ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL
Aneesa kuwa tana isa wurinda ake parking motoci nan ta tsaya ganin babu motar Ashraf a wurinne yasata cigaba da tafiya sai faman tunani take tana mamakin kanta anya kuwa nice Aneesa?
Nice nayi waka a gaban mutane ko kunya babu saboda Ashraf?
Toh wai yaushe nafara jin soyayyarsa a zuciyata hmmmm Gimbiyata.. ….
Jin haka yasa Aneesa ta tsaya cak saidai bata ko juyo ba domin kuwa tasan ko waye ke kiranta zuwa yayi yace habaa gimbiya ina zaki bataredani ba yakarashe maganar lokacinda ya iso gabanta ya tsaya sai faman maida numfashi yake tayi
Aneesa tace………..
✍???? by Leemat
Toh wannan karan babu wanda yaci wannan gasar ni nacinye abina ???????????? kai amma anshaa daku masu karatu ????????????????
Ina yinku so much ????????????
????????????????⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????⚖????????
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
Wannan page din nakine ke kadai SIS FEEDOHM marubuciya ZAN RAYU DAKE ina mai tayaki murnar kammala novel dinku lfy kamar yanda kk farashi lfy Alhmdllh Allah saka da alkhairi darasinda ke ciki kuma Allah bamu ikon yin aiki dashi Ameen
????????????????????????????????????????
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????
25
Aneesa tace yoh toh ko ina zani dole saida kai? Ko kuwa wata salon takurace ka fito dashi kuma?
Ashraf yace Allah huci zuciyar gimbiya sarautar mata amin afuwa tuba nake ya karashe maganar yana rike da kunnuwanshi biyu2
Abin yaso bata dariya amma sai ta matse kawai tace toh idan na tsaya jiranka dame zaka kaini gida bancin baka zo da car dinka ba
Smile yayi kana yace baga bayana nan ba basai ki hau na goyaki ba ya juya mata baya alamun tahau
Aneesa batasan sanda dariya ya kufce mata ba saida tayi mai isarta sannan tace lallai kam Ashraf sannu da kokari kaga nidai na tafi domin yamma tayi kar su mama sujini shiru
Ashraf yace toh dan Allah kizo muje na kaiki da kaina banaso wani ya ganemin kyakkyawar fuskarnan ……
Aneesa tace kaidai kasani toh muje nan yayi mata nuni da suje ba musu tabiyoshi komawa sukayi inda ake parking motoci
Nan yamata nuni da wata kyakkyawar moto kirar BMW fara sal sai flowers da aka ma motan kwalliya dashi red Aneesa tayi smile kafin tace……..
Ashraf wai shin in tambayeka mana Ashraf yace ina jinki gimbiyata
Aneesa tace wai meyasa kasa flowers red akan motarka kuma meyasa ka canzo dressing dinka into red nd white?
Ashraf yayi smile sannan yazo ya bude mata murfin mota alamar tashiga yamata ba musu ta shiga ta zauna ya rufo kofar sannan ya zagayo yashiga mazaunin driver ya tada motar bai bata amsa ba kuma itama bata kuma cewa dashi uffan ba
Ashraf ne ya katse shirun dacewa Anee Dear uhmmm kawai tace sannan yace kinsan ina kaunarki kaunarda ban taba yimawa wata ya mace irinsa ba apart 4rm mom dita ba
Ko kinsan ke kadaice macenda na fara furta mawa kalmar i love u
Ko kinsan….. Aneesa ce ta katseshi dacewa nifa ba abinda na tambayeka kenan ba tohm
Ashraf yace ok naji amma ai naga ba laifi bane dan ina amayo maki abinda ke raina ba
Aneesa ina matukar kaunarki fiye da tunaninki shiyasa komai namu nake kokarin in ga yazama daya dalilina kenan nayin hakan tsabar kaunarki ne yasa haka
Aneesa ko kunya ya hanata dagowa ta kalleshi dan ganin yanda yamata kwarjini
Fuskarta na kallon gefe tace soyayyar karya mukeyi ai skyayyar 2 weeks wanda bazai ……..
Bata iya karasawa ba jin yanda Ashraf yawani taka burki tsoro ne ya kamata nan ta dago ai kuwa ido biyu sukayi ganin yanda idon Ashraf ya canza kala lokaci 1 yaba Aneesa tsoro sosai
Ta bude baki tace Ashraf lfy meke damunka ai kuwa kamar data sani da bata tambayeshi ba nan yahau yimata kuka kamar wani dan small boy dakyar ya iya bude bakinshi yace Aneesa kasheni kikeson yi koh?
