BABU SO HAUSA NOVEL

ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????

                  15

Aneesa taji kamar a zahiri cewar gata ga Ashraf suna soyayya wanda har takaisu gayin aure infact mafarkinsu iri daya dana Ashraf saidai ita babu wanda ya tasheta ita da kanta ta farka tayi addu’a sannan ta zauna tana mamakin irin wannan mafarki haka

Ta dade kafin barci barawo ya saceta

A bangaren Ashraf kuwa ranar bai sha komai a club ba har suka dawo hoton Aneesa keta masa yawo a brain dinsa

Washe gari da asubahi bayan ta idar da sallah tayita kira’a tana kan kira’ar ne taji kamar ana kuka ta danji tsoro amma ganin Al Qur’ani mai girma ne take karantawa yasa taji bata tsoron komai hasalima sai taji tasamu nutsuwa fiye da da

Cen taji kamar an bude kofa an rufe cigaba da karatunta tayi ko ajikinta bata damuba har gari ya waye nan tayi addu’a tashafa sannan tashiga bathroom tayi wanka

Karfe 7:30am tafito cikin wata riga da skirt tayi mata kyau da yar karamar gyalenta part sinsu mama tayi tana zuwa ta rusuna ta gaida baba sannan tawuce ciki nan ta gaisheda mama sannan tafito don wucewa makaranta mamace tace ga abincinki fa ki tafi dashi tunda yau bakison kici abincin a gida smile tayi kana tace mama ai kinsanni inba 10am ba ban fiya son cin abinci da safe haka ba shiyasa kuma kinga yau inada lectures 8:30am

Toh Allah taimaka kidai dauka kitafi dashi toh mama Aneesa ta amsa sannan tafito Allah bada sa’a Allah tsaremin ke Ameen aneesa ta amsa sannan baba yace toh masu diya dariya suka saka Aneesa tayi gun motocinta dake parke wata mota tashiga kirar KIA brown colour ne wato colourn jakarta,takalminta,yan kunnenta,agogon hannunta da bangul din da gyalenta sannan kuma a atamfar datasa akwai brown aciki sai kuma wayarta datasha kwalliya da brown case domin kuwa duk kayanda tasaka tomatch ne komai nashi bata saka any how dress haka motar hawanta different colours ne daidai da wayoyinta suma haka Aneesa kenan yar Presidor

Shiga tayi bayan tayi addu’a nan ta kunna wayrta takira Adama take shaida mata cewar gatanan tafe tajirata toh sai kin iso inji adama

Baba ya bude mata gate sannan yamata addu’a cikin jin dadi Aneesa tamasa goma ta arziki sannan tayi tafiyarta kaji diyar albarka

Ashraf ne a gefe cikin motarsa kirar hilux yana jiran fitowar Aneesa domin tunda garin Allah ya waye yarasa meke mashi dadi kawai fuskar aneesarshi yakeson gani wanda hakan ba karamin bama daddynshi mamaki yayiba dan yasan Ashraf bai tashiwa da wuri koda ya tambayeshi cema daddynshi yayi yau yanada appointment ne da safennan toh son Allah taimaka Allah bada sa’a Ameen ya amsa sannan yace zai wuce Ashraf kenan

Ai kuwa ganin mota tafito yasashi jan tsuka domin kuwa ba motarda aneesa tahau bane jiya har zai maida kansa kan kujera sai yaga kamar mace ce ke jan motar ai kuwa kafin kace me Aneesa tazo ta giftashi tawucewarta bashiri yatada motarshi yafara bin bayarta duk da ta lura ana binta saidai bata kawo komai a rai ba domin kuwa shima ashraf ba motarda yashiga bane jiya ba

Har ta iso unguwarsu Adama ba bata lokaci kuwa saiga Adamar tafito tashiga mota hira suke har suka isa makarantar

Parking tayi suka fito Ashraf sai binta yake da kallo ganin ta fi jiya kyau kuma ga kayan jikinta sun mata kyau wowww mashaa Allah ya furta sannan yace gaskiya gimbiyata komai nata na daban ne smile yayi sannan ya fito da wayrsa yakira Abokinshi Mus’ab

Mamaki mus’ab yayi da ashraf ya shaida masa cewar yana school dinsu ba bata lokaci ya iso gun ashraf nan ashraf ya nuna masa motarda Aneesa tashigo saidai baisan sunanta ba

Mus’ab yayita dariya kafin yace guy i don fall oooo amma bakomai nasan dolema tasoka domin kuwa kaima ajin farkonnan ne wanda yan mata ke mutuwar so

Ashraf yace shege abokina ka iya zuga mutum shiyasa nake ji dakai mus’ab yace bari ina zuwa fita yayi yaje ya sami wani guy dake kokarin shiga department dinsu Aneesa bayan sun gaisa ne yake tambatarshi time dinda zasu fito bayan first lecture 11 guy din yace masa nan ya nuna masa motar Aneesa yace kasan mai ita?
Eh guy din yace sannan yace ai wannan motar yar presidor ce yarinyar arziki mai taimakon talakawa ai tafi president kyauta????

