BABU SO HAUSA NOVEL

ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Aneesa da ta kulu tsabar kuluwa har bata lura da kayan jikin Ashraf ba saida dj yayi magana nan ta juyo ta kurama Ashraf ido ai kuwa mamakine yakamata domin kuwa komansu kala 1 white short gown ne tasa da red leggis sai yar karamar gyalenta red yasha yar aiki da white stone takalmin kafarta white &red chain bag dinta ma haka hatta earings nata ma haka phone dinta ma red & white ANEESA YAR PRESIDENT kenan

Aneesa nakan mamakin Ashraf sai idonta ya tsinkayi wani babbar bama na pic dinsu ita da Ashraf kuma da kayan jikinsu nan ne tasamu damar bude baki tayi magana kana tace waye yayi wannan danyan aiki?

Tafada tana nuna pic dinsu da yatsa wani ne yafito yace nine nan hajiya kuma wallahi ba laifina bane sani akayi amma hajiya ke bakiga yanda kukayi bala in kyau bane

Aneesa tace ina zan gani bancin ni makauniyace bani da ido kaga malam kayi maza kacireshi kafin ranka ya bace Ashraf yace habaa gimbiyata kiyi hkr babu yanda kika iya da ikon Allah wannan ma kadan kika gani nanda wasu yan kankanin lokaci zakisha mamaki sosai kice nina fada maki

Aneesa ta tabe baki kafin tabudesu danyin magana ai kuwa nan dj yacigaba da tsarasu ashraf sai smile yakeyi yayinda Aneesa kuwa ko ajikinta hasalima Allah Allah take ayi a gama tawuce

Sai watsoma Adama harara taketayi da taga abin nasu bamai karewa bane ai sai ta kama hanya domin barin wurin kan kace me an mata zobe ba hanyarda zatabi tafito tayi magana amma ba wanda ya kulata dolenta ta hakura kujeru ne guda biyu aka nuna masu cewar su zauna bayan sun zauna ne Abban love yafito

Nan yafara magana yana yaba masoyan biyu sannan yana jinjinama Ashraf tabbas sun cika masoya Allah sa muga aurensu hakanan Ameen yan wurin suka amsa

Wasu yan mata ne suka shigo dauke da tray biyu a hannu an lullube tray din da red & white material

Ashraf ya rada mata a kunne cewar gimbiyar Ashraf ki nutsu dan Allah ki kwantar da hankalinki ki daina harara na ba laifina bane kinga taimakonmu Abban love yayi bai kamata mu watsa mashi kasa a idoba dan Allah koma me ke ciki indai kyauta ce ki karba dan Allah ya kare maganar kamar zaiyi kuka wanda har dariya ta kubucema Aneesa batasan lokaci ba bayan tadan nutsu ne tace jibi yanda kk abu kamar wani karamin yaro wallahi Ashraf zakayi bayani ne ai bari agama shashancinnan

Ashraf yace toh bake bane komai bakiso sai nayi maki kalar kuka tukuna ba yana maganar a shagwabe Aneesa tayi smile batace komai ba shima smile din ya mayar mata

A gabansu yan matan suka tsaya Abban love yazo ya bude Aneesa ido ta waro kunsan me tagani?
Kunsan meke saman tray din?
Duk wanda ya bada amsar wannan tambayar dai dai akwai kyauta mai tsoka da zan bayar

Muje zuwa saina jiku masoya

????????‍????by Leemat,
Ashraf dan sudan &
Shaba mai Uwar gida

????????????????????????????????????????
????????????????‍⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????‍⚖????????
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Wannan page din nakine ke kadai sweet sis Sajida marubuciya YAR MAHAUKACIYA Allah daukakaki, Allah sa kifi haka Dear, Allah barmu tare Ina yinki irin so much dinnan ????????????❤????????

UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????

                    24

Aneesa ta waro ido waje ganin wata kyakkyawar farin kyalle yasha ado da red stones sannan ga wani abun hannu ajikinshi an rubuta best lovers of d year tareda crown irin na queens dinnan nan Abban love ya dauko ya kira Adama tazo ta daurawa Aneesar sannan ya bukaci Aneesar da ta tashi tsaye ai kuwa sai taki mikewa Adama na zuwa tayi kamar zatayi kuka tana rokon Aneesa kan ta mike kafin ta mike tsayen tana watsoma Adama harara irin na zamu hade ai

Ai kuwa nan Adama ta rataya ma Aneesa akan kafada irin wannan kyallennan ne na beauty contest an rubuta D.B.L.O.D.Year ma ana D Best Lovers Of D Year

Nan aka hau tafi da shewa sai faman kashe masu pics aketayi Nan Adama ta dauko crowm irin na queens dinnan ta daura akan Aneesa kyau kam gun Aneesa sai hamdala

Daga nan takuma dauko wannan abin hannun ta saka mata a dayan tray din kuwa hulace amma na sarauta shima abu daya ke kai irin na Aneesa sai abin hannu sannan sai wani mafeci fari an bishi da red stones an rubuta D best lovers of d year murna kam gun Ashraf baya misaltuwa sai ayyanawa yaketayi acikin ranshi inama ace yau ne yake angwancewa
Kai kaji Ashraf ko saurin me yakeyi oho????

