BABU SO HAUSA NOVEL

ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Ashraf na fitowa bai tsaya ko inaba sai dakin Aneesa dan umma takirashi ta shaida mashi number aneesar bata shiga wayarta a kashe take shima tun jiya yayita kokarin kira amma a kashe take

Da sallamarshi yashiga jin muryarshi yasa aneesa mikewa da wuri tana fadin kafita min a daki dan Allah na rokeka kar kamin illa dan Allah ka rabu dani bana sonka bana son ganinka kuka takeyi sosai hawaye ke zuba a idanunshi sai tafiya yakeyi yana matsowa inda take ya ce dear bazan taba cutar dake ba wallahi ban san meya shigeni ba jiya kiyimin afuwa natuba bazan kara ba

Dan Allah kiyafemin Hannu yakai dan share mata hawayenta itako ta dauka ko zai kuma rungumeta ne ai batasan sanda tasaki wata kara ba nan tafadi kasa sumamma Astagfirullah Ashraf ya furta yana daukarta ya kwantar da ita saman gado ya koma ya dauko rufa da towel yazo yana shafa mata jin yanda jikinta yayi zafi ne yabashi tsoro

Sannan ga idanunta sun kunbura ya salam ya furta yana hawaye yana magan ganu aciyar zuciya tayi tafara bude idonta ganinshi kusa da ita ne yasata rumtse idonta Ashraf yayita bata hkr amma ina taki hakura kuma taki bude idonta suna haka ne cikinta tayi wani kara kululululuuuu……..

Ashraf yamike ya nufi kitchen ya hado mata tea mai kauri sannan yayi toasting bread ya kawo mata kinci tayi duk da kuwa kamshinda bread din keyi smile Ashraf yayi kana yace da ita ok ooo tunda bazakici dan Allah ba toh zan maki irin najiya yafada yana murmushi kamar da gaske

Tabe baki tayi tace shege kafasa…..

Ashraf yace nine shege?

Aneesa tayi shiru bata tanka ba ganin yana matsowa kusa da ita ne yasata sakin wani kukan kuma tana fadin Allah kasake ka tabani sai na kashe kaina jin hakan yasa ya tsaya sannan yace toh karba kishanye ba musu ta karba sannan tace toh idan na shanye zaka barni kuma zaka fitammin anan

Eh kawai yace batareda ya kalleta ba yamike yafito dauko panadol yayi yakoma cikin dakinta ga mamakinshi sai gani yayi ta ajiye tray din ta hade kanta da gwuiwa tana kuka tausayinta yakamashi da dana sanin abinda yamata dan yasan shiyasata shiga wannan halin

Zuwa yayi ya tsuguna yana hawaye yana neman gafararta bata amsamai ba ajiye mata maganin yayi sannan yamike yakama hanyar fita yana fadin dan Allah kisha tea sannan ki hadiye magani ki yafe min ki yafe m……….

Jin fadiwan abu yasa aneesa dagowa da idanunta da suka riga suka kumbura ganin Ashraf a zube a kasa ne yasa ta mikewa da gudu ta iso inda yake kwance tana jijjiga shi tana fadin dan Allah katashi Ashraf na yafe maka duniya da lahira dan Allah ka tashi da gudu ta dauko ruwa ta watsa mai fara bude ido yayi ya saukesu kanta smile ya sakar mata kana yace Aneesa na rantse da Allah kina barina zan mutu ki taimaka ki yarda dani wallahi jiya sharrin shai……..

Shiiiiiii….. tamashi kana tace ya isa pls mubar maganar nan yamike ya dauko tray din yayi feedin dinta sannan tasha magani yace ta kwanta ba musu ta kwanta zama yayi ya kura mata ido kaunarta na kara ratsashi tabbas ya yarda Aneesa ta daban ce Allah kasa na rayu da ita na mutu da ita ……….

Aneesa har barci ya kwasheta saidai sa’i 2 tana ajiyar zuciya Ashraf ma a nan zaunen barci ya kwasheshi anan din

Karfe 1da rabi na rana Aneesa ce tafara bude ido ganin ashraf sai faman barci yaketayi kuma ga wuyarshi bata daidaita ba yasa tamike taje ta gyara mai wuyar sannan tafita kitchen tawuce ta fara hada abinci ta koma dakin yayanta tashiga bathroom dinshi ta watsa ruwa tareda yin alwala nan taji dadin jikinta ta nemi ciwon kai ta rasa wani karfi karfi takeji Alhmdllh ta furta bayan ta idar da sallah ne ta koma kitchen ta gama hada komai sannan ta kama hanyar dakinta don tadashi saidai ga mamakinta tana shiga sai bata ganshi ba fitowa tayi taje daidai kofar dakinshi tana tsaye ta kasa shiga zuciyarta sai bugawa take rumtse ido tayi wanda yayi daidai da bude kofar Ashraf ganinta a tsaye ne yasashi smile kana yace gimbiya ina yini ya karfin jiki smile tayi tace naje domin in tasheka amma sai ban ganka ba

