BABU SO HAUSA NOVEL

ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Hajiya fatima da akai komai akan idonta ne tashigo tana smile tana tausayama diyarta kana tace Alhmdllh Allah nagode maka dukkansu suka juyo suna kallonta Aneesa tayi maza taje ta tsuguna a gaban mom tana kuka tana fadin mom ki gafaceni mom bansan meke damuna ba mom ina bukatar addu’arki Hajiya fatima ta dagota tashare mata hawayenta kana tace ni bakimin komai ba a kullum addu’ata shine Allah shiryeki ya karemin ku da al umman musulmi baki daya Anee dear na yafe maki

Godiya suka shiga yimata kana tace ki nemi yafiyar Aisha domin kuwa ita kikafi musgunamawa rannan har pp soup kika zuba mata a fuska saida aka kaita asibiti

Sannan bayan wannan kika shiga har dakinta kika hada mata electric sannan kika kirata akan tafito ta rakaki koda tafito tana sa hannunta akan kofa sai wutan yajata saida tasuma dan ma Allah yayi tanada karan kwana shima saida tayi kwana 2 a asibiti haka kika kone mata books dinta gabaki daya harda uniforms dinta sannan shekaran jiya jiyannan kika zazzageta harda iyayenta da suka rigayemu gidan gaskiya bata amsa ki ba hakan yasa kikaje kitchen tana aiki kika zuba mata ruwan omo ajiki koda tayi kokarin fitowa ta zame gashi har yanzu tana fama da kafarta na hagu Y Aneesa y????

Aneesa zubewa tayi a wurin tana kuka mai tsumar da zuciya kana tace acikin kukan mom wallahi bansan ma nayi ba mom sanin kanki ne ko makiyi na bazan iya aikata masa haka ba bare sister na wacce nake ji da ita fiye da kaina Aisha ta tsuguna tana goge mata hawayenta tana fadin nima nasani sister bayin kanki bane amma Karki damu Allah yana tare damu kuma babu wanda ya isa ya rabamu sai Allahn da ya hadamu

Dan haka ki daina kuka nina yafe maki Allah yafe mana baki daya Ameen mom ta amsa sannan tace Allah maku albarka ameen suka amsa nan Aisha tace sister tashi kiyi wanka sannan kifito inada suprise maki a palo

Ba musu ta tashi tashige bayin Aisha da Hajiya Fatima suka fito Aneesa ce tafito ta saka jallabiya brown ba karamin kyau yamata ba tana sakkowa Aisha tace wow mashaa Allah sister kinko kalli mirro kuwa?

Dan bugun wasa takaima Aishan nan suka shiga dariya Aisha taja hannunta har zuwa kan dinning tayima Aneesa nuni data zauna ba musu ta zauna nan tafara bude first warmer ganin favourite dinta yasa Aneesa darawa kana tace wowww sister Aisha Allah barmu tare ngode da kulawarki gareni wannan pp soup haka

Aisha tabude na 2 shima lafiyayyen fried rice ne aciki sai kamshi ke tashi duk ya gauraye palon ina gefe rike da ✍???? amma inata hadiyan yawu ina fadin inama ace zan iya ajiye ✍???? domin nima in taya Aneesa kwasan gara ????

Hajiya sai kallonsu take cikeda so da kauna a haka suka zauna suka ci suka sha bayan sun kammala ne suka kintsa wurin tas sannan sukayi ma hajiya Fatima sallama cewar zasu fita shan iska addu a tamasu suka tashi suka fita motoci ne gudag 4 suka bi bayansu har suka je suka dawo a ranar kam shakuwa ne mai karfi tqshiga tsakaninsu abin sai wanda ya gani domin kuwa ranar a dakin Aneesa suka kwana

Bayan kwana biyu saiga hajja rahma ta kawoma Hajiya fatima ziyara nan tayita nuna farin cikin ganin Aneesa da Aisha saidai ita Aisha taki sakewa da ita domin abin har mamaki yake bata ganin yanda hqjja rahma take nuna mata so yau

Zuwa yamma hajja rahma tawuce dama tazo sallamar Aneesa ne dazata koma skul domin kuwa har sayayya tamata washe gari Aneesa takoma skul dama Abu zaria take tana karanta bio/chem Aisha har zaria taje rakata tayi kwana 1 sannan tadawo koda zata dawo saida sukaci kukan rabuwa da juna na wasu yan lokaci Aneesa ta dauki shawarda Aisha tabata kan ta bude shago a zaria ko a minna hakan kuwa akayi ta bude shago a minna babba na indian dress da designers bags harda classic shoes babban boutique ne ya hadu iya haduwa dama ana 2weeks zata koma skul sukaje itada Aisha suka ba wata kanwar Hajiya fatima kudi Hannatu da cewar ta tayata saro kayayyaki lfyayyu haka kuwa akayi nan tasa sunar shagon Tripple A classics & designers

