ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 31 to 40

 Umar dake tsaye,yaji Shima hawaye sun kawomai,ya kamkame Aliyu shima hawayensa na diga bisa bayansa yake fadin”Hakika zuwana Nageria yana da Babban Sanadi,da kuma sila,ammh babban dalilin Shine,domin na warwarema Abbah mafarkinshi na Shekara da Shekaru,hakika Kana da nasaba da damuwar da maimartaba ke Shiga na mafarkin wata mata da Da’n ta suna halin Neman Taimakonsa da bukatarsu,kaine Wannan Fassarar mafarkin kai ne wlh..”Yake fada yana kuka Shabe shabe,Aliyu yana jin Abunda Umar yace sai wasu hawaye suka kara gudunmai bisa kuncinsa yana Dariya da kuka ya dago yana Fadin”Kai dan”uwa ne yanzu? Ashe zanga wannan Ranar? yafada yana kara kamkame Umar din Shima kam ya rikesa yana Fadin”Ba Dan’uwa kadai gareka ba,kana da kanne da iyayye bayan mahaifa da wasu Ahali masu yawa” Kukan Farinciki Aliyu keyi kamar wanda akace zai Shiga aljannah.

  Jabir dake gefe shima Sharen kwallah yake yana dariya,kawai baisan sadda ya saka hannu yana basu Tafi ba Raf raf,Aliyu ya dago yana kallon Jabir,yadda yaga yana hawaye ga Dariya yana yi lokaci daya Hannun ya mika masa yana Fadin”Taho Dude taho,Katayani murna nima yau naji lbrin Ashe nima da,ne kamar kowa ina da uba..”Yafada yana dariya da hanzari Jabir ya isa garesu Aliyu ya hadasu ya Rumgume yana Ta hawayen Farinciko,kafin ya sakeshi ya Riko hannu Umar yana Fadin”Taho muje cikin gida mganganun bana Tsayawa bane..”Yafada duka hakoransa na waje,Rikesa Umar yayi yana Fadin”Toh *YAYA..*….”Wani Farinciki ya lulllube Aliyu wanda baisan sadda ya jawo kafadan Umar ba yana mai mirmishi mai kayatarwa,Jabir dake biye dasu shima yana mirmishi Farinciki ya cikashi yana mamakin Baita ganin kukan Aliyu ba,koda kowa mai zai Faru dashi,ammh yau kam yaga kukan Farincikinsa.

   __________________

 *Kwana Daya daya wuce*

  *Agadez masarautar Tambari buzu*

  Da Sulasainin Dare ni,wajen karfe uku da Rabin agogon Niger,Maimartaba ne ke kwance bisa kayatattacen gadonsa yana barci,gefensa kuma gimbiya Fasilatu ce,don ita keda Turaka Aranar.

 Kamar mafarki taje muryan Maimartaba yana kiran wani Suna,bata maida kai ba,sai tajuya zata koma barci,ammh sai taji mganar maimartaba tafara Fita yana kiran Wani Suna wanda bata gane ba,kuma da alama Sunan mace ne,da hanzari ta mike tana jijjiga Sarki take Fadin”Ranka ya dade..!Ranka ya dade..”!ammh Shuru sai Rike kansa yake yana motsi da bakinsa wani Suna yake kira,ammh bata Fahimtar meyake fadi,ai da hanzari ta diro daga kan gadon,ko alkyabba bata tsaya sakawa taja katon Mayafinta ta Rufa ta fice da gudu,tana zuwa Kofar Shashen maimartaba Fadawa suka taso Hankalinsu tashe ko Sauraransu Gimbiya Fasilatu batayi ba takama gudu sai Shashen Ummah mai babban daki,masu tsaron kofarta suna ganin gimbiya na gudu suka dare,suka bata kofa ta Shiga,Ummah mai babban daki na zaune kan sallayatar ta idar da sallah kenan tana Addu”a Gimbiya Fasilatu tashigo tana haki take Fadin”Ummah kizo maimartaba wani Abu yafaru dashi…”Da hanzari Ummah ta mike tana fadin”Innalillahi wa’inna Alaihirraju’un..Meyafaru dashi? tafada tana Jan alkaybbanta ta sanya tayi gaba tana kiran Sunan Allah,kuyangu duk suka Firfito da Fadawa suna raba ido,basa fatan ace wani Abu ne ya samu maimartaba da gudu gudu sauri Sauri suka karisa shashen nashi yadda ta barshi haka sukazo suka sameshi sai da wannan karon da karfi yake kiran Sunanta” *SUWAIBA…* “Ummah da Gimbiya fasilatu suka kalli Juna kafin su maimata Sunan atare”Suwaiba kuma…? Hawa gadon Ummah tayi tana Rikoshi addu”a take tofamai tana Shafamai bisa kai,cikin ikon Allah ya zabura ya Farka yana kuka yake fadin”Wlh na Tunata,na Tuna *MATATA SUWAIBA…* Yafada yana rike hannun Ummah.

