ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

✍????by LEEMAT
LOVE U OL????❤????????????
????????⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????⚖
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????
Wannan page din nakune jinin jikina yan uwa nagari Aunty Fatima Dada Kuta ❤
Aunty Hasiya Antiwo????
Aunty Safiya Dada Kuta????
Aunty Aisha Dada Kuta????
Aunty Hamida Dada Kuta ????
Ina yinku irin sosai sosai dinnan????❤
11
Tana shiga da sallamarta daki tanufa ta rage kayan jikinta shiga bathroom tayi ta watsa ruwa ajiki sannan ta dauro alwala tafito jallabiya tasaka da hijab tayi sallah a nutse
Tana idarwa tayi kira ar Al Qur’ani mai girma ba ita ta daga daga sallayarba sai 6pm nan tayi Addu’oi tashafa sannan tafito
A palo ta tarar da mama tana jera fruits a fridge murmushi tayi kana tace mama nida nake kokarin fitowa yin aiki ashe har kin kammala
Smile mama ta mayar mata kana tace yar arziki ai kiyi zamanki ki huta kinga mun saba da wannan aikace2 lokacinda muke aiki a cen gidan senator mansur ai yaranshi har…… Aneesa ce ta katseta dacewar habaa mama baki mantuwa ne? Kusan kullum sai kinyi maganar nan kiyi hkr ai yariga ya wuce yanzu baganinan ba diyar mama ita kadai yar tilon mama da baba murmushi mama tayi kana tace tabbas ina alfahari dake inaji ajikina kamar nina haifeki saboda komai daya kamata yaya suma iyayensu na kyautatawa kina mana kamar mu muka haifeki sannan kina mana hidima dagamu har yaranmu sannan…..
Aneesa ce ta rungumeta tana fadin dan Allah mama kibar fadin haka ku kuka haifeni nice diyarku tilo ina kaunarku sosai mama tace Allah maki albarka Ameen ta amsa
Mama ce tace bara naje na duba mana alala Aneesa tace laaa mama harda alala kika mana eh mama ta amsa mata Aneesa tace yauwa mama natuno yau na sawo maki awara nan ta bude jakarta taciro ta mikama mata mama tace inni sa imun habibaty
Wangale baki Aneesa tayi cikeda mamaki kana tace mama kema azumin kike?
Eh mama ta amsa mata Aneesa tace Allah karba ameen mama ta amsa mata mama tafito Aneesa kuwa na biye da ita a baya suna hira har suka isa part dinsu baba mai gadi suka shiga tare da mama bayan ta duba alalanda ke kan stove Aneesa tace mama……..
✍????by Leemat
Love U ol????????????
????????⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????⚖
Na Hannatu Dadq Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????
12
Aneesa tace mama inaso ki daukeni tamkar ke kika tsuguna kika haifeni domin kuwa nima haka na daukeku kuma nayi imani da Allah cewar bazaku taba ganin abinda zai cutar dani kuyi shiru ba kuma…..
Mama ce ta katseta ta hanyar rungumanta datayi cikeda so da kauna mama tace yarana 3 a duniya Haneef,Umar da Ababakar siddeeq kuma duka mazane Aneesa tayi fuskar kuka dariya mama tayi kana tace toh ai ban karashe ba domin kuwa daga karshe Allah ya albarkanceni da diya mace kyakkyawa mai ladabi da biyayya kuma itace yar autarsu 1 mace wato Aneesa yar mama da baba ????
