BABU SO HAUSA NOVEL

ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Niko nace oho

✍????by Leemat

Love u all????????????
????????‍⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????‍⚖
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Wannan page din nakune sisters yan MUNEERA HAUSA NOVELS group ina mai jinjina maku banida kamarku Allah barmu tare Ameen ❤????????????????????

UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????

                    19

Ashraf yace wai me nayi ne yau?
Ban tambayi yaronnan sunarshi ba gashi ya shige anyway ba matsala idan Adama tafito sai ta fadamin sunanshi ai

Yana jingine da motarshi Adama tafito ganin Ashraf ne ba karamin bata mamaki yayi ba ta kasa boye farin cikinta tace Ashraf?

Ashraf yace yes shine Adama karaso mana ta matso bayan sun gaisa ne take tambayarshi yanda akayi yasan gidansu smile yayi yashare zancen kamar baiji ba kana yace da ita number gimbiya nakeso kibani zan samu?

Smile tayi kafin tace tabbas zaka samu amma me zakayi da number?

Ashraf yace pls kibani nan ya kwashe komai yanda sukayi da Aneesa ya fada mata dariya tayi mai isarta kana ta furta inama ace ku tabbata a haka har tsawon rayuwarku da nafi kowa jjin dadi domin kuwa ba karamin matching da juna kukayiba wallahi kun dace da juna

Jin haka yasa Ashraf yace adama zan iya yarda dake?

Adama tace y not? Zaka iya mana Ashraf yace inaso in sanar dake wani abu mai muhimmanci kuma inaso yazama sirri tsakanina dake don Allah karki fadawa kowa Adama tace toh shikenan bakomai inshaa Allahu bazaka jishi a bakin kowa ba har sai in kaine kafadawa wani

Smile yayi kafin ya fara zazzage mata abinda ke cikin zuciyarshi yana gama wa sai Adama tace habaaa……

Ai daman biri yayi kama da mutum ai ni na dagoka tun jiyannan so bkm Allah taimaka saidai samun kan kawata zai maka wuya tunda kaga batada lokacin love smile yayi kana yace ai kibarni da ita kawai nan adama tace ammanfa karikemin ita amana banda……Ashraf yace habaa adama ai ba haka nakeba kinga nima ban tabajin ina kaunar diya mace a rayuwata ba kamar Aneesa ba

Dan haka karki damu inshaa Allahu babu abinda zai sameta sai farinciki toh shikenan Allah taimaka Ameen ya amsa

Sannan yace toh yanzu ki taimakamin da numberta in ba haka ba zan iya rasa ta kuma idan na rasa Aneesa zan mutu tausayi yaba Adama yanda yake maganar kamar zaiyi kuka

Adama tace zan baka karka damu nan tabashi number farin ciki agun Ashraf baya misaltuwa ai baisan lokacinda ya bude mota ya ciro makudan kudade wanda shi kansa baisan ko nawa bane ya mikama Adama ita kuwa tace tagode taki karba yi yayi kamar zai mata kuka hakan yasa ba yadda ta iya ta karba nan yake tambayarta sunan kaninta smile tayi kana tace sharifulla woowww nice name nan yasa hannu a aljihunsa yaciro bandir din 100naira yamika mata yana fadin kibawa abokina shariff adama tace aa kabarshi zan bashi acikin wannan Ashraf yayi juyin duniyarnan amma sam Adama taki karban na shariff ok bkm nasan abinda zanyi cewar ashraf

Nan sukayi sallama da juna har zata shiga gida sai ashraf yace laaaa baki bani numberki ba babbar kawa

Smile adama tayi tace ok gashi nan tabashi yana murna yawuce koda ya isa gida part dinshi yashige yayi wanka sannan yaje part din iyayenshi

ummanshi tayi mamakin yanda yashigo mata yau cikeda farinciki sai smile yaketa faman yi yana duba agogo kasa hkr tayi tace son yadai?

