BABU SO HAUSA NOVEL

ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Ji tayi kamar ta hadiye zuciya ta mutu nan taci alwashin raba Aneesar da koma waye ne

Ashraf yamike shima yace saida safe Abdul basit yace kudaiji tsoron Allah sannan ka kulammin da lil sis dita banda tabata smile yayi yace ok big bro promise

Yana isa kofar dakinta yasa hannu ya murda ta da sallamarshi yabude yashiga nan yasameta tana shirin kwantawa ai baisan sanda yaje ya rungumota ba

Tana kokarin kwatan jikinta bata ankara ba sai jin bakinshi tayi cikin nata duk yanda taso kwatan kanta kasawa tayi shafata yakeyi ta ko ina…………………

✍????by Leemat

Love u all❤❤❤
????????????????‍⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????‍⚖????????
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Wannan page din nakine sweet 6 HAUWA SARKI Allah barmu tare inayinki irin so much dinnan ????????????

UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????

                   28

Ganin abin yafi karfinta ne yasa tasaki kuka mai tsumarda zuciyar mai sauraro jin kukanta ne yasa yasaketa sai faman maida numfashi yaketayi idonshi duk sun canza kala shima hawayen ya soma zubdawa domin kuwa sam ya mance Aneesa ba muharramarshi bace

Abin yakoma bashi haushi tsugunawa yayi a wurin yana bata hakuri itako sai faman kukanta taketayi tana fadin ka cuceni ashe kai dan iska ne hmmm…… niko nace Aneesa ashe daman iska yanada da?????

Ashraf zaiyi magana ta dagamai hannu tana fadin tashi kafitammin daga daki kuma inaso gobe gobennan ka shirya kabar gidannan inba haka ba ranka sai ya bace

Ashraf yamike jiki ba kwari yafito yawuce dakinda aka bashi koda yashiga zama yayi yanata hawaye sannan yana neman gafara agun ubanji

Ganin hawayen bazasu fisheshi bane yasashi mikewa yafada bayi yayi wanka sannan ya tsarkake jikinshi ya dauro alwala yafito

Sallaya yahau yayita nafil fili yana rokon Allah yafemai yana nadamar abinda ya aikata yau

Domin kuwa tunda yake a rayuwarshi bai taba yin irin haka ba shidai kabarshi dashan giyarshi amma baruwanshi da mata

Idan yatuno cewar yabar Aneesar shi tanata kuka tana danasanin haduwarta dashi sai ya rumtse ido zuciyarshi na mashi zafi saboda ji yake kamar ya kashe kanshi

Shida baison bacin ranta amma wai shine yasata zubda hawaye mikewa yayi yafito palo baiga kowaba hakan yasashi ficewa daga gidan ko ina yayi oho

Itako Aneesa taci kukanta ma ishi musamman idan ta tuno da yanda yaketa taba mata na shanunta shikenan ya gama dani Allah zai sakamin mugu kawai azzalumi tayita sunbatu ita kadai tana hawaye cendai dataga bashine mafita ba mikewa tayi tafada bathroom

Saidai ga mamakinta sai gani tayi ashe sharkaf take ido ta waro waje kana tace toh wai me haka ne …….. niko danake jinta a bakin kofa nace kema dai sha’awa tamiki yawa sannan ga tarin ni’ima ????

Bayan tagama tafito tareda dauro alwala tazo tayita nafil fili tana neman sassauci dan zuciyarta zafi yake mata wai ace masoyinta ne zai nema yin raping dinta toh Allah yafishi tana kan haka ne har barci barawo yayi awon gaba da ita saman sallayar

Koda asubahi tayi bayan ta mike bayi tafada tayi wanka sannan ta dauro alwala tazo tagabatarda sallah

Koda ta idar bayan tayi karatun Al- Qurani mai girma tayi addu’a sannan tamike ta haye saman gado takoma barci dan wani ciwon kai kedamunta sosai

Shiko Ashraf club yanufa koda ya zauna giya yayita sha kamar ba gobe mutuminda tunda suka hadu da Aneesa yabar shan giya amma sai gashi yau yana sha

Abokinshi yakira yake tambayarshi inda yake shiko cemashi yayi ina club nan sukayita hirarsu ta mashaya

Wanda hakan ba karamin bama abokin nasa mamaki yayi ba

Tambayarshi yayi ya cemashi me yasaka shan giya kuma kodai Aneesa ta gujeka ne jin yanda kirjinshi tabata dammmm……. ne yasa ya katse wayar yana fadin shege yana neman yakarasar dani toh ina ruwanshi ma da Aneesa ta

