ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Hajiya Atika da sauran matan dasuga Aneesa tafito aguje suma sai suka bi bayanta dansu a tunaninsu iska ne ya bugeta sai faman ku taimaka suketa fada suna binta
Aneesa kam tana kaiwa inda tagasu Ashraf nan ta tsaya tana maida numfashi tana fadin Innalillahi wa inna ilaihi raji’un
Ashraf mijina……..
Ashraf mijina…….
Ashraf mijina………..
Abinda taketa nanatawa kenan hajiya Atika kam sai hawaye taketa famanyi tana yambayarta ina yake Aneesa ta nuna mata motar da su Ashraf suka shigo dashi yanzu ta bude baki kenan dan takuma yin magan sai taji kanta namata wani irin juyi tafara jin jiri na dibarta ai kuwa sai ji kake timmmm…..
Aneesa tazube akasa abinka da taron mata kuma ma gidan biki kuma Amarya sai ihun mata kakeji suna ihu wasu na salati banda hajiya atika da ta zube a kasa sumamma dan ganin Aneesa a kasa ba karamin daga mata hankali yayi ba
Nan dai aka kwashesu akayi cikin daki dasu ba’a dau lokaci ba Hajiya Atika ta farfado saidai Aneesa anyi anyi amma ina
Kuka Hajiya Atika taketayi mutane kuwa sai faman hakuri aketa bata
Ganin kuka bazai fisheta ba yasa tamike tanufi bayi ta dauro alwala tafito nan ta bukaci kowa ya fita haka kuwa akayi kowa yafice yabar dakin banda inna da family dr dinsu da tàketa iya kokarinta dan ganin ta ceto ran Aneesa
Hajiya Atika tahau sallaya tayi nafila raka’anta biyu tana idarwa ta dauki Al Qur’ani mai girma tafara kira’a
Labari har ya isa kunnin Abu Sa’ad cewar Aneesa ta mutu sumewa yayi dakyar ya farfado saidai daka kalleshi zaka gane ba karamin tashin hankali yashiga ba
Haka shima Alhaji ba karamin tashin hankali yashiga ba
Kiran dr yayi yana fadin koda gaske ne Aneesarshi tabar duniya ? Dr tace aa hamdala yayi sannan yafito domin zuwa duba masoyiyarshi
Yaso yashigo yazo yaga rabin ranshi amma sai akace yayi hkr ba mutuwa tayiba sumace kuma inshaa Allahu zata farfado cewar wata mata
Safa da marwa yaketa famanyi gani hakan bazata fisheshi ba yasa yakoma daki ya dauro alwala domin rokon Allah mai kowa mai komai ya farfado masa da muradin rayuwarsa
Su Ashraf kam duk sunbi sun damu barinma Ashraf da kirjinshi ya tsananta buguwa sai kace zai fado kasa
Addu’oi yahauyi na neman sassauci gun Allah
Sai yaji bazai iya barin gidan ba Duk da neman Aneesarshi na ranshi sai yaji ya tausayamawa Amarennan da familynsu nan danan yatuna da ranar aurensufa da Aneesarshi ce aka nemeta sama ko kasa aka rasa kuka yafarayi kamar karamin yaro wanda ya dagama Abbakar hankali shima dan yasan tunowa yayi da abinda ya faru dashi
Rarrashinsa yatayi Abu sa’ad shima ji yayi ya karaya tausayin Ashraf ya kamashi addu’a yayi yarufe Al Qur’ani sannan ya shafa nan ya matso kusa yake tambayarsu ko lfy yaga Ashraf na kuka sai kace wanda aka aikoma da sakon mutuwa?
Ashraf yadan tsayar da kukanshi ya kalli Abu sa ad yace bro ai gwar sakon mutuwa ya riskeni da abinda ya faru dani ace ruhita 1 ta …………..
