ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 31 to 40

   _Bata Fadama kowaba sai Awashegarin An zauna zaman Fada kwatsam sai gani na Shigo,gabadaya Aka mike ananeman guduwa,don kowa ya cire rai da ina raye,nan take kuma Sarki ADIRISA yamike jikinsa na rawa daga kan karagar mulki,yana nunani da hannu,yana so yayi mgana ammh yakasa,nan da nan sai bakinshi ya karkace yafadi yana makyarkyata anan take yasamu ciwon Shanyewar barin jiki,wanda hakkina ne ke bibbiyarsa da kuma asirin da sukamin na barin gida,Domin da bakinsa yafadi Abunda suka aikata agareni dasa hannu yan”uwanshi da iyayensu mata,da Hadin bakin Jakadiya suka kashe mahaifina Sarki YAKUBA,Tare da yimin kurciya na bar kasar gabadaya bayan sun hadamin da mugun sammu,wanda banda sunana da kasata bani da ikon Tuna komai,kuma ko bayan kurciyan ta sakeni sammun dake jikina bazai barni na Tuna wani Abu bayana ba,sai wanda zai Faru agaba,Sun sanar damu cewa sammun yana dadewa jikin mutum kafin ya sakeshi,shine dalilin daya samu damar hayewa karagar mulkin MASARAUTAR TAMBARI BUZU,jin jaka yasa al”ummah yankin Agadez da Masarautar Tambari buzu tayi tir dasu,Sarki IDIRISA Kuwa sati daya yayi Allah yayimai Rasuwa,saura yan”uwansa kuma hukumar gidan Sarauta ta hukuntasu,harda jakadiya wadanda ta yanke musu hukunci kisa ta hanyar sare musu kai,suko iyayansu mata masarauta ta koresu daga yankinta gabadaya Fadawa suka rakasu har wajen gari suna jifansu da Allah tir dasu,bayan an gargadesu da har abada kada sukara tako kafarsu zuwa masarauta_

    

   _Bayan lafawar komai,akama bama mai wuri wurinsa ma”ana akayi min Nadin Sarkin Yanki Agadez Amsarautar Tambari buzu wanda aka kwana ana shagali,wanda al’ummah suka nuna Farincikinsu,Talakawan Agadez sun nuna murnansu sosai wanda aka dau tsawon sati daya ana Shagalin Nadin Sarautata,zuwa wannan lokacin da”a ka nadani amtsayin Sarki nakasa gane meke damuna,inaji ajikina akwai wani babban al”amari dake damuna ammh nakasa gane komiye shi,dama kuma ba”a Nadani Sarki ba sai da Na auri GIMBIYA FASILATU wacce ta kasance diyace ga sarki yankin Yamai,dake kusa damu,Bayan Nadin Sarauta ta kuma na Auri GIMBIYA RAZEENAH,wacce ta kasance jikar sarki Dosso ce,Bayansu bankara jin ina sha”awar kara aure ba,duk da sarakai suna ta kawomin Tallar Auren ya”yansu ammh na Fadama ummah cewa subarni haka bana bukatar kowa ayanzu,bayan hawa mulkina nayi canje canje sosai kama daga jakadiya dakuma masu zaman Fada duk munafukan dake tare dasu Sarki IDIRISA saida na saukesu nayi sabon Nadi tare da sabbin mukkarabai_

 

