ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 31 to 40

  

__________________

    inda suka Faka motarsu wanchan karon,wannan ma anan suka ijiyeta,wato gaba da gidan goggo da kadan,Sun Fito daga motar suna waige waige neman wanda zasu Tambaya don lokacin wajen sha biyun Rana ne,babu kowa alayin,sai ga wani dan yaro wanda bazai Wuce shekara goma ba,da kayan mkranta ajikinsa da alama dai daga mkranta yataso,harya gota su Muneera tayi Saurin kiransa.

“Kai yaro zo nan..”Waigowa yayi kamar bazai zo ba,ganinsu yan gayu sai kuma yaje,ammh sai ya tsaya daga baya baya,mirmishi Muneera tayi kafin ta bude Yar karamar jakar dake hannunta ta zaro Naira dari tamikamai Tana fadin”Karbi dama tambayarka zamuyi..”Da hanzari ya karba yana washe baki,muneera tace”Gidansu wata yar budurwa mai Suna Azeeza,zaka ganta wata mai kiba Fara,idonta asama..”Shuru yaron yayi kafin yace”La Anty Azeeza kanwar Adda Azeema wacce ta auri yaya sojan nan gidan.? yafada yana nuna gidan goggo da hannu,Faduwar gaba ya ziyarci Ni”ima da Muneera atare,Suka kalli juna kafin su kalli yaron Muneera tace”Au dama yayartace ta Auri sojan nan gidan? yaron ko yawashe baki yana fadin”Eh mana gama gidansu Anty Azeezar nan,innansu kawar innanmu ce fa..”Zaro ido muneera tayi kafin tace”Toh mun gode jeka..”

  yako zura aguje yana murnan kudin da suka bashi,Hannu muneera ta saka bisa kugunta tana Fadin”Sweetheart anya ba gadar zare yarinyarchan ta Shiryamana ba,kiji fa ance yar uwartace ta Auri captain fa,? ni zuciyata na bani wani Abu dabam..’ajiyar zuciya Ni”ima ta sauke kafin tace”Nima Abunda ya Dauremin kai kenan,ammh karmu yanke hukunci mu Shiga gidan mugani,ammh da mamaki ace in har yar”uwantane kuma taso ganin bayan Aurenta..”Muneera batayi mgana ba,tayi gaba Ni”ima tabiyo bayanta suka Rafka sallama acikin gidansu Azeeza,wanda suka samu inna Ramatu tana Tsakar gida tana gyaran Shinkafa suka Shigo koda ta amsan sallaman tadago tana kallonsu da mamaki don ganinsu yan gayu dasu,mikewa tayi tana musu maraba bakinta duk abude,taga irin Naira,Sannu da zuwa take jera musu Suko suna binta da gidan gabadaya da kallon banza,Tabarma inna Ramatu tashiga daki ta daukomusu Tana kokarin Shimfidamusu Muneera ta dakatar da ita da Fadin.

“No barshi baiwar Allah ba zama yakawomu ba,don Allah mahaifiyar Azeema muke nema matar captain..”Bata Fuska Inna Ramatu tayi ganin Irin yadda suke kallonta tace”Au ita taturo ku kuzo kumin Rashin arziki? kokuwa kunyi batan kaine,ni ba Uwarta bace,uwarta tadade da mutuwa,ni matar ubantace uwar Azeeza,in wajenta kukazo to ku juya ku Shiga wannan gidan na gaba nan take zaune wajen Uwar mara Asalin..”Tafada tana zaro musu ido,Mirmishin Takaichi Muneera tayi kafin tace”Ai dama Azeeza muke nema munyi batan Sunane..”Tafada tana kallon Ni”ima wacce Tun yanzu Nadama suka dirar mata.

Azeeza dake barci adaki sama sama takejin hayaniyar Inna Ramatu,tsaki taja kafin ta Fito daga ita sai wata doguwar Rigar Atamfa bako kallabi,tana hammah da mika atare ta bude labule tana Fadin”Kai inna waike dawa kike Masifa da Rana tsa….”Bata ida mganarta ba idonta ya sauka kansu Ni”ima da Muneera wadanda ke jifanta da wani kallon banza nazakici ubanki din nan.

