ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 31 to 40

…”ya fada hawaye suna zubomai Kawu ma kukan yake yana Fadin”Abdulnaseer dama kana raye ina ka Shigeni Muda mallam mun nemeka har mun gaji..”Maimartaba yace,”lbri ne mai Tsawo bala,mubar wannan sai nazo zakuji komai ammh yanzu ina Suwaiba don Allah karkacemin Suwaiba ta rasu.? yafada cikin Rawan murya Mirmishi kawu yayi yana Fadin”Suwaiba bata mutu ba,tana nan da Ranta ammh yanzu bata kusa tana gombe tana zaune…” Maimartaba ya maimata”gombe…? gyada kai Kawu yayi yana Fadin”lbrin yana Tsawo bazai yuyu ta waya ba..”Maimartaba yace”Hakane,ammh don Allah bala ka Fadamin gaskiya da gaskene,bayan Tafiyata Suwaiba ta haihu,a mafarkina ina ganinta da da,kuma hakan yanunamin ina da nasaba da Abunda Allah ke nunamin…”Kawu baiyi mgana ba,illah jawo hannun Aliyu dayayi wanda ke gefe yana Tsiyayan hawayen Farincikin jin muryan wani dattijo da sunan mahaifinsa,yana jawosa ya tsayar dashi kusa da Umar,Maimartaba da Sauran su Ummah suka daskare atsaye ganin wani mai kama da Umar sak,da badon Umar din na tsaye awajen ba tabbas zasu karyata suje umar ne,Aliyu ya dago kanshi yana kallon Fuskar Mahaifinsa wanda Manyatane kadai ta bambata danashi,ammh hatta tsawon da gashin kansa duka dayane,harda hancinsa da Shape din Fuskarsa,Sai fuskar kakarsa wacce ta haifi maimartaba itama kamar tashi Fuskar,sai Fuskar kannenshi mata wadanda yadda kikasn dukkansu sun Fita daga mahaifa daya,Kallonsu yake wani hajijiya na yawo dashi Don gani yake kamar ba gaske ba,Zafira da Safaratu da mamaki ya kamasu suka daka tsalle suna nuna Aliyu suna Fadin”La Abbah kalli mai kama damu ku kalli mai kama da Yaya yarima…? Maimartaba da gaban Rigansa ya jike da kwallah ya daga hannu ya shafa Fuskar Aliyu ta jikin wayar yana Fadib” yanzu Suwaiba ita ta haifamin kai da gaske…? yafada yana sakin yar dariya Aliyu ya gyada kai shima yana mika hannu kamar zai tabo mahaifinsa nasa yace”Ab…Abb…Abbbah….!!!Yafada muryansa na hadewa Jabir dake gefe yana leke shima yana kwallar,Aliyu saboda murna baisan sadda ya fada jikinsa kawu ba yana kuka kamar karamin yaro,don saboda yadda Farinciki yayimai yawa ji yake kamar zai iya kashe rai saboda yadda yakejin kansa,Umar dake hawaye ya karbi wayar yana Fadin”Abbah Ashe nima ina da Dan”uwa Shima Soja ne Shugaba nane,Sunansa * CAPTAIN ALIYU ABDULNASEER TAMBARI BUZU*..” Ihu su Zafira suka saka murna sun samu wani dan”,uwa Ummah kuwa mai babban daki,amsan wayar tayi tana Fadin”Allah Shine mai hikima Umar Ashe dalilin zuwanka Garin kenan,tabomin sabon megidana nakara ganinshi don yanzu bana yayinka..”Tafada tana dariya Aliyu dayaji haka ya dago yana kallonta yadda take dariya yasa ya karbi wayar yana Fadin”Nima bani so akai kasuwa..”,Dariya su zafira su saka sanya,maimarbata na tsaye Shima yana dariyan.

    Gimbiya Fasilatu,kuwa daskarewa tayi lalle Tsugunne bata kare ba tana Tunanin cewa itace Tauraruwa awajen sarki itace ta haifan mai magaji,ashe akwai wani boyayyen Sirri da basu sani ba,ashe akwai wata mace wacce take da babban mtsayi azuciyar Maimartaba,uwa uba ga kuma bayyanar wani da’n gareshi wanda ya D’arama Umar akomai,Turkashi,Itako Gimbiya Razeenah murna tacika cikinta ko bazan yanzu bakin gimbiya Fasilatu b zai mutu,kullum cikin Fariya take itace uwar magajin Sarki wato Yarima Umar,Saboda takaramata haushi itama Shigewa tayi cikinsu Ummah suna ta hira da Umar da Aliyu harda Jabir wanda Aliyu ya nunama maimartaba amtsayin Amini garesa,Nan fa akaita hira ana dariya su Zafira murna kamar ta kashesu sun samu sabon yaya,Duk rashin mganar Aliyu sai gashi ya zage yana Surutu da kannensa kamar bashi ba.

  Jabir ne aka kira akace su Fito Atisayen harbi,Dalilin daya sanya Aliyu cewa”Ok kiddo’s matas,mommy,kubari mudawo yau kwana zamuyi muna mgana,yanzu zamu tafi wajen atisayen harbi ne,”Maimartaba ya karbi wayar yana Fadin”Kubama Bala wayar,Tundazu kun hanamu mgana..”dariya sukayi kan su mikama kawu bala wayar nan Maimartaba ke Shaidamai cewa!Gobe in Allah ya yarda dashi da duka iyalansa zasu sauka a gombe,..” baki Kawu ya washe yana Fadin”Masha Allahu..”Maimartaba yace”ina neman alfarman kada ku sanar da Suwaiba komai,kawai sai dai taganni” gyada kai Kawu yayi yana Fadin”Hakan ma yayi nima gobe zamu hadu a gombe duka nida iyalaina..”jinjina kai maimartaba yayi yana fadin”Alhamdulillah Allah Abun godiya…”,Kafin suyi sallama su yanke kiran Babu bukatar wani bayani su Aliyun sunji komai basu bata lokaci ba sukayi sallama da kawu Suka Fito,suka wuce wajen atisayen harbi,shikuma ya juya zuwa gida Shida tawagansu Don lbrin dake cikinsa bazai iya komawa office ba.

