ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Oh daman sunanshi kenan na usuli Umar woww…… nice name toh ko meyasa ake kiranshi da Abu sa’ad oho
Alhaji ya rufe taro da addu’a bayan yamasu nasiha sosai sannan ya tambayi aneesa ko yamata a daura aurensu nanda next week
Aneesa cemashi tayi Abbana duk yanda ka zartar da hukunci akaina daidai ne karka damu zan kasance mai ladabi da biyayya ga iyayenta
Wani kukan farin ciki ne Hajiya Atika tafarayi tana sama Aneesa albarka
Bayan alhaji yaja matarshi sun shige ciki sai yarage Aneesa da uncle dinta
Matsowa yayi kusa da ita yace next week ki shirya dan zaki tashi daga miss Aneesa Isma’l zuwa ga mrs Umar
Mikewa tayi da gudu tashige ciki
Da smile yabita
da yammacin ranar wani uncle dinsu Hajiya Atika yazo shida abikinshi liman
Kudin gaisuwa duka biyu suka bayar da dukiyar aure hadeda sadaki naira dubu dari biyar
Kiran wayar aneesa uncle dinta yayi yace kisameni a waje
Dan kwalliya tayi ta yafa hijabinta tafito ganinshi tayi zaune a wajanda aka tanada dan shakatawa
Zuwa tayi da sallamarta bayan ya amsa yace zauna mana
Zaunawa tayi nan yake cemata ai yaturo da sadakinta ko kuma har ansa masu ranar aurensu nan da sati biyu
Gabantane yafadi hira sukasha saidai takasa sakewa dashi tarasa dalili
Hajiya atika kam visa aka shirya masu suka tafi india don shirye shiryen biki kwanansu 4 suka dawo
Wata kawarta takira yar maiduguri tace hajiya kizo ki gyaramin diyata yanda mijinta zai gigice
Hira sukasha sosai daga karshe takatse wayar su inna kuwa ana cen baki yaki ruhuwa dan murna
Koda Alhaji yaba Aneesa sadakin kin karba tayi tace ita batada bukatar sa yayi yanda yaga ya dace da kudin amma fir Alhaji yaki yace sai dai ta karba
Gyara kam aneesa tashashi gun maman maiduguri
Yau yarage saura kwana biyu a daura auren Aneesa da Umar
Jin jikinta takeyi kamar ba tata ba sannan ga ciwon kai dake damunta sai ganin hoton mutane take tayi saidai bata tunanin ta taba ganinsu a rayuwarta sannan kuma har yanzu Ashraf bai bar takura mata ba
Soyayya mai karfi ne yashiga tsakanin Abu Sa’ad da Aneesa
Ina labarin hajja rahma
Hajja rahma saida tayi sati 1 tana jinya kafin aka sallamota
Yayan Aneesa kam ya yarda da maganar Ashraf kan cewar hajja rahma tasan da batan Aneesa saidai baisan ta ina zai fara bincikenshi ba cen wata dabara ta fado masa
Dan haka zuwa gudan hajja rahma yayi bayan sun gaisa har sun fara hura sai yace hajiya nasani kece tsilar batar Aneesa saidai ina mai tabbatar maki da cewar kin burgeni sosai dan gaba daya su dad basa bani kulawa kamar yanda suke bata kinkoga ai yanzu da bata nan naji dadi sosai
Hajja rahma da kwakwalwar kifi ne gareta sai washe hakora tayi tace laaaa……. wai da gaske kakeyi Abdul
Eh yace mata nan ta kwashe komai ta gaya mashi ji yayi kamar ya kasheta amma sai ya daure yayi controlling kanshi sannan yace kingane ko hajja pls karki dawo da ita ki barta acen tayita shan wuya
Dadi taji sosai nan yamata sallama yakoma gida yana kuka mai cin rai yana tsinema hajja rahma nan ya sanar da Ashraf yanda sukayi da hajja rahma Ashraf sarkin zuciya cewa yayi zaije ya kasheta
Hakuri Abdul basit yayita bashi da kyar ya hakura sannan yace da sassafe gobe zai kama hanyar delta din
Kiran hajja rahma ce tashigo wayar …………
✍????by Leemat
Love u all????????????
????????????????⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????⚖????????