  _Akullum matana da mahaifiyata sun san ina da damuwa Araina Ni kaina ko sun tambayeni bani da amsan da zan iya basu,nikaina cikin wani sarkakiyane nakasa gane meke Faruwa,shekara ta daya Da komawa gida nafara wani mafarki wanda ke tsayamin arai,amafarkin ina ganin wata mata da danta suna kuka suna mikomin hannu,nikuma ko ina da niyyar Zuwa wajensu domin taimakamusu sai wani hayaki ya lullubesu koda hayakin zai washe,sai na nemesu na rasa,Tundaga ranar inda zan kwanta barci sai nayi wannan mafarki,kuma Allah baita nunamin Fuskar matar ba,kullum cikin mafarkin nan nake,tun Abun baya damuna haryazo yana damuna,balle matana wadanda ke tare dani,mahaifiyata tashiga damuwa sosai,tayi tasakawa ana kawo mata malamai wai suyi mata duba su gani meke damuna,ammh ko sun zaunar dani sun Tambayeni bana iya cemusu komai,Nidai Abu daya na sani babu maiyi sai Allah toh gareshi na maida al”amarina Shi zai yayemin duhu zuwa haske,na dau tsawon Shekara talatin ina wannan mafarkin Allah baita warwareminshi ba,sai acikin wannan Sati Allah ya bayyanamin Fuskarki amafarkina Suwaiba ina ganinki na Tuna,bayan na Farka ina kiran sunanki,Sai matana da mahaifa suke ganin kmar nayi gamone,kwana biyu akwance ko Fada bana zuwa,ina zurfafama kaina Tunanin kozan iya Tuna awani gari muka zauna dake,ammh tabbasa na tuna kedin matatace,toh ina cikin wannan halin sai na samu kiran Da’na Yarima umar ya sanar dani Ragowar Abunda ya Shigemin Duhu,na ganin yaron da kika haifamin,bayan Tsananin kamaninsu kuma suna amfani da sunan mahaifi daya tare da sunan Masarauta,Aranar hadda Bala munyi mgana bayan ya tabbatarmin da kina raye,ni na hana agayamiki komai nafison nazo dakaina ki ganni na ganki bayan na baki lbrin duk Abunda yafaru Shekarun baya,Wannan itace mahaifiyata yafada yana nuna Ummah mai babban daki sai Matata ta fari Gimbiya Fasilatu ita ta haifarmin yaro namiji mai suna Umar gashinan,sai gimbiya Razeenah mahaifiyar su Zafira da Safaratu kenan,Bayansu bankara haihuwa ba,bani da wasu ya”ya bayansu,ina Fata da wannan bayanin zaki dubeni da idon Rahama Suwaiba ki yafemin barinki danayi na tsawon lokaci batare dana waiwayeki ba.._

 Gabadaya wajen yayi tsit harda masu kwallah irinsu madina da mardiya da Ummah,Goggo kuwa kanta na bisa kafadan Kawu tana Fitar da kwallah,hatta Azeema sai ta koka,Maimartaba ma kukan yake ammh yana saka gefen Rawaninsa yana Sharewa ammh idonsa kur akan Suwaiba,Ummah mai babban daki ta mike ta isa ga Suwaiba ta dafa kadanta tana Fadin”Dago kanki Diyata…”,Jiki asanyaye ta dago tana kallon Ummah mai babban daki wacce idonta ya cika da hawaye tana Fadin”,wlh tallahi duk tsawon wannan Shekarun Abdulnaseer baiyishi cikin kwanciyar hankali ba,muma namu hankali ba”a kwance yake ba,kullum rokom Allah nake ya bayyana mai koma miye shi,gashi yau Allah ya amsa rokonmu kiyi hakuri kiyafamai nayi miki alkawarin bazai kara barin ki ba..”Tafada hawaye suna zuraromata Goggo da jikinta yayi sanyi ta dago tana kallon maimartaba wanda yake kallonta da tsausayawa kafin ta maida hankalinta kan Gadanga wanda ya hada hannayensa yana nuna mata alamar roko,Komawa da kallonta tayi kan su Madina taga suna gyada mata kai,balle kawu dayake ta murza kafadanta alamr lallashi,Kanta ta mayar kasa kafin ta share hawayenta tace”Shikenan…Na yafemai Duniya da lahira..”Ummah ta rumgumeta tana dariya Gabadaya wajen kowa ya sauke ajiyar zuciya harda maimartaba wanda yaketa maimaimata Alhamdulillah Aransa ashe afili yakeyi,gadanga ke kallonsa yana kunshe dariya.

