ALIYU GADANGA Page 31 to 40

Azeema ko dakyar bayan tayi wanka ta iya Shirya ta Fito,cikin wani dogon Hijabi tana ta Faman sunne kai take gaishe dasu kawu,amsawa sukayi cikin sakin Fuska,Su hibba suna ganin Azeema suka saki Aliyu suka nufeta suka Rumgume suna murnan ganinta,dariya take itama tana rikosu,Gaishe dasu Anty madina tayi kafin ta waiga tana gaida Jabir da Haisam,Haisam kadai ya amsa Shiko Jabir cewa yayi”Sai yanzu kika ganni madam”Yafada yana wani bata rai,kunya takama Azeema ta sunne kai Su Anty madina na kallonta suna Fadin”Masha Allahu Allah ya raba lafiya( Don Tuni lbrin yakai musu).
°•°•°••°••°•°••°••°••°••°••°••°
Karfe 12:30am na Safe Jirgin su Maimartaba yayada zango a babban birnin Tarayyah Abuja, mai girma Shugaban kasamu *GENERAL MUHAMMADU BUHARI* da kanshi yazo ya tarbi maimartaba Abdulnaseer Tambari buzu tare da iyalansa da Kuma wasu daga cikin Masu kula da masarautarsa,kamar irinsu Shamaki, da Sarkin gida sai kuma bayin da”aka zo dasu mata da maza,daganan gidan gwannati,sukawuce sai da suka huta sukaci abinci maimartaba suka kara gaisawa da Shugaban kasa kafin kuma,jirgin ya kwashe su zuwa Gombe.
Koda karfe biyu Tayi jirginsu Maimartaba Tuni ya yada zango Afilin jirgin dake gombe,inda anan ne mai girma gwannan Jahar gombe tare da maimartaba Sarkin gombawa suka zo suka tarbesa,Sai da suka fara zuwa gidan gwannati kafin su rankaya zuwa Masarautar gombe,achan ne sukaci abinci suka huta bayan an Shiga dasu Gimbiya Razeenah Shashen matan sarki bayi kuma ankaisu barayin bayi,shiko maimartaba yana tare da Sarkin gombe suna tattawa,bai boye masa komai ba yadan gutsira masa kadan daga Abunda yakawosa,Maimartaba Sarkin gombe yayi murna sosai,sun jima suna tatttaunawa sai bayan sun yi la”asar a babban masallacin Cikin Masarautar kafin Maimartaba Sarkin Agadez yayima dansa waya Wato Yarima Umar yana Fadamai gashi sun iso,wani anguwa ne Suwaiban take zaune,ba bata lokaci ya sanar dashi Sunan anguwan da Aliyu ya sanar dashi,Maimartaba ya sanar da sarkin gombe wanda ya jinjina kai yana Fadin”Anguwan marasa hali ne,anguwan tana cikin garine bari ashirya motoci yanzu sai ku tafi..”gyada kai Sarki Abdulnaseer yayi yana ma sarki godiya.
Shiko Yarima Umar suna gama waya da maimartaba yakira Aliyu ya sanar dashi wanda yana cikin falon goggo yaga kiran Umar,din da hanzari yafice jin Gasu maimartaba nan karisowa yasa yakira jabir awaya yace asameshi awaje,yana Fitowa Aliyu ya wurgamai key din mota yana Fadin”Maza kaje kataho da Umar,gasu Abba nan zuwa..”Jin haka yasa jabir chabe key din yana fadin”angama Angon Azeema..”Yafada yana dariya kan ya Fada motar yabata Wuta ya Fita daga layin da gudu,cikin gida Aliyu yakoma yana kallon goggo yadda ta ware cikin ya’yan yanuwanta anta hira,Wani Farinciki yakeji aransa,domin burinsa bai Wuce ganin goggo cikin Fara”a ba.
Ba dauki minti talatin ba, Tambari tare da busan algaita suka cika anguwan
*KAGARAWAL* Motoci ne masu rai da lafiya daga Fadar sarkin gombe guda Bakwai suka jero cikin anguwan,daya daga cikin wata doguwar Farar motace wacce maimartaba Sarkin gombe ke hawanta,itace Sarkin Agadez ke ciki Shida iyalansa,Ga kuma yan Sanda harda mobile police,Saboda yanayin cinkuson anguwan sai da Fadawa suka sassauka suna dan bin motan da dugu,Fadawan sun hada dana Sarki gombe ne,dakuma na Sarki Agadez,jin wannan busan algaita,yasa kowa yayi waje yana kallon Abun mamaki,sarki guda a anguwansu,Harda mata masu leke ta gadanga,Daidai lokacin motar Aliyu ta Shigo Layin Wanda Jabir ke ciki Shida Umar,ganin yadda wurin ya cinkushe yasa Umar Fitowa yakarisa da gudu ga motar mai martaba yana Nuna ma Direba kwanar gidan goggo,atare motocin suka dinga shan kwana,suko Su Zafira take cikin mota sunata kalle kalle Suna Fadin”La ga yaya Yarima..”Suke Fada suna nunasa murna ta cikasu,itako gimbiya Fasilatu wani kallo takebin anguwan da kallo,Aranta tana Fadin”Kaskanci ne Sarki guda ya Shigo wannan anguwan..”
