BABU SO HAUSA NOVEL

ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Tayi mai Addu’a Allah kawoshi lfy ya amsa da ameen nan sukata hirarsu ta masoya yayanta sai mamakin ta yakeyi sannan yana mamakin yaushe tazama haka

Sun dade suna hira daga karshe dai sukayi sallama da juna akan saiya iso

Cikin ikon Allah kuwa saiga Ashraf ya iso itada yayanta ne sukaje daukoshi tsabar murna batasan sanda taje ta rungumeshi ba

Ai kuwa nan yayanta ya harareta kunya ce ta kamata shiko Ashraf mutuwar tsaye yayi dan bai taba zaton Aneesa zata iya haka ba

Dan tabashi tayi wanda ya dawo dashi hayyacinshi dariya tayi kana tace ya hanya gaskiya habibi naji kewarka fa sosai

Kullum saiji nakeyi kamar in zama tsuntsu in…… yayanta ne yayi gyaran murya wanda yasa Aneesa rufe fuskarta da tafin hannunta

Smile yayi yace mara kunya a gabana koh
Ashraf yamika masa hannu sukayi musabaha da juna nan suka kama hanyar komawa gida Ashraf sai satar kallon Aneesa yakeyi wacce tunda yayanta yace mara kunya ta kasa bude ido bare ta kuma yin magana

Dan karfin hali tayi ta dago dan kara kallon masoyinta saidai tana dagowa suka hada ido dashi kashe mata ido yayi wanda batasan sanda tafurta ya salam toh wannan wane irin kallo ne haka eh Ashraf

Sun isa an bashi masauki cewa yayi bari ya watsa ruwa haka kuwa akayi Abdul basit yafito ya shaidawa Aneesa yashiga bayi dan haka tadan bada lokaci kafin takai mashi abinci minti 20 Aneesa tamike ta kwashi lafiyayyun food flask tayi hanyar dasu tana isa bakin kofar tayi sallama Ashraf dake zaune yana waya da ummanshi ya amsa shiga tayi wani irin kyau yaga ta kara mashi jin wani yar yar yasashi dauke idonshi daga gareta yana Astagfurullahi

Aneesa kam smile taketamar cema umma yayi eh itace tashigo in bata ne ok mikawa Aneesar wayar yayi yana kallonta

Sallama tafarayi umma ta amsa sannan tace yata kina lfy ina nan inata kewarki yaushe zaki dawo ne

Smile Aneesa tayi kafin tace next week inshaa Allahu

Allah kaimu yata ki kulammin da kanki sannan inaso idan kin dawo kibamu izini muje muga magabatanki domin son dina ya kasa zaune ya kasa tsaye but am sure yau yana cikin farin ciki ganin gashi ga masoyiyarshi kai wannan abu yanamin dadi Allah sanya Albarka Allah sa ayi damu

Aneesa ta mika mashi kafin tace ameen jin muryar Ashraf ne ya shaidawa umma Aneesa kunyarta take cewa tayi lallai kam yarinyarnan batasanni bane smile tayi kafin tace son ka kulammin da diyata fa dakyau sannan karka takuramin ita

Ashraf yace toh umman gimbiya bayan ya katse wayar ne umma tace gaskiya Aneesa tayi a rayuwa duk da ban zauna da ita ba amma inajin kaunarta har cikin ❤ dina

Aneesa kenan haka take yar baiwa ce………….

Serving dinshi tayi ci yake yana sumbatu har yakoshi yayi yayi da ita taci taki wai acewarta ta koshi

Bayan ya gama ne ta kwashesu takai kitcen koda tadawo domin goge wurin sai tagani a goge smile yayi yamtso inda take saura kdan su tabi juna kallonta yakeyi kunya ce ta kamata nan ta juya domin barin dakin dan yanda kirjinta ke bugawa da sauri da sauri

Ai kuwa sai ji tayi ya riko hannunta ta tsaya chak saidai bata juyo ba Ashraf da tun shigowarta yakeji inama ace halaliyarshi ce ita ai da babu abinda zaisa ya sassauta mata yau

Yace Gimbiyata nagode da wannan lafiyayyan girki mai kamshi da dandano da kikamin Allah biyaki dan Allah gimbiyata kibar azabtar dani ki bani izini natura magabatana domin a daura mana aure wallahi ina kaunarki

Aneesa ta juyo saidai ta kasa hada ido dashi dan tausayi yake bata matsowa kusada ita yakuma yi ya rungumeta abu kamar wasa ya fara kokarin shafata ganin haka yasa Aneesa ta zame jikinta da gudu ta fita bata tsaya jin abinda zai fada ba

Jikinta ne ya hau kyarma data tuno cewar Ashraf fa ba muharraminta bane ya rungumeta kuma yake neman shafata

Bayi ta nufa don jin fitsari na neman zubo mata saidai ga mamakinta data shiga bathroom din koda tacire pant sai gani tayi wani ruwa mai yauki yana fitowa ta gabanta cewa tayi oh ni Aneesa me hk ????‍♀

Wai meke shirin faruwa danine?

