BABU SO HAUSA NOVEL

ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

Aneesa tayi wata dariya sannan tace nifa ba mace bace kuma ma ai bani 1 aka aiko cutar da ita ba munada yawa

Baba yace kunkai ku nawa? Kuma me tayima wanda ya aikoku? Wani dariyar takuma yi kana ta tabe baki tace ina ruwanka da abinda tayi? Kuma waima kai me hadinka da ita ne eh dan bakin ciki

Smile baba mai gadi yayi kana yace lallai kam ina umurtanku da kusan inda dare yamaku in ba haka ba…… cikin sauri tace in ba hakaba sai me?
Me zaka iya yi?

Kaga mufa aikanmu akayi kuma mu 30 ne aka aiko mata kakoga idan kasan wata to bakasan wata ba hahahahhhh ……..

Baba mai gadi yace haka kace koh? To muzuba nida ku shge kafasa…..

Tukunama me sunanka?
Cikin gadara yace sunana duna 6aleri subhanalillahi kaiba musulmi bane cikin fushi yace ban saniba dan rainin hankali kawai hannunshi ya daura kan Aneesa wani irin wahalallan ihu tayitayi cen tazube a kasa nan tafara atishawa

Mama kam banda kuka babu abinda takeyi duk tausayin aneesa ya kamata baba yafara bata hkr akan tayi shiru Allah zai kare masu Aneesarsu Ameen mama tayita amsawa da nan tamike taje ta debo ruwa mai dan zafi tazo ta gogema Aneesa jininda ya bata mata fuska bayan ta kammala ne ta daure mata wurin da bandeji baifi 10 mins ba Aneesa ta fara bude ido ganin mama tanata faman share kwalla ne yasata mikewa jin kanta namata zafi ne yasa tasaki yar kararda ya dawo da hankalin mama kanta Aneesa tace mama kaina zai fashe mama zan mutu …….

Rufe mata baki mama tayi kana tace Aneesa Allah yana tareda mai gaskiya kuma inshaa Allahu bazasuyi nasara akanki ba

Aneesa tace suwaye mama?

Mama ta bude baki kenan zatayi magana Aneesa ta……….

✍????by Leemat

Love U all????????❤
????????‍⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????‍⚖
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????

Wannan page din nakine my sweety MUNEERA na jinjina maki kuma ina mai alfahari da samun kamar ki a matsayin besty na Dear I ❤ U ????

                   8

Aneesa tace mamana halan hauka nafara koh? Shiru mama tayi Aneesa ta mike ta dauko wayarta tazo ta zauna kusa da mama nan tashiga dialing number Hajiya Fatima ringin 2 yayi aka dauka Aneesa da sallamarta a dayan bangaren kuwa aka amsa sannan tace mom ina bukatar addu’arki fiye dana da hankalin Hajiya fatima ne ya tashi kana tace lfy?

Aneesa tace lfy ba lfy ba mom nidai kuyita tayani da addu’a mom tace toh shikenan Anee Dear inshaa Allahu zamuyita yimaki addu’a yanzu ma zan sanar da daddynku Aneesa tace ohhh dad yana gari ne eh mom tace mata nan Aneesa tace bashi mu gaisa daddynda tunda suka fara waya yake jinsu sai yace bazan karba ba kice mata nayi fushi tunda bata tunawa dani sai momminta jin haka yasa aneesa ta katse wayar tana smile nan tayi dialing number daddynta bayan ya dauka suka gaisa nan suka hau hira saida suka ci kusan 1hour sannan sukayi sallama kiran number yayanta tayi wato Abdul basit yana dagawa yace yar my queen, my precious little sister smile aneesa tayi kana suka gaisa nan shima take rokonsa daya taimaka mata da addu’a toh yace mata sannan suka hau hirar rayuwa

Saida sukayi mai isarsu sannan sukayi sallama bayan Aneesa tayi mashi alkawarin kai mashi ziyara a cen inda yake karatu a U.S.A next week yaji dadi yace mata Allah kawota domin kuwa yaji kewarta

