BABU SO HAUSA NOVEL

ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Amma abin mamaki saigashi soyayyar Aneesa ta mamayeshi har vaya iya boyewa

Sharewa tayi lokacinda yamatso kusa da ita yace Aunty lfy?

Cemashi tayi bakomai jeka Allah daidaita tsakaninku

Ameen yace jiki ba kwari yafita binshi tayi a baya dan tasanshi tunda yagan hawayenta toh hankalinshi bazai taba kwanciya ba

Abu sa’ad takira shi juyowa yayi smile ta sakar mashi sannan tace karka damu da kwallarda nakeyi na farin ciki ne

Domin kuwa ban taba ganin kanina cikin farin ciki irin ta yau ba kuma ban tabajin kanina na zancen mace ba sai yau shiyasa tsabar farin ciki nake kwalla

Smile yayi yace Aunty kenan kibar zugani smile tayi tace kuje sai kun dawo

Jan motar yayi suka fice itama komawa cikin gidar tayi tana addu’ar Allah sa Aneesa ta amince da kaninta

Basu tsaya a ko inaba sai E.J ice cream yasiyammata da su chocolate da biscuits da dai sauran kayan maku lashe

Har sun kama hanyar komawa gida sai kuma ya juya bai tsaya a ko inaba sai wakiz nan yayi parkin kallonshi Aneesa tayi saidai batace komai ba shima kallonnata yakeyi ya bude baki yace Aneesa ni marayan Allah ne banda uwa banda uba

Ki tausayamin Aneesa ki tausayamin ki ceci rayuwata ki taimakeni kema sai Allah ya taimakeki

Aneesa tace toh ni me nakedashi da zan taimakeka kuma ai naga kamar kafisu Umma kudi me kakeso a rayuwarka karasa eh uncle

Runtse ido yayi nadan wasu lokuta kafin yabudesu sun kada sunyi jajir yace Aneesa bazaki gane bane Aneesa mutuwa zanyi idan narasata

Bazan iya rayuwa batare da itaba

Itace ruhina itace jinin jikina

Aneesa tace ohhhhh so Uncle kana nufin akan mace ne kaketa sumbatu haka wacece ita

Yar gidan wanene?

Kuma waye mahaifinta da bazata so uncle dina ba gaye ga kyau ga naira

Smile yayi sannan yace kenan kina da tabbacin cewar babu macenda zata kini ko?

Eh mana Aneesa ta amsa sannan takara dacewa uncle Allah babu macenda ta isa takika gaka da hankali ga ladabi da biyayya gaka dan gaye

Dariya yahauyi ba kakkautawa saida yayi mai isarshi sannan yace Sweetheart koda kece zaki aminta da soyayyata?

Shiru tayi sai wasa take famanyi da yatsunta ganin batada niyyar amsa mashi ne yasa yace bakowa bace take nemar zautar daniba sai ke Aneesa………

✍????by Leemat

I love u all????????????
????????????????‍⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????‍⚖????????
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????

                  35

Kirjin aneesa ne yabada dam……

Tace uncle wai kana nufin…… katseta yayi dacewar eh ina nufin ke Aneesa

Ki taimakeni ki yarda dani ina matukar kaunarki ki aminta kizama uwar yayana

Yakarishe maganar da hawaye shame2 a fuskarshi rokon Aneesa yake yana gaya mata yanda yakeji game da ita

Aneesa kam cemashi tayi yakaita gida ba musu ya tayar da motar saidai jikinshi rawa yake mashi dan fargaban ko wane amsa aneesa zata bashi oho

Kasa jan motar yayi ganin haka yasa aneesa tace uncle bani inja mu fitowa yayi sai faman hawaye yakeyi yazagayo itama ta zagaya tana mamakin abinda kunnuwanta suka jiyo mata

Jan motar tayi kamar zata tashi sama shiko ko ajikinshi dan yanda yakeji kirjinshi kemashi zafi ko mutuwa ne zai iyayi amma dai bari yaji amsarta tukuna wani ajiyan zucciya yayi wanda hakan yasa Aneesa taka burki da karfi

Kallonshi tayi tace uncle dan girman Allah kabar zubda hawayennan kamar wanda aka aikoma da sakon mutuwa habaa kaifa namiji ne saboda me zaka sama kanka damuwa akan wata karamar yarinyarda kafi karfinta tako ina

Ji yadda kabi ka canza dan kankanen lokaci saikace ba uncle jaruminda nasani ba

Kalon dan karamin bakinta yaketa faman yi sannan yace toh Aneesa idan baso kikeyi kirasani ba idan baso kikeyi na hadiye zuciya namutu ba Dan Allah ki amsamin da kina sona kema

Aneesa tace wai uncle da gaske kake ni kake so?

