ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 31 to 40

  Jabir da hanzari yakoma barayinsu yana zuwa kofar Apartment din Aliyu ya ganshi ya Fito sanye da kayan gudu,cogewa yayi agabansa yana kallonsa Abun ya bashi mamaki,toh wannan Aljanine,yanzu fa ya ganshi Aliyu dake tsaye yaga yadda Jabir ke kallonsa Tsaki yaja yana Fadin”Kai fa dan iskane lafiya kawani kuramin ido,bafa wannan kwailar budurwantaka bace”Yafada yana hade rai,Hararansa Jabir yayi kafin yace”Durun uwar kwailar,Ai kwaila bata Wuce Azeema ba..”Dirowa Aliyu daga saman Apartment dinshi ya Naushi Jabir agefen ciki kafin yayi gefe yana fadin”Ai Azeema Ta wuce kwaila Tunda ta iya daukan Nauyi na,har gashi tana Dauke da ciikina,kuma wannan ne last time dazaka kara kiran Sunan matata gatseai ba sakayawa,Tunda ba sa”arka bace..”Jabir dake duke yana rike da gefen cikinshi ya dago yana Fadin”Allah ya isar min mugu kawai,don kaga kai ka fara kokarin ijiye kwanka aduniya Shine ni zakamin mugunta Rasa nawa,ta Allah bata mutum ba..”dariya Aliyu ya saka mai kayatarwa yana Fadin”,Au kudai zauna yanzu nagama yima gayen nan Hisham,nace ya zauna aikin banki ya daskararmai da kwan haihuwa,ko kuwa zama waje daya da Wuni cikin Ac,ya Lusarar dashi,sai bayan anyi Aure aji mata ta gudu taga ba bayani”Dashi da Jabir din suka saka dariya atare harda Tafawa Jabir yace”Kai Dude kasan kan Tsiya fa”Yafada yana Fada kadafadansa kafin yace’Kai Dude Seroious Fa,kana aiki da Aljanune,yanzu fa naganka sanye da kakin Sojin Niger,yanzu kuma na ganka da kakin Sojan Nageria kuma banga sanda kadawo harka chanza kaya ba,wai kodai layan zana gareka..”Kallonsa Aliyu yayi yana Fadin”Tsiyana dakai kwakwalwarka bataja,Ni da yanzu Fitowata kenan,kuma banda Abunka meya hadani da Sojojin Niger da har zan sanya kakinsu,..? Rantsuwa Jabir ya jero yana Fadin”Wlh da gaske,wai bakai bane Harfa kacemin Sunanka Umar Abdulnaseer Tambari buzu fa? Har Aliyu ya juya Yafara Tafiya jin sunan da Jabir ya ambata sai dayaji yanayin jikinsa ya chanza,waigowa yayi yana fadin”Ni kuma? kai mallam kafara Rudu wlh,bani bane kaji na Rantse maka ma,yanzu dai duk ba wannan ba kashiryo kazo muje Atisayen gudu da za”a gudanar yau..”Yana gama Fadin haka yayi gaba da dan gudunsa.

Tsaye Jabir yayi yana mamakin wannan al”amarin Hannunsa bisa baki yana fadin”Bashi bane to waye? yafada yana kada hannu Alamar Abun yabashi mamaki,tsaki yaja kafin yace”Mtsewww shege shine fa,so yake yayi Wasa da Tunanina”Fadin haka yasa ya juya yashiga part dinshi da gudu domin Shiryawa domin Atisayen na yau na musamman ne,domin Duka Shuwagabannin kowani bangare zasu Koyar da Atisayen na yau,duk acikin salon Dabarun yakin daza”a koya musu ne, na Tsawon Sati daya duk da su sun dade da kwarewa game da Aikin,ammh dalinlin bakin Sojojin dakuma Turasun da gwannatin Nageria zatayi zuwa wajejen da yan boko haram suka mamaye.

*JANAFTY*????

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

            

           *Chapter 29*

    “”Har aka gama Atisayen gudun Gadanga da Umar basu hadu ba,sakamakon Filin ya cika da Sojojin Nageria,dana cameron Chadi,da Niger,kuma akallah kowacce tawaga zata kai kimanin Mutane Dari uku,shiyasa ba wanda yahadu da wani acikinsu tunda ba”a Batch daya suke ba,Jabir ko shima yayi Dube Dubenshi baiga ga Wanda yagani dazu ba,sai ya barshi atabbas Aliyun yagani ba wani ba,ko awashegari da”aka Sake maimata atisayen Allah bai hadasu ba,Jabir ya sanya Ranshi kawai Raina masa wayau Aliyu keson yi don yasaba tunda Halinsane,kiri kiri kana Tambayanshi Abu,sai yayi maka banza koda yasani,ko yashiga Raina maka hankali.

