ALIYU GADANGA Page 31 to 40

Ni”ima da Muneera sunyi matukar shock dajin wannan lbrin,kasa motsi sukayi,Muneera da Ranta ya baci tadaga hannu azuciye zata wanke Azeeza da mari Ni”ima ta damke mata hannu tana girgixamata kai hawaye na kwanroyomata Kallonta Muneera tayi kafin tace”Meyasa kika hanani? kibarni na Sauyama jaka kamanni,Tunda ta iya sakamu muka aikata Abunda ba Halinmu bane..”Danne kukanta Ni”,ima tayi Tana fadin”Barta barta Sweetheart bakiji metace ba,zata kashe yar”uwarta da suke uba daya saboda Captain,to mu suwaye da bazata iya kullah mana Sharrin dayafi wannan ba,kyaleta kizo mutafi insha Allahu Allah bazai barta ba..”Tafada tana jan hannun Muneera wacce ke hararan Azeeza,itako Tana musu dariya kamar taga mahaukata,inna Na madafa taga hucewarsu Ni”ima da hanzari,tana musu mgana, ma ko kallonta ba wanda yayi,baki ta rike kafin ta cigaba da aikinta aranta tana fadin”Azeeza duk kawayenta irin tane..”itako suna Fita tafada gado tana murna harda tsalle.
Amota haka Ni”ima ke kuka Wurjajan Tana fadin”Mun bani Sweetheart yanzu ya zamuyi da hakkin marainiyar Allah,wlh nayi Nadama,shedan ne ya zugani da kuma soyayyar Soja wlh..”muneera na driving Tana fadin”Ai komai ya Faru keki kaja,banyi Gardama ba,ammh kika nuna amincewarki game da yarinyar,nidama Tunda naga idon yarinyarnan Atsaye Nasan za”a rina Shegiya zuciyarta kamar ta kafaran Farko..”Tafada tana cije baki,dafe kai Ni’ima tayi tana kuka,kafin tayi zaraf ta dauki wayarta dake kan motar tana fadin”Kafin tafadama Captain Abunda Ta shirya nidakaina zan sanar dashi gaskiyan Abunda ya Faru Sweetheart shine mafitanmu yanzu..”Tafada tana danna wayar,Fizge wayar Muneera tayi tana Fadin”Ke kina da Hankali kuwa,yaushema zai Saurareki balle harya gane Abunda kike nufi,kwabe waje kawai zakiyi kibari mukoma gida sai musan Abunyi kinji ko..”Gyada kai Ni”ima tayi tana kara Damke kanta kamar wacce akace Uwarta ta Rasu.
*****************
*1 DIVISION NAGERIA AMRY KADUNA*
An Sauke Baki abbban sashen dayake cikin barikin,sakamakon al’amarin dayafaru da Captain Aliyu,Toh daga lokacin baida Sakin jiki,ko achan Abuja ma,yana baya baya ne,ko achan villa gefe yakoma shiyasa baima Shiga cikin bakin Sojojin ba,kamar yadda wasu sukayi,Shiyasa Jabir shima duk bai saki jiki ba,ganin Abokinsa kuma Amininsa haka,Yayi alqawarin bazai kara Tambayanshi ba,shiyasa yamai Shuru sai dai baya barinshi yazauna Shuru zai zo ya zauna yana jansa da Hira koda bazai Tankanshi ba.
Shiko Yarima Umar Tunda suka sauka Abuja yake video call da gida yana nuna musu Yadda Nageria take da kyau da Tsari,gabadaya iyalan mai maimartaba zakaga an Taru ana mgana da Umar,har Zuwanshi Villa ma haka,kannensa,Safaratu da Zafira sune yan kwakwan Nageria suna makale da yawa bini bini kadan su kira suna fadin”yaya yarima muyi Video call muga a inda kake yanzu,shiko jiki na bari zai kira,har saukansu barikinsu Aliyu ma Da sukaga kyan wajen,harta maimartaba ba”a barshi abaya ba,dashi ake kallo,shiko yana mgana dasu yana Nuna musu Wajewaje,duk da bai yarda yayi nisa ba acikin barikin don baisan ko”ina ba.
