ANEESA YAR PRESIDENT HAUSA NOVEL

UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????
16
Koh me ta tuno oho sai kuma tayi shiru Ashraf ne yace me zaki fara eh gimbiya smile tayi batareda tace dashi uffan ba
Adama tace muna zuwa dan Allah kabamu 5mins bakomai yace sannan yace ina jiranku a acen inda naganku jiya ok tace mai sannan tabude tashiga shima juyawa yayi yai gaba gindin bishiyar mangoro ya zauna yana jiransu
Abinci sukeci hankali kwance Ashraf sai bin Aneesa yake da kallo kasancewar suna fuskantar juna ne wowwww yafada
Kana yace komai nata na burgeni kama daga cin abincinta,maganarta,nutsuwarta hmmmm komai ma nata abin burgewa ne
Aneesa ce takai chokali baki daga idonda zatayi sai suka hadu dana Ashraf ai kuwa nan da nan ta rude Adama ta juya ganin Ashraf na smile yasa itama tayi smile sannan taci gaba dacin abinci har suka kammala cin abinci Aneesa bata kuma dago kanta ba gudun kar su hade dana Ashraf
Suna fitowa bayan sun iso gurin da yake zaune nan Adama ta zauna Aneesa kam cewa tayi sai kin shigo Adama tace habaa Mana kizo muyi hira da abokinmu na jiya mana
Ashraf yace shawaranku nazo nema akan wata santaleliyar budurwarda na gaya maku jiya sannan yace yauwa gimbiya jiya wata shawara ma kika ban?
Smile Anesa tayi sannan tazo ta zauna Alhamdulillahi ya fada Aneesa tace ka sanar mata sai Ashraf yace yauwa wato tsabar rowa ko bismillah ma babu ko?
Kunya Aneesa taji dan yakirata da mai rowa Adama ce tacw ai kuwa bata rowa domin kuwa duk wanda yasan kinfi president kyauta dole ……
Aneesa tasa hannu ta rufe mata baki ganin haka yasa Ashraf smile sannan yace woww sunan gimbiyar kenan koh kinfi presidor kyauta wowwww
Sai gashi ni tamin rowa domin kuwa harda wani sauri2 taketayi tana katon loma wai dan kar yarage ince zan ci Aneesa tayi maza tace Allah Ashraf bansan sharri fa
Yanda tayi maganar ya burge ashraf lumshe ido yayi na seconni kafin ya bude sannan yace to yanzu ga abinda zai faru zan fara learning soyayya da daya daga cikinku in gani ko zan iya apprching din masoyiyata Adama tace gud thinking Aneesa kam tace bad idea hakan baiyi ba sam
Ashraf yace ai na sati biyu ne kacal kinko ga kafin nan nasamu ilmi akan soyayya sosai Adama tace haka ne Ashraf yace toh da wace zan yi soyayyar sati biyun
Aneesa tace da Adama mana domin kuwa ita ta saba da yin hira Adama tace gaskiya kam sannan kuma kafin hakan saina sanar wa masoyina na gaskiya tukuna Ashraf yace toh ita gimbiya fa batada saurayi ne
Adama tace ai ita bata kula mata ma bare samari nima haduwarmu daga Allah ne domin kuwa mutane da dama sunata mamakin yanda akayi muka zama aminan juna
Ka ganta nan barta da books dinta kawai kwanakin baya ma da dan sarkin Zazzau ya kawo ziyara nan makarantar yana yin arba da ita sai ya fola amma koda yayi mata magana bata kulashi ba cemashi tayi ba soyayya yakawota ba karatu tazo yi kuma kasan me?
Ashraf da zuciyarsa ke faman yimasa zafi kasancewar abinda Adama ke fada kada kai kawai yayi alamun aa sai kin fada dinnan
Ai kuwa adama taci gaba da fadin zo kaga yanda yan mata keta mutuwa akan prince amma wai sai kawata ta basar daahi
Haka yayanta ya kawo mata ziyara shida abokinshi wato dan sarkin makka shima ya fola mata amma ita ko ajikinta in takaita maka resently yaron dangote yazo shima wai acewarsa ya hadu da ita ne a kasar india ai kuwa har nigeria yabiyota amma taki amincewa dashi
Ashraf ne yayi ajiyar zuciya wanda yasa dukkansu yimai kallon tambaya ai kuwa sai ya wayance yace lallai kam ai dole tayita rejectin din su domin kuwa Allah baiyi dasu za ayi ba
Aneesa tace oh harma kasan ko dawa za ayi koh?
