ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????
33
Inna tace yar Albarka dan sunar da take kiran aneesa dashi kenan aneesa ta dago tana kallon inna
Inna tace wai meke damunki ne eh?
Aneesa kamar bazata amsa mata ba saidai tace bkm inna sannan tamike dashige daki inna ta biyota sai gani tayi aneesar tana kuka hankalin inna in yayi dubu toh ya tashi
Rarrashinta tafarayi amma ina kamar kara zugata takeyi sosai aneesa ke kuka cen kuma sai tayi tsit kamar ba itaba
Ta dago idanuwanta dasukayi jaa jir ta kalli inna taga inna na zubda kwalla nan take tambayar inna ko lfy me yasa take kwalla kuma waya shigo da ita dakin
Mamaki tambayar taba inna saidai ta daure tace yar Albarka meke damunki ne kwata2 kin canza kamar bake ba
Mikewa Aneesa tayi tabar dakin dan batajin dadin tambayar da inna ke mata
Koda ta fita wani shago taje ta zauna abinta ta rasa meke mata dadi a rayuwarta
Tunani tashiga yi cen sai tamike ta nufi dakin inna ganinta tayi zaune inda tabarta
Sai taji ba dadi zuwa tayi ta tsuguna gabar inna tace inna natuba ki yafemin
Rungumota innar tayi tace bakimin komai ba yar Albarka
Aneesa tace inna inaso inyi tafiya inna taji gabanta ya fadi addu’a tashiga karantowa kafin tace ina kika sani?
Ina zaki?
Kodai kin tuno da usilinki ne?
Aneesa tace usuli kuma inna nidai kawai tafiya zanyi amma zan dawo in Allah yaso ya yarda
Inna tace toh ina zaki?
Aneesa tace zan shiga warri ko ughelli ne
Inna tace kin taba zuwa cen dinne?
Aneesa tace aa amma ai Aunty Atika acen take
Baki inna tasake jin aneesa ta ambaci sunar Atika toh a ina kk san atikar?
Ina anan kika santa ranarda takawo min ziyara gaskiya ban yarda kije wurinta ba
Aneesa tafara yin kuka tana bubbuga kafafu kamar wata karamar yarinya tana fadin inna idan baki barni naje gunta ba zan shiga duniya in barki kuma bazaki kara ganina ba
Jin hakan daga bakin Aneesa kuma tasan karamin aikinta ne yasa inna tace toh naji zakije kinji yar lelen innarta
Smile aneesa tayi ta goge hawayen fuskarta sannan tace inna toh gobe zanje koh
Jin aneesa ta ambaci gobe ne yasa inna jin badadi domin kuwa tasaba da aneesa akusa da ita koda yaushe sannan tanason aneesa anyaa zata iya ba aneesa a tare da ita……
A haka dai ranar inna ta wuni sam jikinta ba ko kwari banda aneesa da sai zumudi take tanaji kamar gari bazai waye mata ba
Washe gari da karfe 9am aneesa takama hanyar ughelli daga Asaba domin kuwa inna ta hadata da wani makwabcinsu mai zuwa sayayya a ughelli din
Su aneesa sun iso ughelli lafiya a otowodo park aka saukesu na Dominion park
Mashin suka tsare mutumin yace hausa quarters bada jimawa ba suka iso hausa quarters da isarsu sai mutumin yakira hajiya Atika ya sanar da ita cewar sun iso farin ciki gun hajiya Atika baya misaltuwa domin kuwa shekarunta 20 da aure amma Allah bai bata haihuwa ba tun randa tahada ido da Aneesa sai taji ta kwanta mata arai
Hakanne yasa da Aneesa taje rakata sai tayita zugata akan tazo ta zauna da ita koda na sati daya ne sannan ta sanar mawa Aneesa cewar Allah bai taba bata haihuwa ba don haka ta taimaketa tazo yimata kwana biyu amma karta gaya mawa yar uwarta cewar itace tace tazo kawai dai tayi ne kamar taji kewarta
Hakan kuwa akayi
Kiran number mijinta tayi ta sanar dashi ai kuwa cemata yayi toh bari insa yaro yaje ya taho da ita
Duk da ba hakan taso ba amma koba komai yanzu zata samu abokiyar hira
Ko minti 20 ba ayi ba saiga su aneesa nan sun iso gate suka buga aka bude masu suka shiga ai dagudu hajiya Atika tayi kan aneesa
Tana fadin lale lale yar innarta rungume aneesa tayi sosai tanajinta a ranta
Har palo suka shiga a haka ta zaunar da aneesa sannan tace ya hanya?