Abban love yakuma kiran wasu yan mata nan suka fito da wani basket mai kyau Abban love yasa hannu aciki yana fadin jama’a ku shaida sai suka amsa da mun shaida nan yafito da wani glass irin na award shima abu iri daya ke kai sai dai wannan harda sunayensu akai

Mamaki kam har Aneesa ta gaji da ganinsa ya mikawa Aneesa na Ashraf sannan ya mikama Ashraf na Aneesa sannan yace su ba junansu haka ba yanda Aneesa ta iya tana mikawa Ashraf ai kuwa nan ya rike hade da hannunta wani irin shock taji wanda tunda take bata tabajin irinsa ba

Kwace hannunta tayi tana harararsa shikuwa sai smile yaketa sakar mata nan aka fito kuma da gifts cikin bags guda biyu suma white nd red Abban love ya mikawa Ashraf ya mikawa Aneesa nan dai akata tafawa ana shewa ana cewa sai iyayen love Allah barku tare

Wata ce tace kaga LAILA DA MAJNUN
hahahahaha yeaasssss sunan kuwa ya karbesu Abban love yace ROMEO AND JULIET yeeeeeeassss correct wasu suce king and queen wasu suce prince and princess wasu ko cewa sukayi beauty & handsome sunaye dai iri2 akata basu daga karshe dai wani yace sai A&A Lovers of d year shewa aka rinka yi wato yana nufin Aneesa da Ashraf

Haka dai akata laka masu suna nan dai aka cigaba da gashi kida aka sa sai faman rawa aketayi itako ganin an fara rawa kuma an bude hanya yasa tayi niyyar fita tawuce gida ai kuwa Ashraf ne ya kamo mata hannu ta juyo da niyyar disgashi a idanun jama’a amma ina sai ta kasa ganinshi a durkushe a kasa nuni yayi da abashi mike ai kuwa aka mika mashi nan ya karba dj ya tsaida music din sannan wurin yayi tsit ana jiran jin me zaice Aneesa kam ta kagu taji kala manshi

Ashraf na kafa mike din a baki sai ji sukayi yafara waka kamar haka

Tsuntsu sama ya zagayaaaa
Kifi ruwa ya kewayaaaa
Aneesa Yar baiwa kizo muyi soyayyaaaa aaaaaaaaa

Aaaaaaaaaaa

Taho Aneesa muyi soyayya
Taho Aneesaaaaaaaa

Rumtse ido Aneesa tayi Ashraf kuwa yacigaba yana fadin Assalamu alaiki sahibata
Yaki kizo muyi aure mu huta
Na dade inata binki gimbiyata
Domin kinyi haskawa acikinta
Ke kike jamin ragamata
Kin dade acikin raina ya masoyiyaaaaaa

Fizge hannunta Aneesa tayi tafara takawa da niyyar wucewa nan Ashraf yace idan kika barni ina zan sa kaina gimbiya dan Allah ki aminta da soyayyata wallahi idan na rasaki zan iya rasa rayuwata

Aneesa cigaba da tafiyarta tayi ko juyowa batayi ba ganin haka ne yasa ashraf sakin wata kara ai kuwa da smile Aneesa ta juyo kana tace cikin waka itama

Mike sahibina
Ina sonka sahibina
Kaine farin cikinaaaaa mike kazo wurina mai sonaaaaaaa

Tafawa aka farayi ana shewa domin kuwa ba karamin birge mutane sukayi ba Ashraf kuwa da tunda Aneesa ta fara amsa mashi itama cikin waka yayi mutuwar durkushe dagowa da idonsa yayi yana kallon dan karamin bakinta yanda take wakar gwanin birgewa kashe masa ido tayi kana tace taso ka kaini gida ni na gaji pls sannan kabar kallona haka sai kace yau kafara ganina Ashraf ya mike tsaye ya tako har zuwa inda take kana yace Anee Dear anyaa kece?
Ba mafarki nakeyi ba smile tayi kana tace tabbas mafarki kakeyi dan haka kayi maza ka farka kafin ……. shiisshshsh cewar ashraf sannan yace Anee pls ki mintsileni domin in farka kar mafarkinda nakeyi ya jazamin domin kuwa zan…… mintsilarshi Aneesa tayi wanda saida ya danyi kara nan tahau yin dariya bata tsaya jin me zaice ba tayi gaba abinta smile yayi ya karbi mike yayi ma mutane godiya sosai sannan yace dasu bari nayi maza kar gimbiyata tagaji da jirana dariya suka hau yimashi nan ya karba bags dinda ke hannun Adama wanda Aneesa ce ta mika mata su ganin batada abinda zatayi dasu yana karba yabi bayanta yana sauri sukuwa sai faman dariya suketayi suna yaba irin wannan soyayya haka abin birgewa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button