Su goggo na gida suka Fara jiyo Jiniya da algaita,ba wanda yanuna mamaki,sai goggo wacce ke fadin”To kuma yau wani babba ne yazo anguwan Tamu,Allah yasa mai girma gwanna ne yazo mganar gyaramana mana Titin anguwa haba abu duk ya lalace”Dariya aka sakamata itako ko ajikinta,Motocin mai maimartaba basu ja Tunga ba sai akofar gidan goggo wanda makota dana kusa dana nesa kowa ya Fito ganin Abun mamaki ciki harda inna Ramatu wacce ta Fito ko mayafi bata dashi,duk ta rame saboda Rashin Azeeza ido ta zaro lokacin data ga Fadawa da Sauri Sun Fito dawani katon Capet dogo sun warwareshi Tundaga Kofar gidan goggo har cikin gida inda Sarki xai taka kenan,suko suna cikin gida sukaji shigowar Fadawa suna Shimfida capet,gabadayansu sukayo waje,goggo ce ta zare ido tana Fadin!Wannan daga ina? yaya kamar Kayan Gidan Sarki ne ajikinsu,munbani me mukayi kuma? tafada cikin Rudewa,Kawu ne ya riketa yana Fadin”Natsu Suwaiba babu Abunda zai Faru sai alheri..”
Awaje kuwa Umar ne ya kariso dakanshi ya budema maimartaba kofa,Mutame kuwa baki suka bude suna kallon Abun mamaki,don su Azatonsu Umar Aliyu ne fa,Shiyasa Abun ya dauremusu kai,su duk atunaninsu Sarkinsu ne yazo gidan goggon,Basu cika da mamaki ba Sai da Sarki ya bayyana awajen,Fadawa kuwa sai kareshi suke suna kirari da cewa”Allah ya taimaki Sarkin Agadez..Allah ya taimaki Adalin Sarki mai mukin Masarautar Tambari buzu takawarka lafiya sarki jikan Sarki,kuma ka haifi sarki da yardan Allah…”Hannu kawai Maimartaba Sarki gombe yake daga musu yana Sanye cikin wata alkayaba mai kyau da tsari,ga wani Farin Rawani,wanda ya Kafemai bisa kai,daga wajen bakinsa Farin Rawanin yadan Rufemai baki har zuwa hancinsa kafarsa sanye cikin wani ubansu Takalmi na Jinin Sarauta,Kana kallonsa kwarjinsa zai dakeka,koda yake cikin Rawani kana iya hango hasken Fatansa da Karan dogon hancinsa,Mutane sai Wage baki suna kallon mamaki,don dai koda kallon Farko sunsan wannam ba Sarkinsu bane,Gabadaya Su Ummah mai babban daki suka Fito kowannesu cikin Shigar kayan Sarauta,suma bayinsu da da Fadawan masarautan Agadez suka jera layi,suna zuba kirari,mutane basu kara tsorata ba,sai da su Zafira da Safaratu suka Fito,dukkansu cikin Wasu alkayabba masu ruwan Zaiba,sunyi matukar dacewa dasu,Abunda yaba mutane mamaki kamaninsu da gadanga Zahirin gayinan ya bayyana,suko sai bin mutane suke da kallo,don basu saba Fita waje ba,ko mkrantarsu acikin masarauta take.
Ana zubama maimartaba kirari,Fadawa na karesa Umar ya bashi hanya yafara taku zuwa ciikin gidan goggo hannunsa rike da wata sandar zinare,ta gidan Sarauta Jabir dake baya yana leke,baki ya rike yana fadin”,Tabdijam wani Abu sai gidan Sarauta..”mutane kowa harda masu zubar da yawu saboda kallo,ciki harda su inna Ramatu,wacce saboda kallo,harda Faduwa tayi, idonta take murzawa don ita gani take kamar mafarki take,ammh sai me agaban idonta Sarkin Agadez ya Shigo gidan goggo bayanshi kuma su Ummah mai babban daki,dasu gimbiya Razeenah sai gimbiya Fasilatu sai su Zafira dasu Jabir kana bayi da kuma su Sarkin gida daga baya.
Goggo ba inda jikinta baya Rawa,kirarin Fadawa yafaramasu goggo maraba,Kafin sarki ya bayyana acikin dan Filin Tsakar gidan,Goggo wace ke Rumgume da kawu tabi Su da kallon mamaki,daidai lokacin da Su Gimbiya Razeenah suka gama Shigowa sai gasu Zafira,sai yarima umar ya bayyana yana mirmishi,Aliyu dake chan baya ya dagama hannu alamar jinjina,Goggo data tsaida idonta kan Umar tayi wani shock ya shigeta A gauggauce ta Fizge jikinta daga na kawu tana nuna Umar,kafin tama samu Zarafin mgana gadanga ya bayyana agabanta,Yana mirmishi Azeema ma dake gefe,Ma ware ido take tana kallon mai kama da mijinta ballema Su Madina da suka daskare,hannu goggo ta sanya tana riko Gadanga,Umar take nunamai da hannu tana so tayi mgana takasa,idontane ya sauka kan Zafira cak goggo ta tsaya tana wani Nuna hannu kamar tafita daga hayyacinta,shiko Sarki Abdulnaseer Tsaye yake cak yana bin goggo da kallo,ko Shekara Dari Suwaiba zata yi bazai taba mantawa da Fuskarta,Tuni yaji hawaye sun tahomai,Baisan sadda ya Furta “SU…WAI…Baaa…..”Yafada hawaye suna zubomai,Wata murya goggo keji wanda ko mutuwa tayi tadawo bazata manta mamallakin muryan ba.