ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Su babane sukazo suna rirrikeshi itako hajja rahma banda tari babu abinda takeyi
Dakyar aka raba hannunshi da wuyarta kuka ashraf yakeyi yana fadin wallahi ni ban yarda da wannan matar ba jikina yana bani tanada masaniya akan batan gimbiyata mom kawarki bata kaunarki
Abdul basit tashi ku wuce part dinka
Tashiwa sukayi jiki ba kwari har sunkai bakin kofa sai sukaji hajja rahma na fadin baba mai gadi gaskiya wannan shawaran batayiba ai wannan sabawa Allah ne gaskiya hajja fati karku yarda kawai muci gaba da rokon Allah ya bayyanar da ita aduk inda take ya tsareta
Ashraf ya juyo da sauri ya isa gunda take kafin su ankara ai har yahauta da duka yanayi yana fadin toh karya kikeyi makira munafuka sai an kirawota ko kinaso ko bakyaso itako sai faman ihu takeyi su dad kuwa kokari sukeyi su kwace a hannun ashraf amma ina sub kasa dan haka dad yakira sucurities 6 suka shigo suma dakyar suka kwace hajja rahma da tasha bugu hannun ashraf duk fuskarta ta chanza kala Ashraf yace kadanma kika fara gani makira marar imani kawai munafuka sai na zame maki annoba a rayuwarki iddan baki dawomin da farin cikina ba kema saina hanaki farin cikinki
Kuma sai baba yakira Aneesa ko kinaso ko bakyaso hajja rahma kam ba bakin amsa ma ashraf dan yanzu kam tsoronshi takeyi irin wannan duka haka wanda ko ubanta bai taba yimata irinshi ba amma wani karamin yaro wanda inda haihuwa tayi da ta haifi irinshi ….
Dad ya tashi yaje gaban ashraf da securities suke rike dashi amma sai kokarin kwatan kanshi yake yace Ashraf son calm down pls ….
Ganin yanda idon dad suka rine ne yasa ashraf yin shiru nan yafara yin kuka yana fadin wallahi dad ban yarda da wannan matar ba
Dad ya juya yana kallon hajja rahma kafin yace hajja rahma yi hakuri ki koma gidanki pls
Dan yanzu ashraf baya son ganinki
Mikewa tayi mom ta rakata har tadan girtashi ai jin gabanshi yayi mummunar faduwane yasa yamike yayo kanta wani wawan kulli yamata ai kuwa sai tazube a wurin sumamma
Salati suka hauyi shiko ashraf ko ajikinshi saima kokarin take mata ruwan ciki yakeyi
Rikeshi akayi ita kuwa kinkimarta akayi sai hospital
Yau Aneesa ta tashi da matsananciyar ciwon kai sannan tarasa meke mata dadi a rayuwarta
Ganin fuskar wani takeyi sannan kuma tana yawan ganin shi a mafarkinta saidai batasan koshi wayeba amma koma wanene shi ina kaunarsa ta furta
Gizo yake mata tana zaune sai taganshi yazo yana kiranta da gimbiyarsa sai kuma taga ya bace
Yau dayazo mata sai ta tambayeshi sunanshi ai kuwa sai yace mata sunanshi ASHRAF kuma shi mijinta ne ………….
Toh fa Aneesa tashiga damuwa sai tunani takeyi wai Ashraf kuma mijina ne toh yaushe aka daura mana aure??????
Toh fa masoya Aneesa fa kamar ta fara dawowa hayyacinta amma toh ya za ai tasamu amsar wannan tambayar?
Hmmm……. tabbas akwai sauran rina a kaba…….
Kubiyoni dan jin yanda zata kasance
✍????by Leemat????????????
I love U all❤❤❤
????????????????⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????⚖????????
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
Wannan page din nakune yan GROUP din UMMAN AMIR HAUSA NOVELs nagode da soyayyarku hadida addu’oinku gareni Allah saka da alkhairi ameen nima ina yinku ????❤????????
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????
34
Koda aka isa da hajja rahma hospital taimakon gaggawa aka bata dakyar ta farfado a zabure tana fadin kayi hakuri banda masaniya akan batar aneesa
Nurses ne suka riketa sannan dr yamata allurar barci ba a wani dau lokaci mai tsawo ba tayi barci
Itako Aneesa baiwar Allah tana cen duk hankalinta a tashe hajiya Atika ce tafito tasameta a wannan yanayin hankalinta yayi mugun tashi taje tace daughter na meke damunki?