Smile yayi kana yace inshaa Allahu dani za ayi dariya ce ta subucema Aneesa jin hakan daga bakin Aahraf dariya take shiko sai faman smile yake acikin zuciyarshi kuwa yana addu’a Allah bashi ita Allah mallaka masa gimbiya niko nace Ameen
Saida tayi mai isarta sannan tace wait a moment wai kana nufin kai ta nunoshi da hannu Ashraf yace yes nifa Ashraf nan Aneesa tace lallai kam Ashraf yace idan baki yarda ba toh kiyimin exam yanzu2 nan idan har naci toh yazama dole kiyi soyayya dani
Adama tace aa tayi maka tambaya dai idan har kaci toh sai tayi soyayya dakai na sati 2 Aneesa tace ni?
Soyayya?
Da Ashraf?
Har na tsawon sati biyu?
Hmmmmm lallai ma kam ai hakan ma bamai yiyuwa bane
Adama tace habaa kawata wallahi banajin dadin ganinki ke 1 pls ki koyi yanda ake soyayya koda na sati 1 ne in yaso ni zan cikasa na sati 1
Ashraf yace gud gimbiya kin yarda ?
Aneesa tayi shiru nadan seconni kafin tace eh na yarda
Ashraf yace toh me tambayarki?
Aneesa tace tambayata ta farko itace
……. ………….
✍????by Leemat
Love u ol????????????
????????⚖ANEESA YAR PRESIDENT????????⚖
Na Hannatu Dada Kuta
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
Wannan page din nakune yan group din HAUSA NOVELS ina mai jinjina agareku akan kaunarda kuke mani da addu’arku agreni nagode Allah bar kauna ana tare????
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELS????
17
Aneesa tace tambayata ta farko itace ya sunana?
Na biyu me nake karantawa?
Na uku………
Sai kuma tayi shiru Ashraf yace ina jinki gimbiya na ukun fa sai tace ba yau ba amma biyunnan yanxu nakeso kabani amsarsu
Ashraf yayi shiru cen yace a gaskiya bansan sunanki ba kuma bansan abinda kk karantawa ba
Smile Aneesa tayi kafin tace ai dama nasan za a rina tunda naji kana kirana da gimbiya sannan kana kiran Adama da sunanta nasan baka san sunana ba
Shikenan ka fadi dan haka babu zancen soyay…….. ai Ashraf bai bari ta karasa ba ya katseta da cewar dan Allah karkimin haka Angel
Bani 10mins zan shiga zuciyarki inyi binciken sunanki idan har ban fadeta daidai ba toh na yarda babu love tsakanina dake
Aneesa tace ok ooo shiga ai kuwa nan Ashraf yashiga sake2 yana tunanin wani suna ne zaiyi matching da angel dinshi
Aneesa ko sai smile take dan tasan da kyar yasan sunanta
Ganin ya kasa samun sunarda ya dace da ita ne yasashi hkr kana yace a gaskiya bansan sunanda yayi matching dake ba amma kibani dama in kira sunaye 3 kacal idan babu naki aciki shikenan
Aneesa tace aa ban yarda ba Adama ce tace haba kawa ki bashi dama mana sunaye 3 fa kacal ok ok ok na yarda cewar Aneesa
Nan yafara da Ummul khairi noooo
Yakuma cewa Badariyya hahahahah nooooo
Remain only 1 guy cewar Aneesa tana smile
Shiru ashraf yayi kirjinshi na bugun 3 uku
Aneesa tace oya now d last one
Addu’a ashraf yafarayi yana rokon Allah yasa na ukun yazama sunanta
Na ukun mana malam inji Aneesa shiru Aahraf yayi dan harga Allah ya rude sai tsoron fadan na ukun yakeyi kar ya kasance ba dai2 ba amma bakomai na barma Allah zabina
Nan ya furta ANEESA………
Gaban Aneesar ne ya buga dan bata taba tunanin zai fada dai2 ba shiko Ashraf tsabar fargaba har rumtse ido yayi dan kar yaga ta masa dariya akan bai fada dai2 ba sannan yana tsoron rasa Angel dinshi kawai saboda baisan sunanta ba hakan yasa yaki bude idanuwanshi sai Addu’a yaketa faman yi
Adama kuwa cewa tayi Alhmdllh Aneesa shikenan daga yau sai soyayya jin hakan ne yasa Aahraf bude idanuwanshi da ya rufesu saboda tsoro
Ai kuwa ganin Aneesa tayi tsuru2 da ido ne yasashi ajiyar zuciya Adama kuwa tace shikenan soyayya dole kallon Aneesa yakuma yi kana yace gimbiya naci? Adama tayi saurin cewa eh mana Ashraf congratulations ka cinki sunan dai2 sunanta kenan Aneesa