Nan takira Aisha maganar dai duk 1 ne a tayata da addu’a Aisha ta shaida mata cewar tayi mummunar mafarki akanta saidai bata sanar da ita komai akan mafarkinba nan tacema Aneesa gobe monday su dau azumi sannan su rage barcin dare surika yin nafiloli Aneesa tace toh siater Allah shige mana gaba Ameen Aisha ta amsa nan sukayita hira mama kam na zaune sai faman binta da kallo taketayi sannan tana ayyanawa acikin ranta cewar hardani za ayi azuminnan da nafilan dare wallahi dan bazan taba bari a cutarmin dake ba Yar albarka nan tayi smile wanda yasa aneesa tambayarta nan tacema aneesa bkm kawai tana murnar ganinta cikin nishadi ne

Washe gari Aneesa,Aisha,Mama da Baba mai gadi suka dauki azumi Aneesa ce tafito daga part dinta Zuwa garage tana isa bayan ta bude motar ta tayi bismillahi kafin ta shiga ta zauna idonta ne yakai gun dayan motar ta wani layane baki wul dashi da sauri tafito tana kiran sunan Allah jikinta har kyarma yake tace Baba taho kagani baba mai gadi da wuri ya iso wurin harda matarshi da batason abinda zai taba lafiyar Aneesa ta biyo bayanshi

Yana isa Aneesa ta nuna mai layar nan yaje kusa da layar ayi addu’oi ya tofa nan layar tafara hayaki mama kam wannan al amari yafara bata tsoro sai tambayar kanta take waishin me Aneesa tayi ne da ake neman salwantar da rayuwarta haka yarinyarda babu ruwanta yarinyarda take girmama nagaba da ita………

Aneesa ce ta rungumeta hakan ya dawo da ita daga tunanin da take Aneesa kamar zatayi kuka tace mama waishin wa na batawa rai ne da bazai sanar dani ba in rokeshi gafara ba sai dai yana kokarin…..

Baba mai gadi yace yar Albarka koma wayeshi toh hakika yana wasa ne da rayuwarshi domin kuwa Allah bazai taba bashi sa a akanki ba

Shiga motarki kiwuce makaranta abinki hankali kwance Allah natare dake mama takara dacewa indai har muna raye toh inshaa Allahu sai inda karfinmu ya kare

Aneesa tace nagode baba nagode mama Allah barmu tare suka amsa da ameen haka aneesa tashiga mota tawuce makranta bayan tafiyarta ne mama tace a gaskiya malam yakamata …………….

✍????Leemat

I L U ol????????????
????????‍⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????‍⚖
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????

Wannan page din nakune masoyan asali yan group din ANEESA YAR PRESIDENT ina ❤ ku irin sosai sosai dinnan Allah bar kauna????????????????

                    9

Yakamata musan abinyi tun kafin a cutar mana da Aneesa domin kuwa wallahi nikam sai inda karfina ya kare indai akan Aneesa ce Baba mai gadi sai kallon matar naahi yake shakka babu yasan sun shaku da Aneesa sannan kuma shima yasani harga Allah sai jin aneesa yakeyi kamar jininshi shima kuwa koda zai rasa rayuwarshi ne dan taimakawa Aneesa he’s ready kai kaji soyayyar gaakiya Allah hadamu da masoyan gaskiya
Ameen ………

Mama tacigaba da cewa malam kaga Allah bai taba bani diya macebako?
Sai gashi Allah ya albarkanceni da haduwa da Aneesa tun ranarda nasanyata a idanuna nafara jin dadi domin kuwa nasani Allah ne ya hadamu nakuma ci al washin maida Aneesa diyata tilo sai gashi Allah cikin ikonsa yasa Aneesa ta daukeni tamkar mahaifiyarta sai yau in wayi gari inga wani banza cen na kokarin salwantar min da rayuwarta sammmm…..Allah bazata sabu ba

Baba yace ki kwantar da hankalinki inshaa Allahu babu abinda zai sameta domin kuwa batada hakkin mai kokarin cutar da ita dan haka muci gaba dayimata addu’a Allah zai kareta Ameen mama ta amsa sannan ta mike tana fadin bari inje in debo kayayyakinta in goge mata su kafin ta dawo baba yace kedai ba kullum tana hanaki ke kuma baki bari bako?

Mama tace toh baji ikon Allah mutum da diyarshi ace wai kar ya taimaka mata bayan tanada ladabi da biyayya kaga nidai sai nayi mata gugan in kuma yi mata wanki in akwai masu dauda murmushi Baba ya sakar mata kana yace toh masu diya kardai ki manta nima dai diyata ce kuma yar albarka tace mama bata amsa mashiba tayi wucewarta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button