Waya tabamin yar lele ta
Aneesa tace ummana yau natashi ne da matsanancin ciwon kai sannan kuma wani yana min gizo yana zuwa inda nake washi sunansa……
Kome ta tuno kuma oho sai tayi shiru Hajiya Atika taji kirjinta yabada DAM…..
Amma sai ta daure tace yar leleta kiyita addu’a kinji toh kawai Aneesa tace sannan ta kalli hajiya atikar da itama itan take ta kallo sai tace ummata wai ni wacece?
Kuma daga ina nake?
Kuma waye shi?
Hajiya Atika tafara hawaye tana tausayin Aneesa kuka tafara yi mai sauti tama kasa furta koda uffan ne
Ganin hakan yasa Aneesa tace yi hkr ummata ni banason ganin hawayenki indai baso kikeyi nima nayi kukan ba
Jin hakan yasa tafara share hawayenta dan tasan karamin aikin Aneesa ne zata iya kuma idan tafara batajin yi shiru karshe ma takare da rashin lfy
Smile tayi tace yar leleta zo muje muci abinci ba musu suka wuce dinning dan cin abincin
Da yamma Alhaji yakira Aneesa yana mata nasiha akan hakuri da karbar kaddara a rayuwa sosai nasiharshi ta shigi Aneesa sosai kuma ta sosa mata rai
Yana kan yimata nasihar ne sukaji Sallamar Abu sa’ad suka amsa yashigo da fara’arsa ya nemi wuri ya zauna
Hira suka hauyi shida hajiya Atikar da alhaji Abu sa’ad kani ne awurin hajiya Atika yan jos ne amma aiki ne ya kaishi delta state
Hirarsu suketayi amma hankalinshi nakan Aneesa da taketa faman danne dannen wayarta da Alhaji ya sayammata
Alhaji kuwa yamike yayi ciki abinshi yabarsu anan zaune bayan yagama yima Aneesa nasiha tayimai godiya tace Abbana nagode kuma inshaa Allahu zaku sameni mai biyayya mai bin maganar iyayenta
Allah maki Albarka cewar alhajin sannan yamike yana fadin toh kai Abu sa’ad kodai za ayi yar gida gida ce
Dan nalura dakai kwanarnan kullum cikin ziyara kake
Smile yayi yana sosa keya sannan yace habaa….. mana ya Alhaj ya zakamin haka smile shima alhajin yayi yashige abinshi
Ganin hankalin kaninta baya kanta yasa tace toh bari nima nashige ciki dan naga alamar gaskiya a maganar Alhaji na
Smile yayi amma bai amsa mata ba saida takusan shigewa sai yace kumafa gaskiya Aunty danafi kowa farin cikin faruwar haka jin haka yasa hajiya Atika dawowa tazo ta zauna tana smile ta kalli dan kaninta tace da gaske dan kanina
Ganin suna nemar su dameta ne yasa tamike batace dasu kala ba tayi hanyar dakinta hajiya Atika ce tace ina zakije kuma bayan hira mukeyi
Aneesa tace umma hira kukeyi keda uncle Sa’ad amma banda ni ai
Toh dawo ki zauna ayi dake cewar Abu Sa’ad sannan ya kashe mata ido
Dawowa tayi ta zauna cikin zumudi yace Aunty kidan bani aronta mana ta rakani nan
Kallonshi yayar tashi tayi sannan tace ok ooo gata nan nabaka wuka na baka nama sai kasan yanda zaka yanka ta
Aneesa kam smile tayi tace uncle sayan ice cream zamu? Eh yace mata
Tashiwa tayi da wuri tayi hanyar waje tana fadin sai kafito uncle
Mikewa yayi ya kalli yarshi da itama shidin take kallo yanda yake zumudi sai tace toh dai kar ku dade amana amana amana
Dariya yayi yace haba Aunty kema ai kin sanni bana neme2 mata hasalima diyarkice yarinya ta farko data kwantamin arai itace kadai ta sacemin zuciyata
Ganin zai batama Aneesa lokaci yasashi fadin Auntyna kitayani da addu’a Allah sa diyarki ta aminta da soyayya ta ameen ta amsa tana kwalla dan tausayin dan marayan Allah takeji tun haihuwarshi ne Allah ya dauki ran mahaifiyarsu wanda jin hakan ne yasa mahaifinsu yanke jiki ya fadi baifi kwana biyu a asibiti ba shima yace ga garinku nan hajiya atika ce tayita rainon dan kaninnata har ya girma tunda yataso bata tabajin yana zancen wata ya mace ba dan ko kula mata ma bayayi