Murmushi Aneesa tayi kana tace yauwa mama har naji dadi Allah barmu tare Ameen mama ta amsa
Zama sukayi a palo sunata hira har zuwa 6:30pm nan ne Aneesa ta mike tace mama bara na dauro alwala mama tace toh yar albarka shigewa tayi bathroom ta dauro alwala tafito ganin haka ya yasa mama tafita taje part din Aneesa ta dauko su fruits din ta dawo dashi part dinta tana shigowa taga Aneesa ta dauko sallaya ta shinfida a palon sannan tashiga cikin dakin mama ta dauko Al-Qur’ani mai girma nan tayita tilawarta hankali kwance har akayi kiran sallah nan tayi addu’a sannan ta rufe Qur”anin tana kokarin mikewa ne sai ganin mama tayi a gabanta dauke da tray tana smile itama Aneesar smile din ta mayar mata mama ta ajiyeshi sannan ta zauna tare sukayi budan baki wanda rabin abinda taci duk mama ce taketa bata a bakinta har suka kammala nan Aneesa ta mike taje ta kurkure bakinta tadawo tayi sallah mama itama alwalar ta dauro tazo itama tayi sallar koda suka idar karatun Qur’ani ne sukayita yi har ishaa ‘i tayi bayan sun idar da ishaa’i ne Aneesa ta gaisheda mama nan suka koma kan dinning domin cin abinci Aneesa kam cewa tayi ta koshi mama kam tace ai bata isa ba suna kan dramar ne baba mai gadi yashigo da sallamarsa
Ai kuwa Aneesa sai shagwaba tafara tana bubbuga kafafuwanta smile yayi kana yace wai waye ke tabamin yar leleta ne eh?
Cikin shagwaba Aneesa tace baaaaa mama bace wai dole sai naci abinci ba bayan nakoshiiii…..
Dariya yayi lokacinda ya iso dinning din shima y nemi wuri ya zauna nan yace a toh ai da gaskiyar mama habaa diyata kici abinci mana mama ce tace rabu da ita wai ni nataba ganin yarinya budurwa haka da gobe zan wanketa in kaita gidan mijinta ace batason cin abinci kwata2 kunyace takama Aneesa nan ta mike da niyyar barin wurin mama ce tarikota tana fadin dan Allah kici koda alala ne rusunawa aneesa tayi har kasa ta gaida baba cikeda girmamawa baba ya amsa sannan yasa mata albarka
Juyowa tayi gun mama sai Tausayi mama tabata nan ta zauna mama tayita feedin dinta aneesa ko sai kallon mama taketayi da tayi concentratin akanta ita 1 ko kulawa da baba ma batayi ba a cikin ranta tace Allah nagode maka daka hadani dasu mama wannan irin so haka ai ko yayan cikinsu ne iyakacin kulawarda zasu basu kenan hmmm….
wata ajiyar zuciya tayi wanda yabasu mama tsoro baba ne yace yar Albarka lfy kuwa Aneesa tayi murmushin yake kana tace lfy lau baba Amma a ranta tana jimamin randa za ace ta rabu dasu batasan ya rayuwarta zai kasance ba a haka dai har tasamu ta cinye kulli 1 mama ta yanko na biyun kenan Aneesa tace mama nakoshi wallahi idan ba amai kikeson inyiba kibarni haka
Mama ta dauko ruwa tabata baba ne yace toh masu diya shikenan ni an manta dani ko toh shikenan bakomai bari in taahi inyi gaba since am not welcomed here
Dariya suka hauyi gabaki dayansu kana mama tace kayi hakuri kaima sanin kanka ne idan yar leleta tana nan bana ganin kowa sai ita
Aneesa tayi smile tace su baba ana kishine?
Smile yayi kana yace eh ……. sannan kuma yace aa
Ido aneesa ta zaro kana tace toh wanne zan dauka aciki kashe mata ido daya yayi kana yace ko wanne amma banda na farko dariya sukayitayi
Aneesa ce ta mike kasancewar wayanta na ruri kuma a palo ta ajiyeshi koda ta isa palon ta dauka da sallamarta Aisha a dayan bangaren tace Sweety kinsha ruwa lfy?
Lfy lau Aneesa ta amsa hira suka hau yi sannan Aisha take sanar mata cewar an samu cigaba a store dinta sosai murna Aneesa tayi tayi godiya ga Allah sannan tace Aisha Allah barmu tare
Ameen Aisha ta amsa bayan sun dan tattauna gameda rayuwar yau da kullum ne sukayi ban kwana mamace ta iso wurin ta zauna kusa da aneesa
Aneesa tamike tana fadin mama ni zanje in kwanta barci nakeji mama tace ai kuwa yakamata kije ki kwanta toh saida safe baba yafito yace har zaki je ki kwanta eh aneesa tace toh saida safe yar Albarka kardai ki manta kiyi addu’a dai kafin ki kwanta toh baba cewar aneesa mama ta rakota har cikin part dinta kafin takoma bayan sunyiwa juna saida safe
Aneesa nashiga……….
✍????by LEEMAT
LOVE U ALL????????????
????????⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????⚖
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????