Kallonta yayi sannan yace eh Aneesa ke nakeso kuma sona hakika so na gaskiya so na tsakani da Allah

Ina kaunarki fiyeda yanda kike tunani Aneesa zan……

Katseshi tayi dan ganin yanda yake neman kara daburce mata tace Uncle kayi hkr mu isa gida zan baka amsa amma kafin nan inaso kabar zubda hawayenka

Sharesu yayi sannan tace yauwa uncle kana bani lbrin yar budurwarnan dataso mallakarka by all mrans

Smile yayi yace Aneesa kenan wato dai so kikeyi in bar kwalla toh na daina itama smile din tayi tareda tada motar tajata sukaci gaba da hirarsu cikin annushuwa

Koda suka isa gida aneesa tafito tamikamai car keys dinshi tace tnks 4 d shopping gud nyt har tafara tafiya sai taji yace haba mana Aneesa yanzu idan kika wuce baki bani amsaba kinma zuciyata adalci kenan???

Juyowa tayi tace ban ganeba me kk nufi

Smile yayi yatako har zuwa inda take yace I LOVE U Aneesa

U r my heartbeat…….

Aneesa smile ta sakar masa sannan tace I LOVE U MORE uncle

Tana gama fadin haka tayi cikin gida dagudu

Shiko smile yayi sannan ya fadi kasa yayi sujjada yana godewa Allah dayasa Aneesa ta amince da soyayyarshi

Part dinshi yawuce bai tsaya bata lokaci ba yakira Antynahi yamata albishir godiya tayi ga Allah tanayi tana kwalla Alhaji yayita yimata nasiha sannan yakira Abu Sa’ad yace masa yanason ganinsu shida Aneesa gobe da safe idan Allah ya kaimu

Haka yakira aneesa itama ya sanar mata gabantane ya fadi dan haka bayi tafada bayan ta watsa ruwa tayi alwala tafito tahau yin nafil fili

Shima Abu Sa’ad abinda yayitayi kenan anan barci yayi awon gaba dasu akan sallaya

Jin ana tabata ne yasa ta farka da wuri sai ganin Ashraf tayi yana smile yace haba gimbiyata yanzu da aurena akanki kike kula wani har kika aminta da soyayyarshi

Maza ki janye gimbiyata kuma …… sai yafashe da matsanaccin kuka ba kakkautawa

Aneesa tace wai malam kai wani irin mutum ne ko aljani ma zance toh wai shin ma a ina kasanni kuma idan da gaske kakeyi ni matarka ce kamar yanda kake ikrari toh ina yaranmu kuma meya hanaka zuwa ka daukeni saidai kayitamin gizo

Kaga mallam na rokeka dan girman Allah kabar takuramin rayuwata idan har da gaske kakeyi kai mijina ne toh kazo Delta ka daukeni mukoma gida

Komawa tayi abinta ta kwanta nan barci yayi awon gaba da ita kuma

Washe gari gaba daya suka hadu a palon Alhaji Aneesa kam wani irin kunyar Uncle dinta takeji wanda batasan tanaji ba sai yanzu

Shiko kafeta da ido yayi yanajinta acikin jikinshi

Alhaji yayi addu’a kafin ya fara magana Aneesa yakira sunanta

Ta amsa kanta a kasa batareda ta dago ba yace jiya kawunki yakira ummanki yake sanar da ita cewar kun daidaita tsakaninku hakane?

Shin gaskiyace?

Karkiji tsoro kuma ba fargaba kigayamin gaskiya kina sonsa ko bakya sonsa

Idan kikace bakya sonsa nayi maki alkawari bazan yimaki tilas ba kuma ba wanda ya isa yama diyata auren dole kinji koh

Smile tayi bata amsa ba Alhaji yakuma cewa kina sonsa rufe idonta tayi tace eh Abbana

Wani dadi Abu Sa’ad yayi yace bana gaya makuba tana sona itama saidai bata kaini ba sannan dan Allah alhaji asaka ranar bikinmu kar yawuce sati daya dan ina bukatar matata a………….

Hajiya Atika ce ta harareshi sannan tace kai amma bakada kunya wai Umar yaushe kafara magana ne

Yaushe kazama haka

Yaushe ka…….

Alhaji yace ki rabu dashi dan Allah ai da gaskiyarshi dan haka karkasamu damuwa inshaa Allahu za ai maka yanda kk so

Aneesa kam magan ganun shi kunya suka kara bata a zuciyarta tace lallai uncle bashida kunya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button