BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Muna shirin futa daga gidan wayar Munnu tayi k’ara ts dauka a nutse tare da kashe muryar ta, kasa kunne nayi cike da mamaki jin tana ambatar sunan Shamsu. Ni da Mimi muka kalli juna. Ji mu kayi tana fadin”Eh ka shigo da motar yanzu zamu futo.” Sukayi sallama, dukaninmu muka kalleta cike da mamaki nace”Munnu yaushe Shamsu ya dawo kuka kuma jone wa.” Murmushi tayi tace” shekaran jiya ya dawo da k’arfin sa, Wallahi aurena zai yi domin aranar da ya dawo ma Baban shi yazo gurin Babanmu baku ga kayan da ya kawo mun ba, wannan hayaniyar da muke ciki ce ta hana ni fada muku.”
Ni da Mimi muka Ce”Toum Allah ya sanya alkairi lallai alk’awarin Allah ya cika. ” dariya Munnu tayi cike da farin ciki muka futa daga gidan. Samari na bakin titi suka bimu da kallo kamar wasu mayu.
Wata had’adadiyar mota na hango a fake gefan titi Shamsu na zaune a mazaunin dravar tare da wani Wanda ban gano fuskar shi na, suna sanye da wata masifaffaiyar shadda wagambari hade da hula damanga sunyi kyau har sun gaji. Ganin zuwan mu gurin yasa Shamsu futowa da sauri ya bude wa tauratowar shi motar yana fadin” Girman kujerar ki ne.” Hararasa nayi tare da tab’e bakina nace”Haji Shamsu Ashe zaka dawo ai na dauka muma yaudarar tazo kanmu.” Dariya yayi yace.” Inaaa!! Baby Asma, Ai Munnubiya ta daban ce cikin mata, tab’e bakina nayi nace”Allah yasa da gaske kake.”
Tunda na fara magana abokin Shamsu yake kallona ina kallonsa ta wutsiyar ido tsaki naja a fili na tsani kallo wallahi.
Munnu ta shiga ta zauna Mimi ta zauna nima nashiga sannan Shamsu ya koma gurin zaman shi hade da kunna motar muka tafi.
Shamsu sai janmu da hira yake yana fad’in”Ai duk naji labari lokacin da na tafi har daku ake cewa dama yaudarar Munnu nake yi humm yanzu Asma baby kina ganin zan aikata haka kuwa.”
Nace”sosai ma kuwa Shamsu namiji ne fa kai hunm halin Ku sai Ku.”Abokinshi ya juyo yana kallona tare da sakin murmushi yace.” Baby Asma wasu mazan ne suka bata wasu amma abokina da gaske yake.” Tab’e bakina nayi nace” muna da labarin fa duk ‘yan Matan da ya yaudara sun kai goma. ” Shamsu ya rike baki yana dariya tare da fadin” duk sharri ne wallahi, karya suke min.” Mimi tace”Babu sharri nan gaskiya ce mu dai don Allah kar ka kara guduwa domin wancan karon sai da mukayi jiyyar ta” suka kwashe da dariya shi da abokinsa.
Munnu sai mintsina take wai in daina surutan da nake yi ina jinta na kiyin shiru.
Lokacin da muka Isa guri ya soma cika sosai aka kawata gurin gurin malamai daban da iyayen yara wajan dalibai daban, muma wajan mu daban wajan manyan baki daban .. Masu hotona da vedio baza su kirgu ba, saboda ko wacce da nata,muma mun dauki namu can muka tadda shi, MA kad’a sun fi su biyar suna gefe suna jiyar taro ya watse a fara shagali. Ko wane class da gruop d’insu da kuma irin kalar ankon su, ko wacce tana wace wannan.
Mai girma principal ya bude taro da addu’a tare da yi mana nasiha sannan yayi wa ‘yan matan da aka kusa bikinsu a cikinmu addu’ar zaman lafiya Wanda basu da mazaje Allah ya kawo musu, hakanan Wanda suke shirin cigaba da karatu Allah ya bada sa’a.
Haka Malamai suka dinga mik’ewa suna jawabi tare da addu’a, taro ya tashi guri ya hautsine kowa da ta wagar mutanan shi, da kawayen shi sai d’aukar hoto ake hade da vidio,
Ina gefe tare da jama’a ta domin wasu ma ranar na fara ganinsu duk ya wancin su maza ne, tuni na cire hijabina ina yawo yanda na gadama ‘yan ajimu sai jana suke dole sai munyi hoto duk inda na sanya kafa abokin Shamsu nan yake sauke tasa ya zame min jele, haka na dinga shiga cikin abokan da samarin ‘yan ajinmu muna hoto wasu nayi da waya wasu nayi da Camera man. Abun mamaki ni kadai jama’a suke ja lallai sai sunyi hoto dani, haka Alina ma duk gabar da muke da ita sai da tazo ta jani cikin a bokanta maza da mata mukayi hoto wasu daga cikinsu na fiddo wayoyinsa nayi min.
