ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Ganin haka yasa Alhaji sama’ila ya mike yaje ya karbi wayar a hannunshi yayi sallama Abdul ya amsa Alhaji yace ko zan iya sanin sunanka?
Nan Abdul ya gaya masa sannan cikin tashin hankali yace ina Ashraf din hop lfy yake
Alhaji yace lfy lau lai me dinsa ne?
Jin irin wannan tambayar ne yasa Abdul yafara kyarma dan nan ya fara tunanin ko lfy domin shi a tunaninsa shikenan Ashraf ya…….. bai karasa ba Alhaji yace kayi hkr Ashraf ba…….. Ai Abdul salati yahauyi bai tsaya yaji karshen kalmarda Alhaji zaiyi ba wayar tafadi a hannunshi saida bata fashe ba
Alhaji ya katse kiran sannan ya kalli Ashraf da sai hawaye keta ambaliya a idanunshi sai kace mace yace wai Ashraf me hakane?
Sai kace ba namiji ba habaa dan Allah wai meke damumkune kun tasamu a gaba sai faman kuka kuketa mana kamar wayanda aka aikoma da sakon mutuwa kunga ni wallahi idan bazaku bar kukannan ba Aneesa zata……..
Ai bashiri suka share hawayensu harda smile na dole hada baki sukayi sukace habaa Alhaji ai munyi shiru
Aneesa itama shirun tayi Alhaji yacigaba da fadin kuyi hkr dukkanku Haka Allah yaso nan yace Ashraf ya gaya masu abinda ya faru ba bata lokaci yabasu lbrin komai harda yanda Hajja Rahma tayi da Abdul
Aneesa ce tafashe da kuka mai tsumarda zuciya tace yanzu Hajja Rahma ce tamin haka?
Toh me namata wani laifi Umma tamata da taso salwantar da rayuwata habaa Hajja me namaki wani sabon kukan tasa wanda ya sosa zuciyar Kowa Ashraf kam bako kunya yaje kusa da ita ya rungumeta yana bubbuga bayanta yana bata hkr kunyace takamata wanda batasan lokacinda kukan ya tsaya mata ba sai ta harareshi tace sakeni ji yanda ka rungumeni agaban manya
Dariya suka mata dan yanda take maganar abin dariya ne
Alhaji yace maza ku kira gida ku sanar dasu gobe idan Allah ya kaimu saimu kama hanya dukkanmu muje cen din koh?
Eh hakan za ayi Alhaji cewar Hajiya Atika Aneesa ta kalli Abu Sa’ad tace Uncle tunda aketa magana kai kayi shiru bakace komai ba habaa Angon Aisha kodai bakasan zabinda namaka ne? Wallahi idan kaganta sai ka rude dan Aishata ta daban ce ga kyau ga hali dariya suka kumayi shiko Abu Sa’ad yana kwance kan kafar hajiya sai yace Allah kenan mai yin yanda yaso da bawansa dazu ina cikin farin ciki mara misaltuwa na ganin zan mallaki Aneesa ashe ba haka Allah ya tsaramin ba amma bkm Aneesa wallahi na aminta da zabinki gareni dan nasan bazaki taba zabimin abinda bazai dace daniba saidai damuwata 1 tak Yarinyar ko zata soni tsakani da Allah ko zata amince dani kamar yanda kk aminta dani shine ban sani ba
Smile Aneesa tayi kafin tace indai wannan ne karka damu dan nasan sister na bazata taba sabamin ba kuma bazata watsamin kasa a idona ba dan haka Angon Aisha karka damu indai wannan ne Ashraf yace tabbas kuwa indai wannan ne karkaji komai domin kuwa matata ta iya zabe kuma kud da kud suke kamar hanta da jini
Toh Alhmdllh cewar Alhaji Allah maku albarka nan yamike yayi tafiyarsa itama hajiya ta mara masa baya akabar su 4 Ashraf,Aneesa,Abubakar da Umar wato Abu Sa’ad kenan
Hira sukasha sosai daga karshe Aneesa tasa Ashraf yakira mata gida haka kowa yayi farin cikin jin muryar Aneesa Abdul da Aisha harda hawayensu na murna
Washe gari suka kama hanyar Abj karfe Hudu suka isa murna gun iyayen Aneesa baya misaltuwa su hajiya Atika mamaki ne yakamasu dan sam ba wanda zai yi tunanin Aneesa yar masu kudice bcos she’s so simple Aisha kam kuka tayi na farin cikin dawowar aminiyarta kuma uwar gidanta
Ganin kukannasu bamai tsayawa bane yasa su Abu Sa’ad suka gane itace Aisha domin kuwa tunda suka rungume juna suketa kuka sunki sakin juna
Dad ne yayi gyaran murya domin kuwa kowa ya zauna su suka rage yace ya isa haka yaran Albarka kuyi shiru sannan ku zauna ba musu suka zauna hannunsu rike dana juna dad yace toh da farko dai sai mugode Allah Alhaji bazamuyi magana yanzu ba harsai kun huta yanzu dai bama wannan ba kuje kuyi wanka idan kun fito ga abinci nan sai kuci kuje kuhuta dan nasan kun debo gajiya
Haka kuwa akayi bayan sunyi wanka suka fito suka ci abinci Alhajji yace basai mun huta ba muna iya farayin magana yanzu haka kuwa akayi bayan kowa ya zauna Addu’a suka farayi sannan aka hau magana nan Aneesa take sanarwa Aisha hukuncin da ta yanke akanta batareda ta sanar da ita ba
Dukda Aisha batasan ko waye bane mijinnata ba batayi gardama ba sai ma godiya ga Allah datayi takuma nunama Aneesa inshaaAllahu bazata watsa mata kasa a idoba domin kuwa tasani Aneesa bazata taba cutar da itaba
Aneesa taji dadin jin hakan daga bakin Aisha duk da tasani Aisha bazata taba kin zabinta ba nan tanunama Aisha mijinta kallon juna suka hauyi Umar harda yima Aisha signal ????
