ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL
Mutumin ne yace kai yaro karka fara yana maganar wasu yawu na fitowa daga bakinshi ai kuwa dagudu Abdul yafito daga gidan tsugunawa yayi yata kwarara amai kamar zai amayo hanjin cikinshi hajja rahma ce tafito taje taciro gorar ruwa tamiko mai sannan tace idan bazaka iya ba toh kayi zamanka a mota ni zan koma ciki duk yanda mukayi dashi zan sanar dakai ta juya da niyyar komawa ciki
Abdul basit yace hajja dan Allah karki kuma yimasu komai kawai dai ki tambayeshi ina Aneesa take a delta kiji ko zai sanar damu in yaso ni zansa yan iska suje sumata tsiya tsiya amma karki kuma yimata wani abu
Shikuma Ashraf nqsan yanda zanyi dashi kibarni dashi
Smile tayi tace ok toh baji ai kaima sanin kanka ne idan ban yarda dakai ba bazan bari kasan sirri na ba
Kuma bazan kawoka nan ba
Smile yayi yace kumafa haka ne hajja
Shigewa tayi tabarshi a wurin shiko Al Qur’ani mai girma ta dauko ya fara tilawa da muryarshi mai dadi
Koda hajja rahma takomo ciki boka yace da ita meyasa kika taho dashi
Hkr tabashi nan ta tambayeshi inda aneesa take dariya yayi ya gaya mata inda take sannan yace mun kasa sanin ko tana cikin kunci ne ko cikin farin ciki saboda yarinyar taurin kai ne da ita sannan kuma a tsarkake take tana yawan yin ibada ba kamar kiba da babu ruwanki da yin sallah ba keda babu abinda kika sani sai hassada
Kai hajja rahma karshenki zaiyi kyau kuwa???????
Smile tayi tace ai boka kafin karshennawa tazo ai zan tuba kuma na tabbata kafin karshen nawa tazo nariga na cimma burina akan Hajiya fatima
Boka yace shegiya hajja rahma wato kina burgeni al amuranki babu tsoron Allah acikinsa sam duniyar kawai kika damu da amma ba lahiran ba
Kincemin kinaso a salwantar da rayuwar Ashraf kwankin baya saidai dukkan aljanunda muka tura masa sun kasa yimasa komai dan yanada tsari babba dan haka ki hakura kawai
Toh boka na hakura saidai inaso ka juyarmin da hankalin wannan yaron da muka zo tare yazama komai nace yayi sai yayi batareda bata lokaci ba
Dariya bokan yayi yace an gama maza kuje ku tahomin dashi yanzunnan
Wani irin guguwa ce ta mamaye gidan Abdul dake waje zaune cikin mota yana tilawar Al Qur’ani jin guguwa yasaahi daga glass din motar yaci gaba da tilawarshi abinshi hankali kwance yanayi yana rokon Allah tsare mashi Aneesa da Ashraf ga dukkan shqrrin hajja Rahma da bokanta sannan Allah biye masu hakkinsu Allah maida masu sharrinsu akansu duk karshen kowace surarda ya karanta sai yayi addu’a ya shafa
Allahu akbar Allah maji rokon bawansa boka yafara ihu yana cewa kifita kibar nan yaronnan na konamu
Muguwa daman kinzone da niyyar konamu
Yaronnan yafi karfinki yafi karfinmu kifita kibar nan yana magana yana ihu
Ganin haka yasa hajja rahma fita dagudu takira Abdul yazo ya taimaka ma boka
Ba musu ya fito rikeda Al Qur’ani mai gurma
Koda yashiga ciki a karo na biyu sai ganin namomin daji sukayi suna fitowa daga wata yar karamar bukka sukayo kan boka da ihu yaketa zubawa yana fadin ki gaya masa gaskiya
Ki gaya masa abinda kk so yimashi
Ki roki gafarar su in ba hakaba zaki………
Bai karasa ba gidan tafara ci da wuta fitowa sukayi sukaja motarsu suka bar wurin itako hajja rahma in banda kuka babu abinda take tayi
Abdul kuwa murna yakeyi yana kara godema Allah da hakan ta faru
Gidanta ya kaita fita tayi da gudu tashige gida tabarshi dariya yayi yace kadan ma kika fara gani yanzu bokanki ya mutu saura ke
Ya juya ya fice
Kiran number Ashraf yayi yake tambayarshi ya hanya Ashraf yqce yanzu nake shiga Warri har nakira abokina yazo yanzu muna tare shi yakema jan motar