Koda yamike cikin maye haka ya fito yashiga taxi sai gidansu Abdul basit yana saukowa yabiya sannan yashige ciki

Yana fadawa cikin dakinda aka bashi yasa makulli ya rufe sannan yafada kan gado sai barci bashi ne ya farka ba sai 11am na safe

Domin kuwa koda Abdul basit yazo tadashi domin su gabatar da sallar subhi cemashi yayi yariga ya kammala ko kuma yaki bude kofar hakan yasa Abdul basit komawa ya sauke nashi faralin yanajin Abdul basit na fadin zuwa 7am zan wuce skul fa amma bai tankashi ba

Koda 7am din yayi ficewa yayi abinshi domin kuwa ya kasa gane meke faruwa da masoyannan biyu domin kuwa dayashiga dakin Aneesa da safe samunta yayi tanata barci sannan kuma tana ajiyar zuciya koda yamata kiss a goshinta ta razana mikewa tayi jikinta na kyarma amma ganin yayanta ne yasa ta yin kokarin karfin hali wanda abin yabama yayan nata mamaki sannan kuma ya tsorata tambayrta yayi sai tace mashi ai mafarki tayi mara kyau

Cewa yayi shine kika tashi ko addu a babu koh? Komawa tayi ta kwanta

Nan yamata addu’a ya tofa mata yana shafa kanta yace shi zai wuce makaranta ganin idonta a kumbure ne ya dagamai hankali tambayar duniyar nan yamata amma tace itama batasan meya sameta a ido ba babu yanda ya iya dole ya yarda da kanwarshi sannan ya umurceta datayitayin addu a toh tace dashi gyara mata blanket yayi ajikinta sannan ya manna mata kiss yafita yana fadin idan Ashraf yatashi kice ni na wuce skul pls ki kulammin da kanki ok big bro abinda tace kenan

Ashraf na bude ido ya mike domin wani irin fitsari yakejin ta rike mashi mara sannan ga wayarshi sai faman ruri yake dauka wayar yayi ya kara a kunnenshi bai tsaya jiran abinda za a fada ba sai yafara ummana shikenan Aneesa bazata yarda ta aureni ba ummat zan mutu umma sai faman suruttai yake tayi kamar wanda ke neman zaucewa jin haka yasa umman shiga tashin hankali

Tace son meke damunka anya ba zazzabi bane pls ka kwantar da hankalinka Ashraf ya fashe mata da kuka jin hakan ba karamin tashin hankali yasata ba tayi iya kokarinta kan taga ta rarrashi dan nata tilo amma abin sai karfi yake ganin ba sarki sai Allah ne yasa tace toh Ashraf wai me kamata ne meke faruwa shiru yayi dan baima san ta inda zai fara ba gayama ummanshi cewar yaso yayima diyar mutane fyade ba

Umma nidai dan Allah ki bata hakuri karta barni idan tabarni ina zan saka raina tabbas saidai na mutu dan bazan iya rayuwa batare da Aneesa ba

Umman ta rarrasheshi sannan tace maza kayi alwala kayi nafila ka roki Allah ya kawo mafita ni kuma zanyi magana da ita Aneesar kaji koh

Toh kawai yace sannan ya share hawayenshi yana fadin umma sai najiki umma dan Allah ki kirata yanzu toh kawai tace sannan tace toh kadaina yin kuka kamar dan yaro in ba haka ba bazan kirata ba ai dawuri yayi smile yana cewa umma har dariya mafa nakeyi itama dariyar tayi dan ta tabbata danta ya fadama aneesa sosai

Sallama sukayi nan yaduba time ganin 11am hankalinshi ba karamin tashi yayi ba dan idan da abinda ya tsana toh shine barin yin sallah sam Ashraf baya wasa da ibada duk shaye shayenshi da yakeyi baya bari ta haneshi yin ibadah

Amma sai gashi yau saboda bacin rai da kuma shan giyarda yayi yayi lattin yin sallah mikewa yayi har yana cin karo yashige bathroom wanka yayi ya dauro alwala yazo yayi sallah sannan yafito

Aneesa da ciwon kai ya matsa mata ta kasa koda mikewa ne gashi tanajin yunwa kuma bata tunanin ashraf na gidan ita a tunaninta bazai kuma zuwa inda take ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button