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELs❤
36
Kiran hajja rahma ce ta shigo wayar Abdul basit kallon juna sukayi shida Ashraf da ji yakeyi kamar ya daga wayar ya mata rashim M amma ina ba dama
Abdul basit ya daga wayar kafin yayi magana sai jin muryar hajja rahma yayi tana fadin Abdul ina kk ne kazo kasameni a gidana akwai magana akan shegiyar yarinyar nan ne da kuma dan iskan mijinta wanda yamin rashin mutunci na shirya salwantar da rayuwarsu gabaki daya ko ya kagani
Dariya yayi amma idonshi cike suke fal da hawayen bakin ciki yace kin gaskiya kam ya kamata amma baki tunanin idan mukaje inda za a maki aikin tare zaifi
Wawiyar tace toh ai daman shiyasa nace kasameni a gidana saboda mu tattauna irin illar da za ayi ma shegun
Hawayenda yake kokarin rikewa ne suka fara zuba muryarshi tafara yin rawa ganin hajja rahma zata iya dago rauninshi ne yasa ya katse wayar hannunshi sai faman rawa yake tayi
Kuka yakeyi sosai kamar wani karamin yaro shiko Ashraf dayariga yagama jin komai sai ranshi yakuma baci
Yace big bro saida nace maka kabarni in fito fili in yima matar nan R M amma kaki yarda toh yanzu kaji bata saduda ba ma planning takeyi akan yanda zata salwantar da rayuwarmu nida Aneesa
Kai amma matar nan wawiya ce ta karshe ma inba rashin ilmi da shashanci ba taya za ayi ace kana wa ga Aneesa uwa daya uba daya amma tarasa wanda zata gayama sirrinta saikai
Koda yake kamuwar Allah ne amma bkm big bro kayi hakuri inshaa Alahu zan dawo da Aneesa matata farin cikina
Abdul basit yace bro bazaka gane bane wannan matar fa aminiyar mom ce kusan komai na mom ta sani
Toh me mom tamata dayasa tamata haka
Wannan wane irin kiyayya ce hk
Me Aneesa tamata yarinyarda batada lokacin kowa ma
Ba ruwanta yarinyarda ta dauketa tamkar mahaifiyarta
Ashraf ne yaji wani irin bakin ciki da tsantsan tsanar hajja rahma a zuciyarshi nan yace karka damu bro inshaa Allahu sharrinda tayi shi zai koma kanta
Abdul yace tabbas kuwa dayake dare ya tsala lokacin haka suka cigaba da hirarsu cen suka tabo labarin aneesa suketayi suna dariya
A haka sukayi barci kowannensu da abinda yake sakawa a zuciyarshi gameda hajja rahma
Washe gari Ashraf ya kama hanyar Delta state amma a gida kam cemasu yayi kiran gaggawa akamai
Waishin wani abokinshi ba lafiya kuma baida kowa a nigeria sai shi tausayinshi su mom sukaji har sukace idan yaje yaga da sauki kawai ya daukoshi ya dawo dashi azo ayimai jinya a nan
Toh kawai yace sannan ya kama hanya addu’a sukamai na Allah tsare niko nace ameen
Motarshi ya dauka kirar Crosstour 4wd
Shiko Abdul gidan hajja rahma yanufa dan jin next plans dinta akan Aneesa da Ashraf
Koda ya isa bai jima ba ta kwashi komai ta gaya mai cemata yayi toh me muke jira
Dauko gyale tayi suka kama hanyar kauyen Omayvor sundau kusan 1 hour kafin suka isa kauyen wanda bazaka san da dan Adam acikinta ba Abdul kam ya jinjinawa rashin imani irinta hajja rahma sannan ya tausayamawa mijinta lallai kam hajja rqhma kinyi asara babba a rayuwarki
A fili kuwa sai ya furta gaskiya kin burgeni wannan wuri haka ai dole magani tayi aiki
Dariya tayi tace shiyasa na yarda dakai saboda kanka na dauka wuta da wuri
Kwabe takalminta tayi tashiga gidan ta baya sannan tace shima yayi yanda tayi shiko Abdul cemata yayi Allah bazan cire takalmina ba kuma bazan iya shiga wuri da baya ba
Wani murya sukaji yana fadin toh bakomai bako kashigo ta gaba tunda yaune ranarka ta farko duna baleri ya maka uzuri hahahahahahahah………….
Shiga yayi da sallama wani irin kuwa akayi wanda saida yaso tsoratar da Abdul amma dayake namijin gaske ne sai ya dake abinshi kamar ma baisan dashi ake ba
Cewa akayi ba a sallama anan
Itako hajja rahma hakuri tabasu tace ai baisani bane
Kallon wurin Abdul yafara yi yana yatsine fuska jin wani irin amai daya tasomai sakamakon wani dabur ceccen halitta daya gani a yashe a kasa duk yauki yakeyi kamar wanda ya watsa karkashi a jiki