Abdul yace u cant blv idan na gaya maka Aneesa zata samu sauki
Dan Allah da gaske kakeyi Abdul yace am serious nan ya kwashe komai ya gayama Ashraf hawayen farin ciki Ashraf yayita zubdawa yana godema Allah sannan ya tambayi Abdul ko kafin ya mutu ya sanar masu da inda Aneesar take a delta
Aa yace sannan yayi smile yace yes dan da wawiyar takoma ciki nabi bayanta amma ban shiga cikin gidan kuma ba naji yana fadin tana ughelli
Alhamdulillahi cewar Ashraf yana goge hawayenshi ya kalli abokinshi yace guy ina ne ughelli a nan delta
Smile abokinshi yayi sannan yace karka damu zan kaika gobe
Allah kaimu Ashraf yace sallama sukayi da Abdul
Washe gari da safe Ashraf ko karyawa bai tsaya yiba suka kama hanyar ughelli Abubakar sunan abokin Ashraf na warri suna kan hanyarsu yakira Abu Sa’ad hira sukasha sosai daga karshe Abu Sa’ad yake cemashi yana fushi dashi jiya baizo mashi events biyu da akayi na bikinshi ba nan Abubakar ya shiga bashi hakuri sannan yake sanar masa cewar gashinan zuwa Abu Sa’ad yace toh Allah kawoka lfy Ameen yace sannan ya katse wayar
Kallon Ashraf yayi wanda shima shidin yake kallo da alamar tambaya a fuskarshi
Smile yayi yace Ashraf wai waya gaya maka matarka tana ughelli shiru yayi kamar baiji ba cen
Ashraf yabashi lbr sannan yace tunda ka kira abokinkannan nakejin gabana na mummunar faduwa anyaa……
Abbakar yace kai wannan auren zumunci ne domin kuwa yarinyar yayarshi ce da take riko ita zai aura gobe nema daurin auren
Kirjin Ashraf takuma bada dam…….
Addu’oi yafayi yana rokon Allah kawo mashi dauki niko nace ameen
Abbakar yaci gaba da fadin kuma yarinyar ta hadu wallahi ga hankali ga ladabi da biyayya kai Umar yayi dacen matar aure wallahi dan kamilar yarinya ce
Yau za ayi walima amma na mata ne zalla sai gobe da an taso daga juma’a za a daura auren yau anan zamu kwana inaga
Ashraf yace sosai ma kuwa amma kai a tunaninka zata kai Gimbiyata nutsuwa dariya abbakar yayi baice komai ba
Koda suka isa kai tsaye gidan Hajiya Atika suka nufa saidai makil yake da jama’a kasancewar dan lelen kaninta da yar autar diyarta na aure hakan yasa gidam yacika taf da mutane
Aneesa tana cikin daki sai jin gabanta na faduwa taketa famanyi tunda taga shigowar wata mota da samari biyu suka fito acikinta wanda lokacin tana bakin window ita tama dauka ko Abu sa’ad ne yashigo saidai taga bama motarshi bace dan tanajin kewarshi tun jiya da misalin 9pm rabonta dashi gashi yanzu 10am bata ganshi ba hakan yasa dataji ahigowar mota tazo window
Jin kirjinta na tsananta bugawa ne yasa takuma kallon Ashraf a karo na biyu sai ta ga kamar ta taba ganin fuskar nan toh saidai ta manta inda ta taba sanin fuskar ta dade tana kan hakan cen dai ta furta
ASHRAF MIJINA…………………
Toh fa yan uwa niko nace akwai yaki kenan babba ma ba karami ba Amma.. ……..
✍????by Leemat
I CARE 4 U all ????????????????????????????????????????
????????????????⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????⚖????????
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS tsintsiya muke
madaurinmu 1 ????
Ina mai bama masoya wannan novel hakurin rashin jina kwana biyu hakan tafarune sanadiyyar kirana da wasu yan Adawa sukayi suka cimin mutunci bansan hawaba bansan sauka ba amma bkm ina rokon Allah ganar dasu gaskiya nina yafe masu Allah yafe mana baki daya Ameen sannan da tafiya danayi shima amma Alhamdulillahi Allah ya dawo dani lfy nagode wa masoyana masu kirana ta waya da masu turomin text mssgs na fatan alkhairi Allah saka da alkhairi nagode ????????????????
37
Aneesa tafito a 60 saidai ko kafin ta sauko kasa su Ashraf sun riga sun shige bangaren Abu Sa’ad ko