 Ummah mai babban daki ta dago Fuskar goggo tana fadin”Sai wata alfarma daya danike rokonki Suwaiba.?.”Akunyace goggo tace”Mene ita..? Ummah na kallon Fuskar maimartaba tana Fadin”Ki Amince amaida aurenku da Abdulnaseer,In zamu koma Masarauta kibi mijinki ki koma tare dashi…”Gabadaya wajen aka Tsurama goggo ido,wacce kunya ta kamata kamar ta nutse,gimbiya Fasilatu kuwa kamar ta mutu saboda bakin ciki da kishi,Gimbiya Razeenah kuwa mikewa tayi ta isa ga goggo tana zauna tana riko hannunta take fadin”Kiyi hakuri karki ce A”a domin Maimartaba hankalinsa bazai taba kwanciya ba,balle har ya iya zaman Fada ba balle har ya gudanar da sha”anin mulki ba sai dake,don Allah ki amince amaida aurenku in zamu koma mutafi dake masarauta muzauna mu Rumgumi mijinmu don Allah…”Tafada tana kallon kwayan idon goggo,wacce saboda kunya kamar ta nutse,in tace bata son mijinta tayi karya,Shiko maimartaba idonsa na kan goggo gabansa na Faduwa kada Suwaiba tace”A’a…”

 goggo ta dago kanta ta bude baki zata yi mgana kenan su gadanga dasu madina suka hada baki suka ce”,Karki ce A”a goggo…”Suka Fada kamar zasu kuka,kawu yace”Toh kinji suma ya’yanki suna miki sha”awar komawa Rayuwar aure wacce zaki rabauta da ita har gobe kiyama..”Yafada cikin siyasa Ummah dake gefe ta dinga Kyaftama goggo ido????wai ta yarda goggo na jin kunya ta dago tana kallon maimartaba wanda ya Langwabe kai,alamar ki yarda dani,Saurin kauda kai tayi tana Fadin”Na Amince…”Ai gabadaya wajen ya dau ihu,Ummah ko ta ware ta dafa hanci ta saki guda,suko Fadawa nan suka fara busa algaita suna Fadin”Angaisheki giwar sarki,Angaisheki Gimbiyar Sarki…Sarkinmu na godiya ga Amincewarki Allah yabar soyayyah…”Dariya akasa gabadaya Goggo ko kunya kamar ta nuste,shiko mai martaba dariya yake har hakoransa suka bayyana waje yana kara godema Allah,addu”a Gadanga yayi aka Rufe taro da addu”a kafin abude shashenshi su Maimartaba aka Saukesu anan,itako Ummah mai babban daki tana dakin goggo ita da jikokinta ana shan hira da dariya,Ita dasu jabir da Haisam suna Fadin suma fa dole su garzayo masarauta sunga iri????????Ummah mai babban daki tana Fadin ba wanda zata bamawa,Suko su Zafira suna makale da Azeema wanda suke tare dasu Anty madina,Ummah ko natare da goggo wacce gimbiya Razeenah ta Shige cikinsu ana hira,Shiko maimartaba yana shashen gadanga,suna hira shida Kawu da Mallam lawal wanda kawu yake bama maimartaba lbrin Abunda ya Faru bayan tafiyan shi da dalilin barowarsu zaria yazo ya saima goggo gida anan,Maimartaba ya jinjina al”amarin kuma nan take yace zasu zaria har anguwan da suka zauna,dagachan sai ya wuce Fadar maimartaba Sarkin Zazzau,Gimbiya Fasilatu kuwa tana dayan bedroom din Gadanga tana Fama da bakinciki,Bayi kuma mata,dakin dake tsaKar gida aka Saukesu Maza kuma akwai wani daki a shashen gadanga ammh yana da kofa ta waje shi aka bude musu,inna ramatu tanajin sadda goggo tace ta amince da Auren sarki ta sulale ta fita tana zufa kafin kace kwabo tabi anguwa ta yada lbrin mahaifin gadanga Ashe sarki ne,goggo kuma matar sarki zama amaida aurensu tabishi chan masarauta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button