Lfy aneesa ta amsa
Aneesa tace Aunty dan Allah ki kira inna ki sanar da ita cewar mun iso dan hankalinta ya kwanta smile hajiya Atika tayi tace toh yar inna nan takira number inna ai kuwa bugu 1 inna ta daga kamar dama tana jiraye da kiran
Ko gaisawa basuyi ba inna ta tambayeta ko aneesar ta ta iso dariya tayi kafin ta amsa mata da eh sannan suka gaisa mikawa aneesa wayar tayi suka gaisa da inna
Hajiya Atika takai aneesa wani daki tace ki saki jikinki ki dauka nan gidanku ne kinji toh kawai aneesa tace sannan tace nagode Aunty
Hajiya Atika tace kibar kirana Aunty ki kirani da Ummana
Aneesa tace ummana wani smile hajiya atika ta sakar mata hawaye zafafa na bin kuncinta
Aneesa tasa hannu tana share matasu sannan tace Ummana kibar zubda hawaye pls
Kiss din goshinta hajiya atika tayi sannan tace maza kishiga kiyi wanka kifito sannan kizo kici abinci sai ki kwanta ki huta
Fita tayi aneesa kuwa jikinta ne ya mutu tace gaskiya ummana inasonki duk da ban taba zama dake ba amma inajinki a raina
Mikewa tayi tashiga bathroom tayi wanka
Tafito taje ta rusuna ta gaida Hajiya atika nan suka zauna suna cin abinci tare
Yau watannin aneesa 3 a gidan hajiya atika rayuwa mai dadi takeyi itada sabuwar ummanta Alhaji isma’ila shima yanajin dadin zaman aneesa a gidansu dan tana dibe masu kewa sosai
Gata da ladabi da biyayya hakanne yasa yakejin sonta sosai kamar diyar cikinsa
Inna kuwa kowani sati 2 saitazo ganin aneesa tunda sunki yarda ta dauketa ganin rashin basu taba haihuwa bane yasa inna ta hakura tabar masu aneesar amma badan taso ba
Aneesa kam samari da dama sunata kai mata hari amma sam bata son su hasalima ko kulasu batayi
Yau watan aneesa 4 da bata amma Ashraf yabi ya lalace yayi baki wulk ya rame kuma bai fiya yin magana ba Abokananshi sunso yakoma shaye2 amma sam yaki amincewa da so daya idan suka zo masa da zancen ma da fada suke rabuwa domin yadau alkawarin babushi babu giya tunda Aneesarshi bataso kuma yadau alkawarin bazai taba koma mata ba har karshen rayuwarshi
Mama kuwa koda yaushe tana kan sallaya tana rokan Allah dawo mata da yar baba lfy
Mom ma haka Aisha tabi ta rame tsabar tunani sannan ta daina fita haka baba da dad kullum addu’a suke Abdul basit kuwa kamar wani zaucacce shida ashraf sai surika kiran sunar Aneesa suna dariya suna kuka
Ganin abu yakici yaki cinyewa ne yasa baba mai gadi yace ma dad Alhaji a gaskiya yanzu yakamata mudau kwkwaran mataki akan wannan al amarin
Ni yau zan shiga cen kauyen shimi nan zanje inyita kiran Aneesa har tsawan sati daya inshaa Allahu zata dawo
Dad yace hop dai bai sabama Allah bako baba yadanyi shiru kafin cen yace toh Alhaji ya za ayi yau wata hudu kenan fa ba ita ba labarinta
Dad yakira mom dasu ashraf dasuketa dariya suna fadin wayansu abubuwanda aneesar takeyi lokacin suna tare jin an ambaci dawowar aneesa yasa sukayi tsit sai kuka Ashraf yace da gaske dad
Mom tace eh Ashraf tana kwalla dan tana tausayinsu
Shiko dad idonshi duk sunyi jajir
Sallamar hajja rahma ce ta katse su da kusan kullum tana gidan wai ita a dole ta damu da batar aneesar
Yau kam Ashraf ne yayo kanta yana fadin ke hajja rahma kike kome nifa ban yarda dakeba
Kinga tun wuri kifitomin da matata kafin baba ya kirawota tadawo dan wallahi idan har kika bari tadawo tace kece kika …….
Kaiiiiii dalla kajimin yaro mara kunya har kai ka kaini son aneesar ne kaida baka damu da batarta ba kaida dazaran kasami wata zaka mance da ita kaida kake mata soyayyar karya keeeeee…. hajja Ashraf ya shaketa idanunshi sun kada sai huci yake kamar zaki yace wallahi tallahi hajja ki fadi duk abinda kikaga dama amma karki sake ki bude wannan kazamin bakinnaki kice soyayyar karya nakema gimbiyata dan wallahi zan iya kashe duk wanda ya karyata soyayyata da gimbiya