BABU SO HAUSA NOVEL

ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Aneesa ta isa makaranta tayi parkin amma taki fitowa sai faman tunani taketayi tana tambayar kanta dacewar ni Aneesa wa na batawa rai da har yake nemar cutar dani ni Aneesa wa….. bugun glass dinta da akeyi ne ya dawo da ita daga tunaninda take Adama ce tsaye tana smile itama Aneesar smile din ta mayar mata dashi nan tabude tafito Adama tace Dear yau kin danso kiyi latti fa Aneesa tace hmmm kedai bari kawai abin ba acewa komai

Haka dai sukayita hira har suka shiga class shin wacece Adama?

Adama Uwaisu shine cikakken sunanta yarinyace fara kyakkyawa ga hankali da nutsuwa tunda tazo makarantar bata taba yarda tayi kawa ba sbd yanda suke su talakawa ne hakan yasa tarike matsayinta bata shiga tsabgar kowa abinda yakaita makaranta shi kawai takeyi ta dawo gida dama su 5 ne a wurin iyayensu Rumaisa’u,Umar,jibrin wanda suke kiranshi da Abbati sai ita Adamar sai sharifullah

Duk da su talakawa ne hakan bai hanasu karatun boko ba mahaifinsu yana iyaka kokarinsa akansu haka ma mahaifiyarsu Amina itama tana nata kokarin dan ganin sun samu in gantacciyar rayuwa

Haduwarsu da Aneesa kuwa daga Allah ne domin kuwa ko kadan ba ajinsu daya ba saidai dayake Aneesa batada girman kai hakan yasa suka zama kawayen juna

Ranarda Aneesa taje ganin lecturer dinsu nan taga Adama a tsugune tanata kuka tana rokonshi akan ya kara mata lokaci zata biya kudin nan yayita mata koran kare hakan ya batawa Aneesa rai nan ta tallabo Adama take tambayarta bayan ta sanar da ita ne tace yanzu sir akan 3k kake mata wannan wulakancin

Shiru yayi dan yasan wacece Aneesa nan yashiga bata hakuri bude handbag dinta tayi taciro bandir din 1k tamikama Adama sannan ta zari kudi tamikamawa lecturer n yana kirgawa yaga 6k ne yace hajiya Aneesa 6k kika bani instead of 3k budan bakin aneesa sai tace sir ka rike sauran dan naga alamar……. kome ta tuna kuma oho sai tayi shiru nan taja hannun Adama suka fito har sunkai bakin kofa sai tajuyo tace saura kuma kaki yimata abinda yadace nan sukayi ficewarsu suka barshi cikin murna dama ranar ko sisi baida

Koda suka fito Adama tace yar uwa ga kudinki nagode tunda kin biyamin Aneesa tayi smile tace sister karki damu ki ajiyesu incase ko kinada bukatar wani abu
Tun daga ranar suka zama Aminan juna

Cigaban labari Aneesa da Adama sun maida hankulansu gun lecturer daya shigo dama basa wasa da karatunsu ko kadan karfe 11 su Aneesa ne zaune suna hirarsu sai jin ……….

✍????by Leemat

Love u all????????????????
????????‍⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????‍⚖
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

UMMU SAFWAN HAUSA NOVELs????

Wannan page din nakane kai 1 masoyina, abin al faharina,jinin jikina,rayuwana,farin cikina MUHAMMAD LAWAL BONSAY???? miji nagari Allah barmu tare,Allah karemu da sharrin makiya Allah dada hada kawunanmu da dankon soyayya, kaunarka ta mamayemin zuciya I ❤ U so dearly ????????????????

                      10

Sai jin murya sukayi daga sama anyi masu sallama ai kuwa adama ta juyo itako Aneesa ko ajikinta saidai ta amsa sallamar batareda ta juya ba

Adama tace lfy haka mallam ta kanmu?
Shiko yace lfy amma ba lau ba dan Allah ina iya zama Adama ta bude baki kenan zatayi magana sai Aneesa tayi maza tace aa bazaka iya zama a nan ba sbd nan wurin mata ne smile yayi sannan yace haba beauty dan Allah fa nace Adama ce tace toh bismillah mana zo ka zauna kallon Aneesa yayi yace kin bani izinin in zauna tabe baki tayi abin dariya ma yabashi Aneesa tace kana iya zama amma da sharadi cikin kaguwa yaji sharadin yace me sharadin tace bazaka damemu ba

Smile yayi yace naji zan kiyaye dan haka ina iya zama?
Kada kai tamai alamun eh dinnan zama yayi nan Yake tambayar Adama yar kawarmu ya sunanki?

