ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS???? tsintsiya muke madaurinmu 1 ????
13
Aneesa nashiga bathroom tafada tayi wanka ta dauro alwala tana fitowa tayi nafila sannan ta kwanta
A bangaren Ahraf kuwa tunda yakoma gida ya kasa samun sukuni sai tunaninta yake gashi baida numberta bare yakirata ummanshi ce tashigo part dinshi da sallamarta ashraf ya amsa bayan ta zauna ne tace son meke damunka ne yau kwata2 na lura dakai yau baka cikin hayyacinka sai faman tunane2 kake
Smile yayi na karfin hali kana yace umma lfy ta lau kawai …..
Kome yatuna ohoo
Sai kuma yayi shiru
Ummansa tace habaa son kasan bana boye maka komai pls sanar dani damuwanka
Jin kalaman ummanshi yasa jikinshi yayi sanyi nan ya gaya mata komai bai boye mata ba
Smile umma tayi kana tace toh Alhmdllh yar wani gari ce kuma ya sunanta?
Nanfa daya wai ance da shege ina ubanka……
Aahraf yace wallahi umma bansan sunanta ba kuma bansan ko daga wani gari take ba nidai abu daya nasani shine dana kaima Mus’ab ziyara ne na hadu da ita kuma tunda na ganta sai naji ta kwantamin arai amma bari zan tambayi mus’ab din sunanta da garinta
Toh son Allah taimaka Allah sa alkhairi ameen ya amsa yana smile dan yaji dadin addu’ar umminsa
Koda tafita nan fa yakoma aikinda yasamu yau shine tunani yana kan haka ne barci barawo yayi awon gaba dashi
Aneesa ce da Ashraf tareda yara 2 kyawawa mace dana miji Aneesa sai firan soyayya suke cikeda nishadi dayar yarinyar ce wacce batafi 3yrs ba tace mommy daddy zan cha ice cream smile Ashraf yayi kana yace to kuje gun kande ta kaiku kusha tashiwa sukayi suna tsalle yesssss we love u daddy sannan sukama Aneesa gwalo nan suka fice daga dakin ganin haka yasa Ashraf yin maza yaje ya rufe kofar dakin Aneesa na kallon ikon Allah yana dawowa ya janyota jikinshi Aneesa tace Habibi da tsakar ranar nan kashe mata ido yayi kana yace bakisan na rana yafi……..
Ai kafin tasamu bakin magana yariga ya hada bakinshi da nata sarrafata yake duk yabi ya kashe mata jiki yana kokarin zuge zip din rigarta ne yaji ana bubbuga kofar
Ai ba shiri ya mike domin zuwa dubawa ko wanene
Dalla cen guy tashi mana ka barni inata faman jiranka bude idonda zaiyi sai yaga mus’ab bata rai yayi yace kai amma kai banzane wallahi yanzu ina cikin soyewa nida masoyiyata acikin mafarki shine zaka wani zo ka tasheni
Dariya mus’ab yamashi sannan yace au yaushe kafara soyayya ban saniba?
Ashraf yace yau mana katuna danaje makarantarku dazu har nake cemaka nayi budurwa amma sai ka dauka wasane ko ai da gaske ne wata kyakkyawar yarinya ce na gani tamin wallahi zan iya yin komai akanta
Mus’ab yace kenen harda holewar da mukeyi zaka iya bari saboda ita?
Shiru yayi kafin yace holewar banza in dai zata aminta dani ta yarda ta aureni wallahi zan daina shirmennan
Dariya kawai mus’ab keta faman yi domin kuwa shi a tunaninsa duk shirme ne ashraf keyi
Tashiwa yayi yashiga bathroom ya watsa ruwa yafito ya shirya nan suka fita don zuwa sharholiyarsu
Toh jama’a wata irin waina Ashraf ke toyawa shida mus’ab?
✍????by Leemat
Love u all????????????
????????⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????⚖
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
Wannan page din nakine ke kadai uwa mai gyara yarta nayi godiya gareki mahaifiyata, uwa bada mama, mai kaunata farin cikina Allah kara nisan kwana Gimbiya sarautar mata MAMA HABIBA DADA KUTA AKa Maman Titiwo Allah sadaki da alkhairin duniya data lahira Ameen nagode ????????????????❤????????????????✍????
14
Shin wanene Ashraf?
