BABU SO HAUSA NOVEL

ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Saidai maganar ta tsayamai a makogoro jin kukar aneesa tana fadin subhanalillahi dama ashraf kai dan giya ne Allah ya tona asirinka bazan aureka ba ashraf na tsaneka……..

Zaiyi magana ta katse wayar tana kuka fitowa tayi ta dauki key din motarta a palo ganin mama tayi zata shigo rungume ta tayi tana kuka mama kuwa abin ya daure mata kai dan yanzu tafita tabarta cikin farin ciki meke faruwa ne

Saida Aneesa tayi mai isarta sannan mama tace zo mu zauna yar mama waya tabamin ke Aneesa tayi yake tace banso in wuce in barku ne mama ta karasa maganar tana kuka wanda itama mamar kuka tahau yi saidai tayi karfin hali tace yi hakuri Aneesa rabuwa ba mutuwa bane

Tayita yima aneesa nasiha hardai ta samu ta nutsu saidai tausayin kanta takeyi tana maimaitawa a ranta ashe dan giya zan aura dama Allah tsare ni

Aneesa tayi sallama dasu mama takama hanyar niger state Ashraf yakirata yanata bata hakuri yake kuma shaida mata shima yana bayanta da farko bata yarda ba saidai tana duba mirrow ta hango motarshi na binta a baya hakan yasata neman wuri ta tsaya shima tsayawar yayi bata fitoba sai shi yafito yazo yasameta ya tsuguna a wurin ga mutane ga motoci na giftasu yayita rokanta shareshi tayi dan ga alama nan giyar bata gama sakin jikinshi ba

Cemashi tayi ka koma kabarni nayi tafiyata kiran Adama ce ta shigo wayar ta dafe kai tayi ta dauka Adama na kuka take shaida mata cewar Allah yama kakanta rasuwa sannan ummanta tana asibiti Aneesa tace kiyi hakuri na kama hanyar niger ban samu damar zuwa na sallameki ba amma ganinan dawowa yanzu inshaaAllahu tunda dama banyi nisa ba yanzu nabaro kaduna

Ashraf ne yace lfy Aneesa tace kakar Adama ya rasu dan haka zan koma zaria yanzu kana iya tafiyarka daman saboda bakin cikinda ka cusamin ne yasa na kama hanya batareda na sallameta ba ka cuce ni Ashraf amma bakomai

Tada motar tayi tajuya shima haka sai binta yake abin har dariya yabata wanda batasan sanda tayita dariya ba ta furta mutum kamar kaska

Isarta zaria bata tsaya ko inaba sai kofar gidansu Adama shima Ashraf nan ya parker bayan tayima Adama ta’aziyya ne takira mama ta shaida mata cewar ta dawo ta fasa tafiyar sai next week murna mama tayi ta tambayeta dalili Aneesa ta gaya mata Aneesa bata bar gidan ba sai yamma shima Ashraf yana ganin fitowarta ya mike yamasu sallama yabi bayanta

Har tashiga gida shima ya shigo ta fito daga mota Ashraf yayi maza yazo ya tsaya yana bata hakuri da cewar sharrin shaidan ne

Aneesa tace bata bashi kuma…… ganin mama yasa ta sake fuska kamar bq ita ba bayan mama ta mata barka da dawowa ne tajuya gun Ashraf Ango Ango kaji dadinka Ango mai jiran gado smile yayi nan yasa hannu aljihu ya dibo makudai ya mikawa mama dan jin dadin yanda taketa wasashi

Itako Aneesa tacika tayi fam dan batason koda ganin Ashraf ne bayan mama tabar wurin Aneesa tawuce part dinta tana shiga ta rufe ba yanda Ashraf baiyi ba taki budewa sai faman cemashi takeyi ai da ace kana sona da baka batamin rai ba …….