Kasa karasa maganar yayi sbd wayar Abu Sa’ad da yahau ruri ganin ansa Heart 2 Heart da sauri ya daga yace Amincin Allah ya tabbata gareki ya ruhi ta
Aneesa tayi smile kamar yana kallonta tace tare dakai
Smile yayi yace mata ya jikinki itama tace ya jikinka ganin sun hada baki gun sanin lfyar juna ne yasa dukkansu yin dariya
Atare suka kuma amsawa dacewar Alhmdllh saidai kewarki/ka data addabi raina
Dariya suka kumayi idon Abu Sa’ad ne yakai ga Ashraf nan danan ya lura da halinda Ashraf yashiga kokarin mikewa yayi dan barin dakin saidai Ashraf ya kada masa kai alamar aa karya tafi yayi zamanshi
Ba musu ya zauna yacigaba da waya hira suka hauyi nan tabashi lbrin yanda akayi ta farfado sannan taji anacewa shima ya suma
Tanata tsokanarshi tana dariya shiko yace ok hakanema ko toh bakomai zan rama ai nima
Aneesa tace saidai ka rame………. takuma cewa au banasonfa ka rame nafison kayi kiba
Smile yayi hira sukasha cen dai hajiya Atika tashigo tace maza ta katse wayar yanzunnan tunda duk sun zama marasa kunya daga ita harshi kunyace ta kamata tace habibi sai anjima ummana tace in katse wayar tanada magana dani kasan tsakanin uwa da diyarta………
Fisge wayar hajiya Atika tayi ta kara a kunnenta tana smile tace toh marar kunya wato umar kai alan dole kasan soyayya koh?
Toh karka damu gobe wara haka ai tazama mallakinka marar kunya kawai
Abu Sa’ad ya marairaice mata yace habaa mana big sis ya kikeson inyi da rayuwata ne eh?
Sanin kankinefa Aneesa itace ruhina kuma na dade ina cikin wani irin hali na……………
Hajiya Atika taki barin ya karasa dan tasan kaninta lafiyayye ne kuma jarumi ne yanada yawar bukata duk da bai taba sanar da itaba sai yau amman ita tasani saboda yana fama da ciwon ……….
Tace umar wllh bakada kunya waini Atika yaushe umar yazama hakane banida lbr
Abu sa’ad yacigaba da fadin ana gama daura aurenmu zanzo in dauki matata dan ina bukatar kasancewa tare da ita
Allah shiryeka umar cewar Hajiya Atika tareda datse wayar juyowa tayi don yima Aneesa magana saidai bata ganta a dakin ba
Smile tayi tace su Aneesa sarkin kunya Allah dai yabaki hkr da juriyar bukata irin ta umar
Fitowa tayi abinta
Abu sa’ad bai kara tambayar Ashraf ba hk shima ashraf bai cigaba da bashi lbrin ba hirarsu sukayitayi sosai Ashraf yadan saki jiki da Abu Sa’ad
Karfe 3:30 na rana aka fara shirye2 walima har zuwa wannan lokacin Aneesa bata sake jin muryan Abu Sa’ad ba hakan na damunta saidai batada mafita sai hkr
Inna ce tashigo tana guda tana wakarta na ayye mama ayye mama mamaye iye
Ayye mama ta tafi kenan mamaye iyeee ………niko leemat sai kwasan rawa naketayi????????????????????????
Takuma karawa ta rera Amaryace Amaryace Amaryace Amaryace Amarya…….
Kiyiwa mijinki biyayya ki bashi kanki idan ya bukaceki ki ware kafa ki………..
Aneesace tamike ta fisgi wayar hannunta tayi wani dakin ta kulle tana murmushi
Number Abu Sa’ad takira kamar yana jira bugu 1 ya dauka jin muryarta ne yasashi gigicewa sai kuma gashi sandar girmanshi sai faman harbawa take Allah yasoshi shi kadai ne a cikin dakin wani irin nishi yake hadeda smile da karfi ji yake kamar yana tare da ita
Yace inama muna tare yanzu haka da banga abinda zai hanani shan…………………….????????????
Wash hannuna yagaji gashi ink dina ya kare kuyimin uzuri masoya masu son jin abinda Abu Sa’ad zai fada …… ……….
Sai mun hade a gaba
Luv U all????????????
????????????????⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????⚖????????
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
THE END
40
Aneesa sai kuka take tana kwance a kafar Hajiya Atika Alhaji Sama’ila ne yayi gyaran murya yace Aneesa ya isa haka ki daina kukannan haka Alhamdulillahi mugode Allah da ba’a daura aurenba Allah cikin ikonsa ya bayyanar da gaskiyar lamari da gaggawa
Umar ina mai baka hakuri da yimaka nasiha kazama mai dangana ka karbi jarabtar Ubangiji hannu bibbiyu kuma kazama mai godiya ga Allah aduk yanayinda ka tsinci kanka kayi hkr kabar wannan hawayen
Kai kuma Ashraf ga matarka nan sai ka godewa Allah daya bayyanar maka da ita batareda kasha wahala ba kuma yasa ta fada a hannuai kyau ba mugun hannu ba
Wayar Ashraf ne ta hau ruri ya dauka da wuri yana washe hkr kai aboki yane? Cewar Abdul
Ashraf yafara hawayen farin ciki yama kasa furta koda A ne bare ya bashi amsa