Ashraf kam dakyar yasamu nutsuwa yadan kwanta dan hutawa har karfe 6pm bai kara sa Aneesa a ido ba sai ji yayi bai kyauta ba kilama tana fushi dashi ne

Ita kuwa tanacen tana hada musu better da zasuci na yamma hira suke da Abdul basit saidai ina hankalin Ashraf ba akanshi yake ba jin kamshi ya gauraye gidanne yasa Ashraf lumshe ido cen yakuma budesu kafin yace Allah mallakamin ke gimbiya

Abdul basit yace Ameen dan tun dazu yake ganin take taken Ashraf ya gane hankalinshi baya jikinshi kana yace Ashraf karka damu indai lil sis ce inshaa Allahu kai zamuba

Kunya takama Ashraf dan shi baimasan a fili ya furta ba nagode kawai yace nan yace da Abdul basit ko zan iya shiga na ganta

Y not yace dashi mikewa yayi ya nufi hanyar kitchen din dan har yariga yasan ko ina na gidan domin kuwa dazu daya fito Abdul basit ya shigar dashi ko ina lungu2 sako2 na gidan

Ashraf ya tashi ya nufi kitchen din tana kwashe abinci daga pot tana zubawa a flask gimbiya Asraf yace amma bata ko kulashi ba matsowa yayi yana kokarin rikota ta baya ne tajuyo tana fadin kar ka sake ka tabani

Hawaye suka ciko mata Ashraf yace yi hkr natuba ya tsuguna yana rokanta

Smile tayi tace toh mike habibi amma pls mubar yin haka baida kyau kar shedan watarana ya……

Shiiiiii….. Ashraf yamata nuni datayi shiru kafin yace Allah tsaremu da sharrin shaidan Ammen ta amsa smile sukawa juna yajuya taci gaba da aikinda ke gabanta shikuma yana taimaka mata har suka kammala tare bayan sun fito ne Aneesa tace bari taje ta watsa ruwa shima haka yace mata yawuce dakinda aka ware mai bayan sun fito karfe 6:40pm sukayi sallar magrib sannan suka zauna cin abinci har sunci sunsha Aneesa ta kimtsa wurin ta dawo ta kwantar dakanta akan cinyar yayanta gyaran murya yayi wanda ya maido da hankulansu kanshi

Yafara dacewar nasani kunason junanku sosai wanda bakwa kaunar daya yayi nisa yabar daya amma inaso kusani kar ku bari shaidan yayi amfani da soyayyarku har tagaiku ga halaka

Jikin Aneesa ne yayi sanyi nan tafara tunani kenan yaya yasan komai shafa kanta yayi yace lil sis dazu daya wuce kitchen nabiyoshi domin kuwa nasan ba muharraminki bane duk da na yarda dashi nan ya kwashi komai dasuka fada a kitchen din baki suka sake suna mamaki

Bayan ya gama fada masu tareda yimasu nasiha ne yace masu shi zai shiga daga ciki da yayi sallar ishaa’i zai kwanta dan yanada lectures da safe toh Allah tashemu lfy suka mashi yace Ameen yamike yashige ciki Aneesa tamike tace tashi muje mu sauke farali

Bayan sun idar da sallah ne suka fito dan cigaba da hirarsu ganin Abdul basit sukayi a zaune wanda duk gwadasu yakeyi saidai bai bari sun ganoshi ba

Zama sukayi hira sukeyi hankali kwance su ukun idan hkagansu saikace sun tare suka taso

Nan Ashraf ke shaida masu cewar zuwa jibi zai wuce Syria dan akwai abinda yakeso yayi acen fuskar Aneesa ce ta canza nan tamike tana fadin saida safenku ni inajin barci smile Ashraf yayi dan ya dagota batason wucewarshi ne yasa tamike shikuwa Abdul basit yace ok Allah tashemu lfy ameen tace tashige abinta

Hajja rahma ta kasa samun biyan bukatarta abin sai haushi yake bata musamman da taji hajja fatima na fadin ai yarku takusa aure in Allah ya yarda a wurin meeting dinsu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button