*Bayan kwana biyu*

_Gombe_

  Yau Azeema Tafara Jarabawarta ta WAEC sun Fara da Pratical Chemistry,karfe biyu sukaje suka dawo biyar,koda tadawo duk ta gaji,goggo nata yimata sannu,kan kujera ta Jabe tana cije baki,yanzu bata wani karfin jiki tafiya kadan takeyi taji tagaji Tafara haki,taji Sauki sosai karfin jikin ma babu laifi tasamu mganar abinci ma tanaci shima,duk da ba sosai ba,cin goribane sai Abunda yayi gaba kuma don ba raguwa yayi ba.

   Sai dai Abu daya dake damunta Shine Tunda suka dawo asibitin Kewa tare da Son kasancewa da mijinta ke damunta Wani lokacin rasa inda zata saka kanta take,sai dai ta Shige daki tayi ta kuka,tana Jin haushin kanta na yarda ko ada batayi wannan Jarabar ba sai yanzu,kullum dakyar take barci saboda muradi da son kasancewa da Yaya captain ammh Abu yaci Tura,gashi kullum Abun baya raguwa saima gaba gaba yake,haka in Abun ya ciyota zata saci wayar goggo ta Shige Tiolet talalubo Nombar Yaya captain takira,sai Tafara ringing watarana ma harya dauka sai tayi Saurin takashe tana jin haushi datakaicin kanta,yanzu in yadaga sai tacemai miye? Tace yazo tana cikin Tsaninin bukatarsa? haba aiko ba abunda yahadasu bazata iya ba,balle dama Tana Fushi dashi,datayi wannan Tunanin sai tayi Saurin Fitowa tana Share kwallah tayi hanzarin Ijiyema goggo waya a inda ta ijiye,shiko yana ganin kiran goggo,in yana busy ne xai bari daya samu sarara zai kirata,da goggo ta dauka bayan sungaisa sai yace”Goggo naga kiranki,Allah sa bawani laifi nayi ba..”Goggo da mamaki zatace”Kirana kuma? anya bani bace sai dai ko in Azeema ce”,Mamaki ya cikasa kullum aka kirasa da nombar goggo daya kira goggo zatace ba itabace to waye”?Azeema ce? Daya Fahimci haka dayagani, zai yanke sai yayi Saurin kira,ammh har takarishi ringing bata dagawa,wani lokacin in yayi sa”a tadauka,ammh mganar Duniya zai mata taki cewa ko Uffan,yarasa meke damun Azeemar,koda ya tambayi goggo sai cemai tayi lafiyanta kalau babu Abunda ke damunta,bai yarda ba,yadai bar mganar ne,zai yi kokarin zuwa koda a asati na sama ne.

Ko yanzu ma datake cije bakin,Abunda ke damunta kenan,Tun amkranta Abun ya isheta,dakyar ta dawo ita wlh tama Rasa wannan Jaraba,ace wai tana Bukatar Namiji Abun kamar wani Asiri,goggo data Shiga kichen ta daukomata Ruwa tazo ta isketa tana yamutsa Fuska tana wani mele baki,kallonta goggo tayi kafin tace”Wai duk gajiyan ne? kwanciya tayi kan kujeran tana Fadin”,Eh goggo kaina ke ciwo..'”Tayi karya ijiye Ruwan goggo tayi tana Fadin”Ash sannu,bari na kawo miki panadol bayan kinci abinci sai kisha,sai fa ahankali yanzu keda barin laulayin nan sai ciki yayi kwari,Allah ma ya Soki bakya Miyau da Amai..”Tafada tana komwa kichen,tana Ficewa Azeema taji kuka yazomata ta danne da hannunta bataso goggo tajita ganin kukan yana so yayi karfi,sai tatashi da gudu Ta Shige bedroom ta fada Tiolet kafin ta Fito da kukanta,tarasa wazata Fadama damuwarta,kowani ciwo gareta ne,kodai zata Fadama goggo su koma Asibiti ne? don Tana Tunanin bata da lafiya,ta dade tana kuka kafin ta Tube kaya tayo wanka Ta fito,sai da tafara gabatar da sallar la’asar kafin taci abincin da goggo ta kawo mata Danbun Shinkafa da zogale,yayimata dadi dayake ta bankada yaji,har sai da goggo ta dauke Roban yajin tana Sababi,batasha mganin ba sai da sukayi issha”i kana tasha ta kwanta ammh bawai don tana jin barci ba,cikinta ne juyawa,babu Abunda take bukatar sai lafiyar yaya captain,don Hakurinta yakusa karewa tarasa meya sameta ne,kodai wata Allura akayimata asibitin? gaskiya tanajin da wata kasa????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button