ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

4
Hajiya Fatima tace haba hajja rahma meyasa kin kk ma Aisha haka ne ko kinsan munfi yarda da aisha acikin gidannan akan sauran yan aikin domin aisha ta daban ce dan Allah kirage tsanarda kike mata yanzu ji yanda kk sa anee dear tayi fushi taki cin ma abincinda na hana kowa ya hada mata nida kaina nashiga kitchen na hada mata dan welcomin dinta gaskiya hajja rahma banji dadin abinda kk yiba hajja rahma ko ko ajikinta sai gyara zama da tayi dan kwasan gara
Hajiya fatima ta maida kallonta gun Aisha da taketa zubda hawaye tace Aisha yi hkr kinji Aisha tayi murmushin karfin hali kana tace bakomai Hajiya sannan tajuya da nufin barin wurin hajja rahma tace ke dan uban.. wa kk so yayi servin dinmu? Nan da nan aisha ta juyo ta……
Hajiya fatima tace Aisha diba abinci ki kaima Anee Dear daki ki rarrasheta kuma ki nuna mata komai ya wuce Aisha tayi smile nan ta diba abinci ta dauki juice da cup a tray takama hanyar dakin Aneesa
Tana isa tayi sallama jin muryar Aisha yasa Aneesa ta saki smile kana amsa sannan tace shigo abinki sister Aisha tashiga Aneesa na kallonta suka hada ido sai smile suka sakarwa juna Aisha taje ta ijiye tray din a saman gadon Aneesa
Aneesa tace Sister kiyita hakuri da hajiya rahma domin kuwa….. Aisha ta katseta dacewar ai yariga ya wuce dan haka yanzu kici abinci Aneesa ta rungumi Aisha na wasu yan seconni sannan ta saketa kana tace wallahi Aisha ina matukar jinki ajikina kamar yar uwata ta jini Aisha ta murmusa tace nima haka nake jinki sister na ta kaina
Nan Aneesa tamike taje ta dauko spoon ta ce ma aisha suci tare ba musu suka fara ci idan ka gansu gwanin sha awa wannan kenan…..
Koda suka kammala Aneesa ta hana aisha fita tace saidai suyi fira ai kuwa haka akayi fira suketa yi har barci barawo ya kwashesu basu suka farka ba sai after 2 da sauri Aisha ta mike ta hau hada plates dinda sukaci abinci Aneesa tace sister ai kya bari kiyi sallah ko kafin ki fita Aisha tace toh shikenan tashiga bathroom ta dauro alwala tafito tana jiran aneesa dan suyi jam’i Aneesa na fitowa nan sukayi sallah bayan sun idar Aisha tace sister ina bakin ciki a duk lokacinda kika koma makaranta kinsan meyasa ?
Aneesa tace aa sai kin fada sai Aisha tafara hawaye tace saboda aduk lokacinda kk tare dani sai inji ni kamar ina aljanna amma idan bakya nan ina shiga damuwa har wani lokacinma sai inji inama ace mutuwa ta daukeni dan in huta……..
Takarashe maganar tana kuka mai tsumar da zuciya Aneesar ma hawaye take batasan lokacinda ta rungumi Aisha ba sai kuka suketayi dukkansu biyu babu mai cema daya bari suna cikin hakane hajiya Fatima tashigo mutuwar tsaye tayi cen tace…………….
✍????By LEEMAT
Love U Ol????❤????????
????????⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????⚖
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELs????
5
Cen tace wai ku kenan kullum bakuda aikinyi sai kuka kamar wayanda aka aikomawa da sakon mutuwa?
Aneesa tace mom ina tausayama Aisha mom dan Allah kimaida Aisha yarki kisota kamar yanda kk sona????????????
Shiru hajiya fatima tayi nadan wasu seconni kana tace Aisha maza kije ku kammala aikinku domin kuwa yanda ake biyanki haka suma ake biyansu
Aisha ta share hawayenta nan ta juya da niyyar fita har ta gifta hajiya fatima sai ji tayi anriko mata hannu chak ta tsaya bata juyo ba jin muryan hajiya fatima ne yasata juyowa dan ganema idanuwanta abinda kunnuwanta suka jiyo mata smile hajiya fatima ta sakar mata kana tace Aisha?