*After 1 day*
Bayan kwana daya da isowarsu Yarima Umar,Da yammah da misalin karfe biyar na yammah Aliyu ya shiga gidan Jabir yace yazo ya rakashi cikin gari gidan kawu,zaije su gaisa sun kwana biyu basu hadu ba,baiyi gardama ya Shirya cikin irin Shigar Aliyun na Riga da wando White and blue,na kamfanin Armani,Suka Fito Ras dasu,amotar Jabir aka Fita,shiyasa shike Driving din motar,Har suka isa gidan kawu bala,Basu waji jima ba,don sun samu kawu agida,Tunda Abun yafaru sai Yau yataka kafarsa zuwa gidan,kuma kawu bai mai mgana ba,sai dai yayimai Nasiha tare da jirwaye,akan yadinga binciken Abu kafin ya zartar da Hukunci,zasu Tafi Ummah ta matsa sai sun Tsaya sunyi Dinner,sai da sukaci suka koshi kana suka baro gidan,ta wajejen Anguwar Rimi din nan,sun kawo kenan sai Danja ta tsaidasu sun tsaya,kamar ance ya waiga gefensa yaga wani Namiji bisa mashin yasaka hulan kwano dayake motar Tinted ne,ba”a ganin na ciki,har zai kauda kai,kawai sai yaga ya cire hular kwanon,kara kallonsa yayi yana Tuna Fuskarsa wanda ko Barci yakeyi Tana mai gizo Tsabar yadda ya haddaceta ido yazaro yana Fadin”Shine…”Da hanzari Jabir ya kallesa yana fadin”Shine wa? shima yana bin gayen da kallo,ganin danja ta saki ne,har yamaida hulan kwanan yafara Tafiya cikin hargitsi yace”Plz Jabir Follow dis bike….”Yafada da karfi yana nunamai Shi,da hanzari Jabir ya bi Mashin din wanda yakara gangarawa cikin anguwan Rimi Da gudu,shima da gudun yatakemai baya.
*Comment and Share…*
#Janafty..#
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty????_
*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*Chapter 28*
Aliyu da kanshi ya dauki Azeema da hannunsa ya sakata acikin mota goggo ta Shiga baya,jabir na Driving,su Muneera ma Motarsu, suka Shiga suka Mara musu baya,Mallam lawal Bai bisu ba,yadai bisu da addu”ar Fatan samun lafiya,general Hopital suka kaita,suna zuwa aka karbeta da gaggawa,likitan yana ganin yadda take yafara Sakamata drip tare da wasu Allurai,domin yace ba Suma tayi ba,jikinta ne babu karfi sam,Jininta aka diba First,aka tafi dashi lab,domin gwadawa,itakuma Dama Ruwan daya samata saboda yataimakamata wajen samun karfin jikinta.
Gwajin Farko ya Tabbata da Samun ciki Azeema na Tsawon Sati Takwas koda Resuilt din ya Fito Gadanga aka Damkawa murna kamar bakinshi zai zage,Rumgume jabir yayi yana godiya ga Allah,goggo ko mirmishi take na Farinciki,domin dama Tuni Ta Fahimci ciki ne da Azeemar,itako Azeema batasan wainar Da ake toyaba,tana kwance duk jikinta ba karfi,bata dade ba ta Farka tana Fadin”Goggo Ruwa…” da hanzari Goggo ta bata Ruwa,kafin ta taimakamata tatashi Tana tashi idonta na kan Aliyu wanda yakafeta da ido,yana kallonta lokaci daya da mirmishi bisa Fuskarsa,kauda kai tayi tana amsa Sannun da Ni”ima da Munnera suke mata,amsa musu tayi da kai,tana Kara kallonsu,ita Ni”imar nema ke bata Tsausayi,jabir ne yayimata sannu takarba dakai,Aliyu dayake tsaye chan gefe sai ya matso kusa da ita yana fadin”pretty ya jikin?Kura masa ido tayi tana Tuna sanda yayi Shuri da ita,Runtse ido tayi hawaye na kwararomata,kauda kai tayi tana cije bakinta,ganin haka yasa goggo ta Girgiza kai ta saka kai Ta fice,Jabir ma yabi bayanta Ni”ima ce ta karisa gaban Gadon Azeema tace”Zamu Tafi Azeema,Allah ya baki lafiya..”
“Gyada kai tayi kafin tace”ngd…”Dakyar cikin muryan ciwo,kallon Aliyu tayi kafin tace”Captain zamu Tafi,ina Fata dai An yafemana kuran damuka aikata..”Tafada idonta na cikowa da kwallah,Mirmishi yayi yana kallonta kafin yace”Bakomai Ni”ima buh next time Kada hakan takara Faruwa ko ba akaina ba,ku koyi yaki da zuciyarku don Allah…”
gyada kai tayi kafin ta Share kwallah Tana Fadin”Insha Allahu hakan bazata kara Faruwa ba..”Gyada mata kai yayi yana Fadin”Toh Yayi kyau naji dadin haka,share hawayenki kibar kuka hakanan,komai ya wuce..”Mirmishi tayi batayi mgana ba,sai ta waiga tana kallon Azeema wacce ta Runtse ido ammh kaf Abunda suke Fada akunnanta ne,Dafata tayi tana fadin”Congratulatino Sisto Allah ya inganta..”Daga haka tajuya,muneera dake tsaye itama tayi Fatan samun lafiya kafin su Fice,awaje sukayima su goggo sallama,suka Tafi suna jin zuciyarsu tayi sanyi Tunda komai ya Wuce yanzu.