Alhaji yabasu Dad labarin yanda abin ya faru kamar haka
Ana shirin dauran Aurensu Aneesa kenan bayan su Ashraf sun fito cikin shigarsu ta alfarma Allah mai iko yasa shi Umar yakirata ta waya yace tazo ya ganta kunsan yaran yanzu itako tabita baya taje suna kan magana Ashe shi Ashraf ya manta da zobensa akan mirrow sai yashigo yana fadin ango ango ango kashaaa……. bai karisheba sai kawai yafara hawaye yana kiran sunan Aneesa matata kece
Itama da ganinshi sai tafara rawar jiki nan tafadi sumamma suka kiramu ta waya haka mukabi ta baya mukaje muka riskesu Ashraf na hawaye shiko Umar sai binsu da ido yakeyi dan bai gane komai ke faruwa ba koda ta farka nan tafara kiran sunan Allah sannan takira Ummanta da Dadinta sai Abdul Ashraf da Aishanta sai kuma su mama da baba daganan sai tafashe da kuka tana fadin kanta namata ciwo
Hankalinmu yatashi nan aka bata magani tasha nikuma na tambayi Ashraf shine yabani labarin komai dajin hakan sai Umar ya suma dakyar aka samu ya farfado nan nace toh ya za’ayi bayan mun tara jama’a awaje ana jiranmu gashi yanda Allah yaso bkm bari inje ince an fasa kowa yawuce har nakai bakin kofa sai Aneesa takirani tace Abba idan Uncle bazai damuba ni nayi mashi zabi kuma zabinda bazai taba yin kuka dashi ba
Dajin haka Umar yace bkm shi indai Aneesarshi ce tamashi wannan zabin toh ya aminta da zabinta saboda so da kaunarda yake mata duk ni banso in biyewa yara ba Amman sai naga bamuda mafita taya za ayi mutara mutane sannan muce suwuce batareda an daura auren ba wannan dalilinne yasa na amince da hakan
Nan muka shirya muka fita aka daura Auren Aisha Da Umar abisa sadaki naira dubu dari biyar
Gashinan ma mikawa dad kudin akayi dad ya karba yasa Albarka sannan yamikawa umma itama tasa Albarka sannan suka mikawa Aisha itako kin karba tayi tace umma ni bana bukatarshi kuyi yanda kukeso dashi dad yace hakkinki ne dan haka ki karba ba musu ta karba ta mikawa Aneesa itama kin karba tayi tace sist nakine kirike Allah sa albarka Allah bamu zaman lfy baki daya Ameen kowa ya amsa umma ta basu labarin abinda ya faru da hajja rahma
Allah sauwaka kawai sukace dan tabbas hajja rahma bata kyauta ba koda yake ai abinda tashuka shi takenan take girbewa yanzu Dad yace kowannensu ya dauki matarshi suje sashin Abdul su kwana Sannan ya aika asiyo naman kaji da yourghurt yace akaima amaren ????
Addu’a sukayi nan manya suka fita suka bar amarennan biyu Umar ne yamatsa kusada Aisha ya rungumota bako kunya
Shiko Ashraf mikewa yayi da niyyar daukar Aneesa amma sai taki yarda Hajiya Atika ce
dan yin magana da kaninta sai dai abinda tagan sunayi yafi karfin idonta dan soyayyace zalla sukesha kamar basu ba nima ganin haka yasa nabi bayan Hajiya Atikan da gudu kunsan ni karamar yarinya ce ????????