Aisha tace na am hajiya ta tsuguna a wurin hajiya tace mata Aisha sanin kanki ne duk fadin gidannan babu wanda na yarda da ita domin kuwa halayyanki daban yake dana saura aisha inaso kisani ina kaunarki sosai saidai hajja rahma ta tsaneki bansan dalili ba amma karki damu Allah zai sa tasoki wata rana
Kiyita hkr da halayyarta kinji sannan inason in sanar dake cewar zan maidaki makaranta Aisha kuka tafarayi na farin ciki tanata godiya da addu’oi hajiya ta dagotatana kada mata kai alamar aa dinnan ganin taki yin shiru ne yasa Aneesa tazo ta rungumeta nan hajiya fatima ta rungumesu su biyun tanata faman kwarara masu albarka cendai hajiya tace masu suje shan iska a waje ba musu suka fita Aisha kam dawowa tayi ta tsuguna kana tace hajiya wane aiki ma kk ce inje in kama?
Smile hajiyar tayi kana tace ni daga yau ki daina kirana da hajiya ki rika cemin mom kinji toh kawai aisha tace sannan hhajiya tace daga yau kin daina yin aiki makaranta kawai zaki rinka zuwa cikin kunya da jin dadi aisha tamike tana godiya sannan tace Allah dada budi mai albarka mom dina aguje tafita
Murmushi hajiya tayi dan har cikin kasan zuciyarta taji dadi ashe duk abinda suke yi duka a kunnen hajja rahma
Niko nace babban magana
Bayan 2days halayyan Aneesa ya fara canzawa kullum yakasance batada aikinyi sai wulakanci da musgunawa al’umma ga rashin kunya abin duk ya daurema kowa kai
Hatta mom dinta ta kasa gane kanta Aneesa abinnata sai cigaba yakeyi kullum abin mamaki kuwa shine tafi tsanar Aisha
Kwata2 bata kaunar ganin Aisha a rayuwarta ita kuwa Aisha kullum cikin damuwa take domin kuwa ta dauki Aneesa tamkar jininta ana cikin haka ne wata rana…….
✍????by leemat
Love u all????????????????????
????????⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????⚖
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????
Wannan page din nakine HAJMA Dear nagode da addu’arki da fatan Alkhairi gareni kina raina Allah bar kauna ????????❤
6
Wata rana Aisha tashiga dakin Aneesa domin yi mata nasiha sannan ta tambayeta laifinda tamata dahar yasa tafi tsanarta acikin duk masu aikin gidan duk da Hajiya Fatima ta hana Aisha yin aikace2 amma bai sa ta daina kirga kanta acikin yan aiki ba
Tashiga dakin da sallamarta Aneesa na kallonta amma bata ce mata komai ba sai amsa sallamar datayi
Aneesa na kallonta harta zauna kana tace sister na takaina nazone in tambayeki laifinda namaki kike fushi dani kuma kika tsaneni haka kamar ba keba dan girman Allah ki sanar dani abinda namaki idan kuma bazaki iya sanar dani ba toh kiyi hakuri kiyafemin
Nayi maki alkawarin zan kiyaye koma menene indai bai sabawa mahaliccinmu ba sannan inaso inyi maki nasiha akan abinda kikewa mom agaban kowa kisanifa itace ta dauki cikinki wata 9 tayi nakuda batasani ba ko zata rayu ko zata mutuba a haka har Allah ya sauketa lfy har ta haifeki bayan kin fito duniya tayita shayar dake idan kk yi kuka batada nutsuwa idan kkyi barci tayita gadinki idan bakida lfy…..
Aneesa ce tayi maza ta katseta dacewa dalla malama ya isa hk kece uwata ko kuwa ubana da zaki tasani a gaba kina tofamin yawun bakinki maza kifita a dakina kafin in…..
Aisha tace kafin ki kasheni ko dan iya abinda zaki iyamin kenan amma inaso kisani wallahi bazan fita ba har sai naji dalilanki nayin hakan
Dariya aneesa tafarayi kamar wacce ta zauce Aisha kuka tafarayi ta tsuguna a gaban ta tana kuka tana fadin sister dan Allah kifadamin abinda nayi maki ok idan bazaki fada min ba dan Allah ki daina yima mom rashin da a Aneesa tayi shiru ganin Aisha tana kuka hakan ya karya mata zuciya ta tallabo Aisha ta rungumeta itama tana kukan tace sister yi hkr kibar zubda hawayennan haka wallahi nima bansan dalilina nayin wayannan munanan abubuwa ba wani lokacin saidai in tsinci kaina cikin aikata hakan Aisha kiyi hkr ina kaunarki ki yafemin bazan kara ba