  Inna Ramatu tace”Nida wadanan yan Rainin arzikin ne,wai da Farko sunce wajen Azeema sukazo,sai da sukaji na balbalesu kana suka dawo sukace wajenki sukazo,kiji fa rainin Hankali ina kika sansu ma..”Tafada Hankalinta kwance,Azeeza wacce ta Razana da ganinsu Ni’ima ammh sai ta boye Razanarta Ta Fito tana fadin”kyalesu inna Wajena sukazo na sansu yan sch dinmu ne..”Inna Ramatu ta washe baki tace”Oho ai sai kuyi bayani,kuyi hakuri fa,ke Azeeza kishiga dasu ciki mana sannunku da zuwa..”Tafada tana mikewa zata kawo musu Ruwa,yake kawai Azeeza tayi kafin takoma daki tana fadin”Ku Shigo..”Ai bata gama Rufe baki ba Muneera ta bankada dakin da Sauri Ni”ima tabi bayanta suka tsaya cirko cirko suna kallon Azeeza wacce ke tsaye tana jifansu da wani kallon uku saura kwata,suna tsaye sai ga inna Ramatu ta Shigo da Jug da Ruwa hade da kofuna ta ijiye tana fadin!ku zauna ga Ruwa kusha..”yake kawai Muneera tamata tana Fadin”Toh…Inna bata kawo komai Aranta ba,ta Fice zuwa waje.

   Muneera ce ta katse kallon da Azeeza ke binsu dashi tana Fadin”ke baiwar Allah nasan kinsan meke Tafe damu ko,and wht all dis ya akayi kika samu aiki,kuma alhalin Azeema matar captain yaya take gareki,and abubuwa dayawa da bamu gane ba plz u need more explanation fa”Tafada da kakkausan murya,Baya Azeeza taja kafin ta tuntsire da dariya harda dukewa Ni”ima ta kalli Muneera idonta na cikowa da hawaye,itama muneera ita ta kallah,kafin ta maida hankalinta kan Azeeza tace”Lafiyanki kika tasamu kinamana dariya..? tafada tana bin jikinsu da kallo,dariyan Azeeza takara kecewa kan ta tsagaita tana fadin”oh don Allah kiyi hakuri,wlh ba Dariyan komai nake ba,sai dariyan gaku ridaridan yan mata,ga kyau ga iya wanka,ga kudi ga ilimi ammh sam kwakwalwarku bata aiki daidai ko nace ta wawaye ne wlh..”Tafada tana Tafa hannu tana cigaba da dariya,Zaro ido sukayi suna mamakin Furucinta Ganin yadda sukayine yasa Azeeza tacigaba da cewa”Yo eh mana banda Wauta da Saunanci daga ganin mutum yace,kayi Abu kaza,kaikuma dayake gabo ne,sai kayi jiki na rawa,koda yake duk acikin son dakikema captain din ne ko,?don naga Tun kwana hudu da mganarmu Aka sako Azeema tadawo gida duk da ba”a Fallasa Abun ba,inaji nace lalle kinyi kuskuren yarda dani,domin wannan Abun dana sakaki kika aikata na saki ne saboda nakara nesanta yaya captain dake,bayan kin kashe auren Azeema kinga na jefi Tsuntsu Biyu da Dutse daya kenan..”Tafada tana daga musu gira,Muneera da Ni”ima sukayi wani slow suna bin Azeeza da kallo yarda karamar yarinya ta iya Wasa da hankalinsu Ni”ima ce bakinta na Rawa tace”Toh sa..saboda mene…?

  Daure Fuska Azeeza tayi kamar ba ita ke dariya ba tace”Ko baku Tambayaba,dama yakamata kuji koda jin bazai muku amfani ba,Yaya captain nawane nikadai,nafi kowa sonshi harda da uwarsa nafita sonshi,Duk duniya bani da wani buri sai na yau na ganni amtsayin matar Yaya captain,nasoshi Tun banso mai ake kira soba,Na rayu da Sonshi na girma da Sonshi,kullum mafarkina na Aureshi,sai gashi kwatsam Adda Azeema tafim Shigar Sauri,saboda shi na tsani yar”uwanta naji bana  kaunarta balle nakaunar ganinta da Abun kaunata,Tunda akayi Auren naketa Shiryamata gadar zare,ammh yana Tsallakarta da ita,tadalilin haka ya dauketa daga garin nan ya maidata kaduna,ganin haka yasa na Rasa mafita ammh duk da haka ban hakura ba,kwatsam sai Allah ya jehomin ku,,naganku kuna neman agaji,sai naga kema ai kina son Abunda nakeso ne,nikuma bana barin watama ta rabi yaya captain Shiyasa Na ce ki kashe auren Azeema sabida bani da halin zuwa kaduna,ko kulla wani makirci akanta,nayi hakane kema na gama dake,Bayan ki kullah Abunda kika kullah,daga karshe zan kashe Azeema da hannuna,sai na fadama Goggo cewa kice kikayi sanadiyar mutuwar Auren Azeema bayan nan kuma kika aiko har gida aka kasheta,kinga daga Yaya captain yaji lbri zai makaki kotu a yanke miki hukunci kisa,nikuma yazo ya Aureni ya tattarani mu koma kaduna Duniya Ta budemana Sabuwa…”Tafada harda daga Hannu tana tsallen murna kamar Abun ya tabbata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button