Shine nace bari inzo nan smile yayi yace ai nazo nayi wanka ne sannan na sauke farali hop kema kinyi sallah

InshaaAllah tace sannan ta juya tana fadin bismillah zomuje kaci abinci

Wowwww me gimbiyata ta shirya min bata amsa mai ba saidai smile taketayi

Bayan sunci sun sha ne Ashraf yakuma bata hakuri da yimata alkawarin bazai kara ba sannan yace sufita ganin gari yakuma roketa akan ta kunna wayarta

Sun fita sukasha yawo basu suka dawoba sai wuraren 5pm lokacin yayan Aneesa ya dawo bayan sun huta ne Abdul basit ke masu albishir cewa yayi waya da Abban Ashraf inda Abban Ashraf ke rokon shi akan ya turo mai da number dad dinsu koda ya sanar dashi sunan dad dinsu ashema abokan juna ne da Abban ashraf din domin kuwa a yanzu maganarda nake maku suna tare da juna a china yanzu haka sannan abbanshi ya riga ya roki alfarma gun dad cewar yaba danshi ke kuma ya bashi saidai mu roki Allah sa albarka

Cikin kunya Aneesa tace Ameen amma yaya ……. Ashraf amma yaya me haba dear karkimin haka kinsani ina sonki ina kaunarki banda kamarki

Gaskiya banda abinda zance maka bro sai godiya Allah barmu tare ameen suka amsa

Washe gari Ashraf ya komo nigeria dan acewarshi yama fasa zuwa syria din domin kuwa maganar aurenshi da Aneesa tafi mai zuwa syria

Koda dad yakira Aneesa ya tambayeta cemashi tayi ta amince Allah sa hakan tafi alkhairi wanda dad yaji dadi sosai yayita samata Albarka

Da isan ashraf yace shifa a tura gidansu Aneesa ai kuwa shima ya shirya sai niger mom taji dadin zuwanshi domin kuwa ashraf nada shiga rai da wuri

Hakan yasa suka saba da ita kamar sun dade da sanin juna su Abba kuwa sun dawo lafiya har anje gidansu Aneesa an saka ranar Aurensu nan da wata 5 Ashraf baiso haka ba danshi bai damu asaka ranar aurensu nan da sati daya ba

Saidai dad yaki amince wa da hakan saboda karatunta sannan gashi yafito takarar president wanda yake saran zai ci wamda nan da 1month za ayi zaben hakan yasa Ashraf ya hkr

amma badan yaso ba saidai dan ba yanda ya iya ne ranarda Aneesa ta dawo murna kam agun masoyan biyu ba acewa komai

Sai faman zolayarta yakeyi yana cewa Amaryar Ashraf

Akwana a tashi ba wuya a gun Allah yau ana saura 2mnths ayi bikin su Aneesa Alhaji Abbas kuwa Allah baiyi ba anyi magudi agun zabe domin kuwa yanada mutane saidai bai yarda da cin nose ba shiyasa aka kayar dashi badon baici ba aa sai dan cin nose da rashawa

Bai damu ba domin yayi imani da Allah inda ace Allah yayi zai zama president din da babu wanda ya isa ya canja abin tabbas wannan haka take Alhaji Abbas mai tawakkali ga Allah

Aneesa da Ashraf kuwa babu wanda baisan soyayyarsu ba A&A wasu ke masu lakabi wasu kuwa best lovers of d year sunaye dai iri iri

Yau Aneesa ta kammala karatunta kuma yau yarage 3weeks da bikinsu tana shirye shiryen komawa Niger state dan anan ne za ayi shagalin bikinsu sai taji kamar mutane na shewa acikin part dinta bata damu ba tacigaba da abinda takeyi

Kiran Ashraf yashigo tace mashi ai ita tariga ta wuce ai kuwa jin haka yasa Ashraf gayama Abokinsa nan Abban love yace su hadu a club haka kuwa akayi sun zauna suna shan giyansu sai ga kiran Aneesa yana dagawa cikin maye yace mata waye ke damuna lokacin shanawana kai wai bazakazo club bane yau muna nan munata bugar da kwalabe kaga gimbiyata ta tafi ta barni dan haka yau sainama kwalabe kacha kacha kuma ………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button