Mus’ab yace ya sunanta nan fa yace ni bansan sunanta ba domin kuwa kowa da yar presidor yake kiranta dukda batason sunar amma ba yadda ta iya da mutane sannan wasu kuma suna kiranta da kinfi president kyauta

Ok nagode sai anjima guy din yace amma lfy kake tambaya akanta mus’ab yace lfy lau kawai tamin ne guy dinne yace tabbbbb

Lallai kam dama kabar wahalar da kanka domin kuwa batada lokacin samari barta da karatunta mus”ab yace nagode guy sai anjima ok ooo nan yajuyo yazo yashiga motar ashraf

Ya kwashe komai ya gayawa ashraf ajiyar zuciya ashraf yayi kana yace indai wannan ne badamuwa

Nan mus ab yace inajin yunwa fa guy smile ashraf yayi sannan ya tada motar suka fito sai gidansu Ashraf da shigarsu part dinshi sukayi bayan sun shiga ciki kan dinning mus’ab yanufa shikuwa ashraf bedroom yawuce domin sake yin wanka

Dashigarsa bayan ya rage kaya ya fsda bathroom ya sakeyin wanka yafi 30mins sannan yafito

Wata hadaddiyar shadda yasa mai tsada ga kyau brown colour hulama brown takalmi brown yana shirin yana smile saida yafi 1hour kafin ya kammala

bayan ya kammala ne ya furta komai namu colour daya gimbiya

Sannan yafito kamshi yakeyi kamar wani sabon ango mus’ab da har yafara gajiya da jiranshi ne yamike don shiga dakin yaga ko me ya tsayar da ashraf har yanzu

Mutuwar tsaye yayi ganin yanda ashraf yasha kwalliya kai ka rantse zai angwance ne yau

Har ashraf ya iso gabanshi bai saniba clappin yayi wanda ya dawo da mus”ab hayyacinshi dan tunda yake da ashraf bai taba ganin ashraf yayi mashi kyau irinna yau ba

Amma wallahi baba ka hadu kai dolenema yarinyarnan tasoka ko wacece ita smile ashraf yayi sannan yace mashi ka koshi koh? Eh yace sannan suka fito mus’ab sai faman zuba yaketayi kamar fanfo shiko ashraf sai smile yake

Gun wata hadaddiyar mota ya nufa kirar Hilanda brown colour ce itama mus’ab yabishi da kallo alamar tuhuma smile ashraf yayi kana yace inasonta ne shiyasa komai namu nake son ya zama daya

Mus’ab bai tankashi ba har suka iso makarantar Ashraf ya dubi agogonda ke hannunshi ta gold yaga 10:20 nan yace wai mus’ab yau bakada lectures ne

Mus ab yace ahhh dole kacimin fuska kawai kacemin in wuce kar na ga beb dinka kawai kabar yimin kwana2

Ashraf yace ba hk bane na sanka ne dason kyawawan yan mata mus’ab yace toh wane darene jemage bai ganiba a duniya?

Dallah cen mallam ni nayi tafiyata nan yafito yanata banbanmi cewar tun ba akai ko inaba beb na neman rabasu dan hk yazama dole yayi maganinta

11 dot mutane suka fara fitowa cen saiga Su Aneesa sun fito itada Adama fitowa yayi lokacinda suka karaso gun motar Aneesa sallama yamasu suka amsa Aneesa taje tashige mota Adama ko ko motsi ta kasayi kasancewar ta folama kyawun Ashraf ganin taki shigowa ne yasa Aneesa yin horn Adama tace Ashraf ya kk lfy lau ya amsa mata nan tace mashi tana zuwa zasuci abinci ne toh shine dan rowa kawarki kota kirani koh?

Aneesa ta sauke glass tace wai me kk jirane nifa zan fara….

✍????by leemat

Godiya agareku masoya Allah bar kauna ????????????
????????‍⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????‍⚖
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button