Ma ana Aneesa Aisha Abbas AAA

Sannan tasa Aisha a managing director na shagon haka ta nemi tailors tazuba acikin shagon shago kam duk wanda yashiga bazaiso fita ba sbd tsabar haduwar sa domin kuwa ko kofar shiganta ma abin kallo ce

Aneesa ba wanda bai santa a makarantar ba domin kuwa tana taimako sosai hakan yasa kowa yasan da ita hatta estate din mahaifinta kowa ya santa kamila ce bata kula maza kuma mai gadin da matarshi ta daukesu kamar iyayenta ana haka bayan satinta 1 da komawa ne …………..

✍????by Leemat

Love U Ol
????????‍⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????‍⚖
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????

Wannan page din nakine Habibaty MUM MUHIBBAT ???? Allah bar zumunci da kauna jinjina da godiya agareki sweety I L U so dearly ????????❤????????????????????????????????

                   7

Wata rana taji kamar ana kiran sunanta lokacin tana cikin part dinta sai taki amsawa aka kuma kiran sunarta a karo na 2 nan ma taki amsawa a karo na 3 ne taji murya kamar na matan mai gadin estate din ai kuwa sai ta amsa da na am mama ina zuwa

Kamar da ta sani karta amsa ai kuwa nan taji kamar ance fita abinki da gudu tafito daga ita sai wando 3qrter da yar karamar riga ajikinta ko kan ta isa bakin gate baba mai gadi yariga ya hangota hakan yasashi mikewa yana fadin subhanalillahi yar Albarka lfy kk fito babu ko kayan kirki ajikinki……

Bata kobi ta kanshi ba tana kokarin bude kofa tafita ne dayaga da gaske take kuma baida karfin hanata hakan yasashi yi mata tsawa sannan ya dafata ai kuwa ihu ta sakar wanda yasa duk aka firfito gata sai wani huci take kamar kumurci sai hararan baba mai gadi take amma ba daman fita

Isowar mutane ne yaba baba mai gadi bakin magana yace ma matarshi da wata mata ku kaita ciki Aneesa tace kar wacce ta tabani mutane suka fara tambayar ko lfy yasa tayi ihu hk????

Aneesa tace lfy ta lau kuce yabarni in fita babu ruwanshi dani mama tace subhanalillahi yar albarka lfy hk wani wawan harara Aneesa tamata kana tace ina lfy fa mijinki ya hanani fita nan mama tagane da matsala kallon mijinta tayi shiko yace idan baki koma cikiba zan maki abinda bazaki manta daniba Aneesa tace kayi Allah kabarni in fita ai kuwa ya bude kofar sannan yace fita mugani kasa fita tayi jama’a sai kallon ikon Allah suke dan wannan ba dabi’un Aneesa bane sa insa dana gaba da ita ba

Baba mai gadi yace maza kafin in rufe idona in budi ki koma ciki inba haka ba ai bata tsaya jin abinda zai fada ba da gudu takuma komawa ciki mama ce tabita abaya sannan baba mai gadi yace kubarta kawai asiri aka mata ana son tabi duniya ne saidai duk wanda yake shirin kwasan alhakin baiwar Allah bazaiyi nasara ba kuma sai ya tozarta a idanun duniya

Ameen kowa ya amsa sannan wani daga ciki yace gaskiya yakamata muyita tayata da addu’a domin kuwa Aneesa ta daban ce
Allah yabata lfy ya mayarma duk wanda yake niyyar yimata hk Ameen suka amsa kowa ya koma yana jimamin irin wannan al amari sannan suna mamaki wai ace kamar Aneesa tanada makiya duk taimakonta ga al umma kuma gata bata da girman kai Allah sauwaka niko nace Ameen

Koda Aneesa tashiga ciki sai ta tsinci kanta da tsanar kanta nan tafara bubbuga kanta a bango ganin haka yasa mama ta kwallama baba mai gadi ihu akan yataho ba lfy aikuwa da gudu yataho shiganshi cikin palon Aneesa keda wuya ai kuwa sai ta tsaya chak tana huci ga jini nazuba a saman goshinta baba mai gadi yace ke wai bazaki fita kibar jikin yar talikar Allah bako saina saba maki …….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button