Aneesa wai ya kikeso inyi da rayuwana ne?
Aneesa bazan iya rayuwa ba in batare dake ba
Aneesa ki……. bai karasaba ya kamo hannunta ya daura saman kirjinshi Aneesa sai kokarin janyewa take amma ina takasa
Ashraf yace kina jin yanda take bugawa domin ki
Toh duk randa kk rabu da ita a ranar zata daina bugawa
A ranar zata…..
Aneesa tace Ashraf pls rake me home
Ko kana tunanin zuciyarka ce kadai take bugawa hk
Ko kana tunanin ko Aneesa bata damu da wanda ya damu da ita bane
Ko kuwa ka dauka Aneesa batada zuciya ne
Ashraf ina kaunarka
Ashraf I Love U too ……….
Rike bakinta tayi domin kuwa batasan lokacinda ta furta hakan ba wani smile Ashraf yayi hadeda ajiyar zuciya kiss yamata a hannu fizgewa tayi
Ashraf ya daga hannayensa bibbiyu yanama Allah godiya Aneesa tace pls take me home
Tada motar yayi yana smile har cikin estate din yashiga da ita kokarin fita tafaryi ai kuwa taga yana lock
Wani harara ta watsomai yi yayi kamar baimasan tanayi ba har saida tace wai Ashraf me hk ne
Cemata yayi kamar me?
Sweetheart pls kicemin nayi kyau mana kamar yanda nace maki dazu
Smile tayi kana tace ok toh idan nace kayi kyau zaka budemin eh yace
Ai kuwa nan tace mashi kayi kyau ashraf kuma tsarinka yamin kyau motar nan dakamata kwalliya itama tamin kyau
Lumshe ido yayi wani irin farin cii na ziyartar zuciyarshi
Anee Dear komai naki yamin Allah barmu tare niko nace Ameen
Nan yabude mata zata sauka yace wait fitowa yayi yabude mata tafito sannan yace mata pls tek very gud care of ur self 4 me I really really so much love U my queen uhmmm….. kawai tace
Har tafara tafiya kome ta tuno kuma oho sai ta juyo tace tanks 4 today Ashraf I Love U
Sannan tawucewarta part dinta Ashraf kuwa komawa motar yayi cikeda farin ciki yau fa kakarshi ta yanke saka
Da shigarta bayan tayi wanka tafito bata fi 20mins ba saiga kiran Adama kin daukawa tayi dan tasani iskanci kawai takeaon yimata
Ashraf kam tunda ya isa gida sai faman waka yakeyi yana godiya ga Allah yaje ya sanar ma ummanshi itama tayi murna sosai nan tace ranar saturday ya kawo mata Aneesar ta ganta sannan tamasu fatan alkhairi
Koda dad dinshi yadawo shima nan mom dinshi ta sanar mashi shima murna yayi sannan yabisu da Addu’a
Karfe 8:30pm Ashraf yashigo bai tsaya ko inaba sai part din Aneesa wacce take zaune a varanda tana karanta wani novel mai dadin gaske mai suna LEEMAT DA CHOKALI na Hannatu Dada Kuta
Da sallama ya isa gurin yana smile a hannunshi dauke da bag mai kyau ya zauna nan suka hau hira ta masoya bashi yabar unguwarsu ba sai 10pm shima dan Aneesa ce ta matsamai kan yawuce
Yana isa gida ya kirata ta waya nan suka cigaba daga inda suka tsaya har saida sukayi barci basusan lokaci ba
Washe gari da safe Ashraf yazo yakai Aneesa school soyayya ce mai karfi yashiga zukatansu cikin yan kwanakinnan biyu
Yau takama friday Aneesa ta shirya domin karfe 10am ???? zai ✈ zata kaima yayanta Abdu-basit ziyara
Ashraf kam yacika fam dan ba ason ranshi zatayi tafiyar ba koda yazo cemata yayi ……… ………
By Leemat & Chokalin potiskum
Love u all????????????
????????????????⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????⚖????????
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
Wannan page din nakune yan group din YOBE STATE WORLD WIDE sama tayima yaro nisa sai dai ya…………… saimu masu kaunar juna saimu masu……. ???? Allah bar kauna Ameen????
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????
26
Cemata yayi yanzu da gaske kike sai kin tafi cen U.S.A din? Habaa mana dear ya kikeson nayi da rayuwata