Ashraf wani matashi ne maiji da kyau da naira irin tashin palonnanne wato Ajebo
Ashraf da ne daya tilo agun hamshakin mai kusdinnan wato Alhaji Sudais da matarsa Hajiya Saudat shidai Alhaji sudais dan kasuwa ne babba wanda sunarsa ta bazu a nigeria da kasashen waje ita kuwa matarsa hajia Saudat ita ba yar nigeria bace ita yar kasar egypt ce acen suka hadu lokacinda yaje kasuwancinsa kuma ya sami iyayenta nan aka bashi aurenta yaci gaba da zama acen har tsawon shekaru 12 basu samu haihuwa ba hajiya saudat ba karamin damunta abin yakeyi ba ana haka ne wata rana tace mijinta yakara aure nan ya nuna mata cewar shi baida ra ayin ajiye mace fiye da 1 dan hk tayi hkr haihuwa ta Allah ne in da rabonsu wataran zai basu
Haka dai rayuwa taci gaban ma ma auratannan 2 cikeda so da kauna abokan harkallansa sunyi2 akan ya kara aure don samun zuria amma yayi kunnen shegu saboda yanason matarshi
Kuma mutum ne mai tawakkali yayi imani wataran sai lbr wata ranar monday ce hajiya saudat ta dauki azumi ranar yini tayi tana rokon Allah har akasha ruwa Allah maji rokon bawansa ne cikin ikon Allah kuwa sai mijinta yake shaida mata cewar bazai samu dawowa a ranar ba ta dan ji ba dadi amma ta nuna masa shikenan Allah dai ya tsare mata shi aduk inda yake Ameen ya amsa ashe yana bakin kofar falon ne lokacin bude kofar yayi ita kuma lokacin ta taso da niyyar zuwa kulle kofarta tunda bazai dawo yau ba tana hawaye tana tafiya ganin mutum tsaye a kofar yana murmushi ne yasata tsaya chak
Cemata yayi kuka?
Cikin shagwaba taje ta rungumeshi tana fadin toh bakai bane ba wai bazaka dawo yau ba ta karashe maganar tana kuka……..
Rarrashinta yayi nan ya dauketa kamar baby suka shige basu tsaya ko inaba sai bedroom ya direta saman gado
Cemashi tayi muje kayi wanka kafito kaci abinci sai shikuma yace sannan inzo in kwashi gara ko ????
Kunyace ta kamata dan haka tashi tayi tafita da gudu smile yayi yace I love u wit all my hrt
Bayan yayi wanka yaci abinci nanfa suka shiga duniyar ma aurata ranar saida hajiya saudat tayita kiran sunar Ummanta da Abbanta tsabar ……..
Shikuwa nan yamata kyautar kujeran makka tsabar………????
Niko nace saikace yaune darensu na farko
Bayan sati 6 ne tafara zazzabi alhaji duk yabi ya rude koda yakaita asibiti bayan yan gwaje2 da aka yimata nan aka shaida masa cewar tana dauke da juna 2 har na tsawon sati 5 murna agun alhaji baya misaltuwa nan aka basu magunguna tun daga ranar ya hanata yin komai har Allah yasa cikinta yakai wata 5 nan ne yace su dawo nigeria dazama taji dadin jin hakan ai kuwa haka akayi
Cikinta na wata 9 kuma gashi lokacin tafiyarsu hajji yayi haka tashirya suka tafi cikin ikon Allah acen nakuda ya kamata ta haifi danta namiji kyakkyawa kamar balarabe
Koda ranar suna ta zagayo a cikin masallaci aka rada masa suna Ashraf koda lokacin dawowar yan hajji tayi ita bata dawo ba dan mijinta cewa yayi saitayi 4months tukuna kasancewar yanada gida acen cikin madina haka kuwa akayi
Tun da ta haifi Ashraf shikenan Allah bai kara bata wani ba
Don haka ne suka dauki son duniyarnan suka daurawa ashraf saidai bai bata tarbiyyarshi ba ko kadan har sai lokacinda ya cika 19yrs llkacin ne ya kammala 1st degree dinsa a oxford university dake amurka inda ya hadu da wani mai suna micheal wanda baida aikinyi daga shaye2 sai bin matan banza
Saidai shi ashraf bai taba yarda yayi hurda da matan banza ba amma yana shaye2 wannan kenan
Cigaban lbr koda suka isa club nan ya zauna saidai yau anyi2 yasha kayan maye amma sam yaki sha gaba daya ma hankalinshi ba anan yake ba
Aneesa tana cikin barci ne sai taji……….
✍????leemat
Love u so very much sweet mom ????❤????????????????
????????⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????⚖
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????