Lfy kk ta duba agogo ko wani secon?
Smile yayi baice da ita uffan ba cen minti 5 haka sai yace umma inajin yunwa fa cikin jin dadi yau danta tilo yace yanajin yunwa wanda bai damu da abinci ba umma tace son muje gasucen jere akan dinning sai wanda ka zaba

Ai kuwa yayi kan dinning ya zauna umma duk tabi ta rude sai faman tambayarshi taketayi wanne zata zuba mar
Ya nuna mata wani hadadden fried rice wanda yaji kayan hadi bayan ta zaba mashi ne yace umma costlow nan ta zubamai cin abincin yayi hankali kwance har ya cinye umma ce tace Allah nagode maka yau dana ne yacinye abincina nan hawaye yafara zubo mata ganin haka yasa Ashraf smile kana yace habba umma yanzu dan na cinye abincinki ne kk hawaye toh inshaa Allahu bszan kara ci ba nan da nan ta share hawayenta tana fadin haba son ai hawayen farin ciki ne wannan tunda na haifeka baka tabacin abunci……

Ashraf yace ummata takaina zan baki mamakine amma ba yanzu ba kici gaba dayimini addu’a Allah bani sa’a akan abinda nake nema nikuma nayi maki alkawarin cigaba da cinye abincinda kika dafamin

Allah bada sa’a son kullum addu’ata kenan Allah taimakeka yabaka mace ta gari jin haddu’arnan daga bakin ummanshi yasashi yin smile dan harga Allah yaji dadin addu’ar Ameen ya amsa

Aneesa ko tunda tashiga cikin gida bayan ta kammala abinda takeyi sai taje ta kwanta ai kuwa sai hoton Ashraf kawai taketa gani tajuya nan ta juya cen ganin ba sarki sai Allah ne yasata fito waje a varandarta ta zauna sai faman tuna yanda sukayi da ashraf taketa yi smile tayitayi data tuna yanda yaketa mata yau

Mama ce ta iso wurin ta zauna tana fadin yar mama yau kin gaji koh

Jin shirun aneesa ne ya bata tsoro taba aneesar tayi nan tadan razana kafin tace mama yaushe kk zo nan mama tace yar mama meke damunki ne

Aneesa tace bkm mama ta lura da yanda taketa smile itama smile din tayi nan tafiddo da dambun shinkafar da tayi dazu aneesa na ganin dambun shinkafa ta fara smile tana fadin mamata2

Tashiwa tayi taje ta dsuko ruwa tafara cin dambun mama kuwa shigewa tayi don gyara mata ciki koda mama tashiga sai taga ko ina a kimtse

Karfe 7:30pm Ashraf na hango yafito daga bathroom nan yayita kwalliya kamar mace karfe 8pm yafito yashiga motarshi kirar infiniti sai gidansu aneesa a kofar gate din ya faka nan ya fiddo da wayarshi ya kira aneesa

Aneesa da take zaune itada mama da baba sunata hira ita tama manta da wani wai ashraf jin wayarta na kara ne ya katse masu hirarsu tana dubawa sai taga bakuwar number taki dagawa rejectin tayi ganin anyi rejectin ya dagama Ashraf hankali kara kira yayi akaro na biyu nan ma taki dagawa mama ce tace kiba baba ya daga tunda bakuwar number ce haka kuwa akayi tamikama baba ya sa a kunnensa baice kala ba a cen dayan bangaren akace Amuncin Allah ya tabbata agareki ma abociya kyau da nutsuwa gimbiyata ina… . Jin haka yasa baba yamika mata yana fadin kiji abinda ake fada ai kuwa aneesa tasashi a handsfree nan Ashraf yace gimbiyata kinajina kuwa gani a kofar gidanku ina jiranki

Datse kirar aneesa tayi batareda tace uffan ba kirjinta ne ya hau dukan 9 tara

Mama tafara cewa Allah abin godiya
Baba yace shine wannan dayazo da rana?

Aneesa tace eh kanta a kasa toh tashi kije mana kice yashigo kallon kayanda ke jikinta ne tayi mama tace haba ai kayan baida matsala je kishigomin da suruki na Aneesa tace mama bafa surukinki bane wannan a….

Mama tana dariya tace toh naji maza jeki cemai yashigo ba yanda ta iya haka ta mike cikeda kunya jiki ba kwari tafito ai kuwa mutuwar zaune Ashraf yayi ganin yanda kayan jikinta suka mata kyau dukda ba kwalliya a fuskarta amma ba laifi tayi kyau

Fitowa yayi dan yasan batasan shike cikin motar ba gimbiya jin sunar yasa tagane shine ai kuwa kafin tayi magana sai ji sukayi…………..

✍????By Leemat

Love u all????????????
????????‍⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????‍⚖
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button