Saida Aneesa tayi two days sannan tasallami Adama bayan ta biya bill din mamansu Adama dake hospital sannan ta budema umar yayan Adama shagon dinki lafiyayye takai ziyara ma marayu kamar yanda ta saba sannan ta ba Adama jari harna 500 thousand taba mahaifinta Awaisu takuma sayammasu gidan hayanda suke ciki ya zama nasu albarka kam tashashi ba iyaka addu’a ma hk

Bayan ta koma niger state ne a millonaire quarters da kwana biyu tana kwance sai taji ana kiranta taki amsawa cen sai taga hajja rahma tashigo tana fadin yata zo muje inata kiranki kinki amsamin Aneesa tace yi hkr hajiya ina zuwa fita taga hajja rahma tayi a cen waje kuma taji Aneesa da karfi kuma muryan hajja rahma ne sai Aneesa tace na am ina zuwa ai kuwa shikenan tun lokacin batasan inda take ba kuma koda tafito palo mom na magana da ita sai cema mom tayi ina zuwa ana kirana tayi ficewarta mom bata kawo komai a rai ba tayi smile ita ta dauka ma ko Ashraf ne dan tunda Aneesa ta dawo koda yaushe Ashraf na gidan

Mom tace kai nidai ayi a daura masu aure ko ma huta da wannan rashin kunyarsu ba itaba bashi ashraf din ba bini bini suna tare saidai ita batamasan suna fada da juna ba domin kuwa duk lokacinda aneesa tafito har su rabu bata amsa mai shikuwa baya damuwa musamman idan ya tuna saura sati biyu bikinsu

Aneesa takira drivernsu tace ya kaita zuba ba musu ya kaita ya ajiyeta a zuba tace ya wuce zata dawo idan ta kammala abinda yakaita ba musu ya juya don komawa gida nan Aneesa tashiga motar lokoja ra zauna

Abu kamar wasa yau kwana biyu ana neman Aneesa ba a ganta ba Ashraf na gadon Asubiti ba lfy tunda yaji lbrin bacewar Aneesa ya fadi koda ya farfado baida kalmarda tawuce innalillahi wainnailaihi raji’unnnn…………..

✍????by Leemat

Love U all ????????????
????????????????‍⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????‍⚖????????
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Wannan page din nakune yan SEE SEE Novels group Allah bar kauna kuna ❤ dina ina ji daku kamar yanda kuke ji dani musamman ma sis MaARYAM NURAINI YUSUF I ❤ U so much ????ana tare????

UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????

                     29

Koda Aneesa ta isa lokoja batasan kowa acen ba wuri ta samu ta zauna sai kalle kalle take abin nabata mamaki meya kawota nan mikewa tayi da niyyar zuwa garaji don tashiga motar da zai komar da ita Abuja amma ina ta kasa tamike yafi sau 6 kome take tunowa oho sai kuma ta Zauna

Dare nayi ta nufi wani hotel bayan taci abinci aka bata daki nan tabiya sannan tashiga ta kwanta gari na wayewa takuma fitowa ta koma inda ta zauna jiya itadai batasan me takeyi anan wurin ba saidai abinda tasani shine tanajin dadin zaman wurin

A kwana na 3 ne taji ana cewa da ita Aneesa ki tafi Okene kije cen kiyita zama har sai randa na umurceki ki bar wurin toh hajja kawai Aneesa ta iya cewa nan tamike a ranar tanemi mota dayake ba wani tazara ne dasu ba tasshiga mota sai okene aka sauketa wani abin mamaki batasan inda take samun kudi ba kuma babu wanda yake tambayarta ko daga ina tafito haka ta zauna a okene har tsawan sati 1

A ranarda tacika 1week and some days ranar ne aka kuma umurtarta data tafi Edo state tana mikewa sai ji tayi wani guy yace tafiya ne hajiya eh tace sannan tafada cikin mota ina zuwa Aneesa tace Edo state

Ashraf duk yabi ya rame ya susuce mom hankalinta a tashe itama duk tabi tayi baki sannan kullum cikin kuka take koda yaushe tana kan sallaya tana rokon Allah kare mata Aneesa a duk inda take

Alhaji Abbas kuwa yasa an bazu sai neman Aneesa aketa faman yi Ashraf kullum kuka kamar karamin yaro yana ji kamar shine silar fitarta daga gida tunda tace bata sonshi

Su hajja Rahma kuwa duniya tamata dadi domin kuwa abin nema ya samu saidai kullum tana gidan su Aneesa tayita habaici tana cewa amma duk wanda yamana haka bai kyauta ba kuma Allah bazai barshi ba tanayi tana kuka sai kace da gaske sannan idan tabar gidan sai tayita dariyar mugunta

Yau ana saura 3days da bikinsu Ashraf da Aneesa Alhaji Abbas yace baza a daura auren ba tunda ba asan inda Aneesar take ba

Ashraf sumewa yayi dayaji Dad yana neman tarwatsa rayuwarshi dakyar ya farfado nan yashiga yimasu kuka sosai yakeyi yana rokon kar a fasa daura aurensu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button