 Shiko maimartaba suna yanke wayar ya Rumgume Ummah yana murna su Zafirama suka Rumgumeshi sunamai murna hakama gimbiya Razeenah ke nuna murnanta afili,Gimbiya Fasilatu dai na gefe tana yaken dole ranta duk ba dadi,itako Gimbiya Razeenah tana kallonta Farinciki yacika ranta,Maimartaba ya dago yana Fadin”Akiramin sarkin gida,…”Yafada da dan karfi,nan da nan fadawan dake waje suka isar da sakon sarki kan kace kwabo sai ga sarkin gida ya iso,Falon Shashen maimartaba ya tsaya inda maimartaba ya Fito ya sameshi da kafarsa Jikinsa da kuzari yana mai nuna murnansa Sarkin gida ya mike yana fadin”,Allah Taimaki sarkin Agadez mai mulkan Masarautarmu Ta tambari buzu Allah dai yakarama Sarki lafiya,Gani kiran Adalin sarki ba”a yimishi jinkiri…”,Dariya maimartaba yayi yana zama kafin yace”Sarkin gida katashi yanzu katafi kakira waya zuwa Nageria,inaso in sanar dakai kakira Waya zuwa Masarautar garin gombe ka sanar cewa zan zo kasarsa dakuma jaharsa agobe,Ammh kabari sai waziri yazo munyi mgana dashi ashiryamana jirgin masaurata in yagamaka lokacin dazamu isa sai kakira wayar..”,Jinjina kai Sarki gida yayi yana Fadin”Allah karamaka yawan Rai,angama…”,Yatashi da hanzari zai Fice sarki yace”Ka fadama Waziri yazo yanzu inason ganinshi…” Sadda kai Sarkin gida yayi yana fadin “Yanzu kuwa Adalin sarki..” yafada yana Hucewa.

   

*JANAFTY*

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

*I DASH D WHOLE PAGE 4 U INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION..????Son So Fisabillahi*????????????

      *Chapter 31*

     “”Koda Sarkin gida ya isa Fada ya sanar da waziri sakon maimartaba da hanzari ya mike ya isa zuwa ga Sarki,inda maimartaba yake Shaida masa ashiryamsa jirgin masaurata shida duka iyalansa Tafiyan ta mussaman ne,shiyasa zai Tafi da Sarkin gida,Da shamaki,shi waziri zai zauna ya maye gurbin sarki saboda adokar Gidan Sarauta ba”a barin Fada babu wani Shugaba,Sarki baiyi wani Nauyi baki yafara warwarema waziri kadan daga cikin lbrin Abunda zai kaishi Nageria,Mamaki yakama Waziri Kiran Sunan Allah kawai yake yana Fadin”Ammh Allah yasakama ka Ranka yadade,domin sun cutar dakai babu Shakka Sihirin dasukayimaka babba ne mai daukan Lokaci mai Tswao bai saki mutum ba..”.

  

Mirmishi maimartaba yayi kafin yace!”Koma miye sun ma kansu waziri,yanzu bagashi Allah ya warware komai,ka hanzarta so nakeyi ayi komai da hanzari,gobe Tun safe mu kama hanya..”Gyada kai Waziri yayi kafin ya mike yana Fadin”Angama Ranka ya dade..”Ya fice yana gyara zaman Rawanin kanshi,daganan Maimartaba cikin gida yakoma,Ummah yafara gayama cewa Ta Shirya gobe zasu Tafi Nageria,koda yagama Matan nasa Gimbiya Razeenah ce kadai Da ya’yanta suka Nuna murnansu Afili itako Gimbiya Fasilatu Ranta baiso ba bata da yadda zatayi kawai tayi Shuru ammh datana da iko datace bazata ba,Gimbiya Razeenah ita ta umarci Jakadiya data sanya bayin barayin Ummah mai babban daki dasu Shiryamata kayanta,sai takoma shashen ya”yan nata ta umarcin Shugaban bayin nasu data Zabi wadanda zasu Shirya musu kayansu dakuma bayi guda uku dazasu Tafi dasu,jiki na rawa shugabam bayi Uwani ta shiga Shashen bayi tana bawa kowa umarnin kowa yatafi barayin da zata turashi yin aiki,ita dai gimbiya Fasilatu sai da taga Fada ta rude da Shirye Shiryen Tafiyar maimartaba Nageria agobe ne yasa Ta Umarcin bayinta da suhada mata kayanta,kuma ta zabi bayi har biyu wadanda zata Tafi dasu,kaji hadama????Tun adaren Sarkin gida yayi waya zuwa Fadar Shugaban kasan Nageria ya da sakon maimartaba,kana yayi waya zuwa Fadar maimartaba Sarkin gombe ya Shaidamusu zuwan maimartaba agoben,Jirgin Masaurata aka Shirya za”a tafi dashi,domin ababbar Masarautar ta Tambari buzu akwai jirage kama da Aeroplane da Helicopter,Kowane An Rubutamai *TAMBARI BUZU PALACE* Toh daga daya daga ciki aka Shirya tafiyan Kuma duka matuka Jiragen suna da kwalinsu na kammallah babbar mkranta amtsayin pilot,wato dai Sun karancin Abun kenan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button