyu yayi yana fadin”Kai daga chan kake? gyada kai Umar yayi yana Fadin”Eh ina daga cikin Sojojin gamayayyar nan,.”gyada kai Aliyu yayi kafin yamikama Umar din Hannu yana Fadin”Good ni kuma Sojan Nageria ne,am *CAPTAIN ALIYU ABDULNASEER TAMBARI BUZU* Kaifa..? Umar yaciro hannu da niyar yamikama Aliyun ammh jin Furucinsa na karshe yasa yayi Saurin dauke hannunsa kamar ya razana gabadaya idonsa awaje yana nuna Aliyun.

 Jabir da Aliyu suka bisa da kallon mamaki kafin Aliyu yace”Lafiya kuwa…?Bakin Umar na Rawa ya nuna kansa yana Fadin”ni…Ni..Ma Suna…na *UMAR ABDULNASEER TAMBARI BUZU* kuma Tambari buzu masauratarmu ce,mukadai keda wannan Sunan ta masaurata,kuma mahaifina Shine *SARKI ABDULNASEER TAMBARI BUZU MAI MULKAN MASAURATAR TA TAMBARI BUZU WACCE KE YANKIN AGADEZ*…!

 gabadaya daga Jabir har Aliyu daskarewa sukayi Aliyu dayaji wani Abu ya wucemai ta makogaro,yayi Saurin Riko kafadun Umar yana Fadin”Da gaske kake yi? yafada kamar yafita hankalinsa Umar ya gyadamai kai,kafin ya samu zarafin mgana Aliyu yace”Mahaifinka yataba zuwa Nageria achan baya,ma”ana katabajin lbri..? Shuru Umar yayi kafin yace”Eh Tabbas Abbah ya Fadamin shima yayi Rayuwa A Nageria,ammuh bazai iya Tuna a ina ya rayuwa ba,balle ya Tuna da Wasu Ahali yayi Rayuwa ammh Tabbas koda zan Taho din nan ya jadaddamin shima yayi Rayuwa A Nageria..”

  Aliyu da Wasu hawaye masu dumi da sanyi suka wankemai Fuska,yayi Saurin Rumgume,Umar yana Kuka Muryansa abude yake Fadin”Wlh Dan”uwa ne,dan”uwa ne yau naga wani nawa yau na hadu da jinina,yau nazama kamar kowa yau zanji lbrin mahaifina,wanda banta gani ba Tunda nazo Duniya Allah na godemaka Alhamdulillahi..’,Yake Fada yana kuka da duka muryansa yana kara kamkame Umar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button