Adama tace sunana Adama Uwaisu nan yace wow nyc name tank u tace mai nan shima yace Sunana Ashraf Sudais nan Adama tace sunan da zan sama dana na farko kenan inshaa Allah smile yayi yace Allah baki iko ameen ta amsa

Sunata hirarsu da Adama amma yana satan kallon Aneesa da ko dagowa ta kalleshi batayiba sai faman latsa wayrta taketa yi ya lura tunda yazo gurin bata dago ta kalleshi ba acikin zuciyarshi yace wannan wace irin mutum ce haka nan ya furta gashi na kamu da sonta kullum saita hanani sukuni yau kuwa ga …… Adama ce tace Ashraf kaida wa?

Ajiyan zuciya yayi yace bkw Adama tace ka kamu da sonta ko?

Ashraf yace kina nufin kinajin abinda nake fada a zuciyata?
Adama tace aa sai dai wanda ka furta a fili

Ashraf yace wallahi Adama na kamune da son wata kyakkyawar yarinya nan yafara describing din Aneesa yana gamawa Adama tace kuma ya sunanta nan yace ban san sunanta ba domin kuwa bata bani daman zuciyata tayi bincike akan sunantar ba amma muddin taba zuciyata izinin binciken sunanta to shakka babu zuciyata zai san sunanta kuma zai sanar dani

Aneesa da take jinsu batasan sanda dariya ya kufce mata ba nan tafara dariya shiko sai faman kallon yanda take dariyar yakeyi ushiryarta mai kyau gata da dimple kai mashaa Allah yarinyarnan tayi a rayuwa Adama ce tace Anee lfy? Bata kulata ba saida tayi mai isarta sannan tace kai amma wannan guy din koh nan ne ta dago idanuwanta ai kuwa karaf idanuwansu suka hade dana juna wani irin abu sukaji ajikinsu gabaki dayansu

Subhanallah aneesa ta furta a fili shima haka maida idanuwanta kasa tayi shiko yace meya baki dariya beauty?

Adama da tariga ta dagosu smile tayi nan tacema Aneesa eh meya baki dariya nan Aneesa tace jin wannan abokin naki daya fadin wai zuciyarshi zatayi searching sunar masoyiyarshi ne yabani dariya dan ban taba ji ba wani dariyar takuma yi

Shima dariyar yayi dan ya dagota tana so tace mai makaryaci amma kuma sbd ganin girman dan adam yasa ta kasa

Nan yace mata eh mana kuma idan kina ganin wasa ne sai inje inyi searching kuma tsab zan gano sunarta smile aneesa tayi kana tace toh bismillah je kayi nasan saidai kaje ka tambayi wasu

Ashraf yace idan kika ganta ko toh ko ke saikin bata sunarda zaiyi matchin da ita bare ni masoyinta

Aneesa tace toh kaje ka sanar mata abinda kk ji mana game da ita nan yace toh ai bazan iya ba sbd ban taba yin hakan ba

Wani kallon tuhuma Aneesa tabishi dashi Adama ce ta katsesu nan sukaci gba da hira har lokacin shiga lectures dinsu Aneesa yayi nan sukayi sallama da juna Ashraf sai ji yakeyi kamar yabisu amma ba dama karfe 4 daidai suka fito nan suka shiga motar Aneesa daman tunda suka hadu da juna itace ke dauko Adama tazo ta sauketa a gida wani lokacin ma tare suke zuwa makaranta A motar Aneesa

Aneesa takai Adama har kofar gidansu Ashraf kuwa na biye dasu nan Adama tafita tayi cikin gida sannan Aneesa ta juya tayi hanyar gida itama ganin kamar mota na binta a baya ne yasa taja burki ta tsaya Ashraf na ganin haka sai yayi kamar ba ita yake biba har yazo yawuceta kasancewar tint glass ne ya hana Aneesa ganin fuskar wanda ke ciki

Nan tafito ta sayi su fruits sannan taja motarta shiko ashraf koda yayi gaba kadan nan yayi parkin ganin wucewarta ne yasa shima tada motarshi yabita ganin ta tsaya a Alhaji Abbas Estate ne yasa yayi smile a zuciyarshi yace woww lallai dole yarinyarnan taja aji

Baba ya bude mata gate tashige bayan tayi parkin ne ta fito da su fruits dinda tasayo tazo ta mikawa mama bayan ta gaishesu kamar yanda ta saba nan tayi wucewarta part dinta dan yin ibada tana shiga ……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button