 Dukkansu sandarewa sukayi saboda namaki Ummah tabishi da kallo kanshi na bisa cinyarta,atare Ummah da gimbiya Fasilatu sukace”Matarka kuma…? gyada kai Maimartaba yayi yana Fadin”Eh na Tunata,yau Allah ya nunamin Fuskarta Suwaiba ce,lokacin dana bar gida ummah,dasu na zauna har mahaifinta ya Auramin ita,daganan ne kuma Ummah Tunani na ya Shafe na Rasa awani yanki ne ?wani gari ne,?na kasa Tunawa ummh ammah yau tabbas na Tunata Suwaiba ce wlh…”Yake Fada yana dafe kansa.

 Ummah da Gimbiya Fasilatu suka kalli Juna kafin su bisa da kallo,Girgiza kai Ummah tayi kafin tace”,kira Likitanshi yazo ya Dubashi yanzu…’Jin haka yasa ta Fice da Sauri ammh kalaman mai martaba Sun bata mamaki,kamar yadda suka saka Ummah cikin Rudu.

     *Janafty….*

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

_* Oh ni Jikar Fati????Gabadaya yau ba”a barni nayi barcin Safe ba,gabadaya Anki barina nayi Sukuni ko”ina naje GADANGA..GADANGA…Toh gashinan Dai kada asamu masu cinyeni danya ban gasu ba???? Nasan in ban sakoshiba,Akwai masu zuwa har zaria sucini Tara,irinsu TEAM AZEEMAR GADANGA????Happy Lahadi day????????Asha karatu lafiya Masoyan kwarai*_????????

   *Chapter 30..*

    “”Gimbiya Fasilatu ta kira likitan mai martaba Tasanar dashi ko mintigoma  baiyi ba, ya iso masauratar,kai tsaye akayi mishi iso shashen maimartaba,koda ya isa ya iske maimartaba nata sambatu yana kiran Sunan Suwaiba,bai bata lokaci ba ya nemi da su Ummah su bashi wajen don yasamu damar gudanar da aikinshi,suna Fita ya karisa gamai maimartaba wanda ke zaune yayi Tagumi yana Ta so kwalkwalwarsa Ta tunamai Sauran Abubuwa ammh Abu yaci Tura,Likitan baiyi mgana ba,illah bude akwatin kayan aikinsa ya Fito da allurai ya harda harda ya juye a Siriji yayi mai martaba ita,wanda ko minti biyar bai karaba ya sulale yana barci,koda likitan ya Fito baice masu Ummah komai ba,illah sanar dasu dayayi”Da zaran ya Farka zai Dawo daidai Ranki Shi dade..”Sallama sukayi yatafi wanda dama Likitan Shima zuru”ar Mairtaba tsohon sarki ne,da yake ga Sarki Abdulnasser din.

Har garin Allah yawaye maimartaba Bai Farka ba,yana ta barcinsa Hankalinsa kwance,Tuni lbrin ya ishi kunnen sauran iyalansa da kuma Shamaki tare da waziri da galadima,su suka sanar da Fada cewa sarki bazai samu zama ba yau sakamakon baitashi da jin dadin jikinsa,Fatan samun sauki akayimai sai Waziri ya Karbi sarki Aranar aka cigaba da gudanar da Mulkin.

   *********************

Suna Shiga cikin gidan Aliyu,suka zazzauna,Aliyu bakinsa yaki Rufuwa saboda murna wayarsa yazaro yana Fadin”Dude ni nama Rasa wazan Fara kira goggo ko kawu? yafada yana Danna wayar dariya Jabir yayi kafin yace”kira kawu first shine ke kusa goggo kuma,in son samu ne ayimata Big Suprise kawai…”Dariya sukayi gabadaya.

Umar yace”Nikuma sai komai ya kammallah zan kira video call na hadaka da maimartaba nagani ko yaya zaiyi..? Shuru Aliyu yayi yana mirmishi daidai lokacin da Kawu ya daga kiransa yana Fadin”Aliyu Gadanga ya”akayi ne? Bakinsa duka abude yace”Kawu yau Allah ya gwadamin dan”uwa na,kawu yau naji lbrin dangina,Ashe nima Da”ne kamar kowa ina da uba da yan”uwa da kanne da yayye..”Yafada idonsa na cikowa Da kwallah.

Kawu Bala dake zaune a office yayi Saurin mikewa yana Fadin”Aliyu are u Serious….? Da hanzari yace”Wlh kuwa kawu kazo barrak dinmu yanzu kaga wani Abun mamaki..”Kawu bai jira cewarsa ba ya datse kiran,alokacin yana da tattaunawa da yan jaridu,ammh ya tsallake Shida tawaganshi Suka Shisshiga mota sai bariki,tun amota yake addu”a Allah yasa Abunda Aliyu yafadamai da gaskene.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button