Mimi ce tazo ta jawo ni da k’arfi tana fadin” meye haka kike yi don Allah ki daina ratsa maza kina shiga tsakiyar su baki San suba
Fuzge hannu nayi INA fadin “Kinga Mimi yau rana daya ce daga ita babu wata ki k’yaleni.” Mimi ya rabu dani ta koma gurin Munnu da sauraynta
Duk ankon da mukayi sai da muka sanya su Shadda ce karshen sawa. Waiiiii!!! Fitina! Lokacin Dana futo cikin shadar idanun jama’a kamar ya cinye ni, ni kaina sai bayan na futo a haka Nazo ina da na sani dinkin fitat ne iya cibiya Sam rigar bata da hannu gashi ta matse ni, siket din yayi d’an, kwankwaso na kamar zasu yi magana da kyar nake cire k’afa ta saboda yanda ya matse ni.
Tuni suka yo kaina suna ihu!!! Wani Dj ya saki wak’arnan ta Hamusu brekar wato shimfidar fuska Filin na nufa sauran k’awayenmu suka rufa min baya, rawa sosai na dinga wakokin gwanja kamar ni na rera su mussaman wak’ar shi ta d’akin bak’uwa dudu bak’ar ashana ai ina bala’in son wak’ar nan na zage ina rawa tare da sauran ‘yan ajinmu Mimi ma da Munnu sun shigo filin ana yi da su.
Alina ce tazo ta ja hannuna wai inzo muyi sallama da abokanta, muka nufi bakin get, kamar walkiya naga gilmawar motar guy nan ta futa daga gurin. Abunda yasa na gane sunan shi dake bayan motar kuma na shiga cikin kusan sau biyu. Mamaki ne ya kama ni, mutumin da baya gari me ya kawo shi gurin nan.
Sama-sama mukayi sallama dasu na koma ciki ina tab’e bakina.
System d’in shi a kan cin yar shi yana dubawa Anthony na gefan shi yana waya cikin yaran na chana.
Sak’o ne ya shigo yana dubawa yaga rambow ne, pictures ya fara gani kusan guda Dari suna shigowa, da sauri ya bude yana dubawa, ji yayi zaman gurin ya gagare shi a sabili da abunda ya gani cikin loptop din shi, babu shiri ya mik’e da sauri ya shige wani had’addan bedroom hade da sanyawa kofar key ya zauna gefen bed hannu na rawa yake duba hotonan wani irin gum! Yana tsatstsafo masa a saman goshi
3/NOVEMBER/2019
[11/4, 11:56 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO
Mallakar_BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.
39
Yarinyar yake gani cikin maza ko ta ina, ga sassan jikinta a bud’e ko duk motsin da zata yi kana ganin saman breast dinta ga sunan a waje hankalinsa bai k’ara Tashi ba sai inda yaga ta shiga filin rawa tana juyi ana mata watsin kudi, wani uban ihu!! Ya kurma hade da jefar da loptop din ta fad’i kasa ta gangara can bakin kofa, mike wa yayi a zafafe! Ya kai wa bango duka da hannunshi!! “Ni wannan yarinyar zata tozar ta. ? Da k’arfi ya fad’i maganar, kaiwa yake yana kawo wa a dakin, a fusace! Yaje ya dauki wayar sa, yana lalubar Mimi, bugun duniya yayi tak’i shiga, jefar da wayar yayi ta fad’i kasa, dafe kansa yayi dake mugun sara masa, fuskar guy nan kawai yake hangowa Wanda yake nanikar yarinyar duk inda ta sanya gaba shine ya fi kowa zak’ewa, shifa idan ba idonshi ne yayi mishi gizo ba sai yace kamar yaga ya rungume ta, wani irin ihu ya kurma!!! Hade da sanya hannunsa biyun yana dukan katifar dake kam bed din sai kace wani mahaukaci, da sauri Anthony ya shigo domin yaji ihu!! Cin karo yayi da lopot bakin kofa a kife, cike da mamaki ya sunkuya ya dauko ta yana gyarawa, k’araso wa nan ma yaga wayar sa a jefe.. Ajiye loptp din yayi kusa dashi ya dauki wayar yana dubawa dake mai hade da batir ce kunna wayar yayi ta kama abunka da abu matsada nan take ta kama.
Zama yayi kusa dashi cikin harshen turanci yake tambayar sa.” Dago kamshi Yayi yana kallonsa da idanunsa Wanda suka kad’a sukayi mugun ja!! Hannu ya mik’a masa alamun ya bashi wayar, da sauri Anthony ya mik’a masa wayar, Numbar Mimi ya kara kira is switch up, cikin sauri ya nemo numbar Rambo, bugun farko ya dauka, bai saurari maganar da yake masa ba, yace.” A ina guy nan yake? I wiil kill you!!!.” Rambo ya tsorata jin muryar Oban gidan shi, na wani irin rawa!! Yace. ” Sir ban gan……….kafin ya karasa maganar ya katse shi cikin wata irin razananniyar tsawa yace.” Rambo!! Ni kake fad’awa baka gane ba, Dan ubanka me ka turo min Yanzu.”!!! Rambo yace.” Sorry sir Wallahi ban San dai a ina yake ba, a tare dai suka zo gurin cikin mota…. Yace.” Kafin safiya ka bunkito min a wani guri ya ke shi Dan gidan uban waye, sai na kashe shi.”!!!!! Rambo yace.” An gama sir insha Allah… Katse wayar yayi yana wani irin haki!