BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Shuru tayi daga bisani tace”Bari in yi masa waya jiya na fad’a masa zamu je asibiti dake yace.” Babu matsala amma yanzu nasan babu abunda zai ce tunda yasan Mujahid din. ” Shiru nayi ina kallonta na dauki wayarta tana kiran sa, ina ji sai da tayi ringing sai biyu ana ukun ya d’aga muryar da da alamun bacci da gajiya naji yana fad’in”My wife kin tashi Lafiya .”? Mimi tace.” Lafiya Lou Alhmdullahi nayi ta kiran wayar ka, tun d’azu baka dauka ba.”
A hankali yace.” Bacci nake Momy nayi aiki na gaji.”
Mimi tace.” Dama Asma’u ce tace ko Dector Mujahid za muyi wa magana tunda likita ne ba sai munje asibiti ba.”

Tunda Mimi ta fara magana naji kamar in tashi in fuzge wayar daga hannunta in kwad’a mata mari, Mimi wata irin sukuwa ce da bata da wayo.

Nashi b’angaran kuwa Mik’ewa yayi zumbur ya wani hade fuskar sa tam! Yace.” Bani Asma’u muyi magana da ita.”

Wayar ta mik’o mun da sauri na bi hannunta da kallo, Idanun kakar shi ya sanya na karb’i wayar raina a b’ace.!

A hasale yace.” Ke kar ki kuskura ki gayyato min wani gardi cikin gidana, wai da sunan yazo duba wife dina, saboda rashin hankali irin naki. Wallahi sai na b’ata miki rai, mutukar kika shigo min da saurayin ki gida, ki kaita Asibiti a duba ta ko nawa ne a kashe amma ban yarda da wannan iskan cin ba.”!!

Shuru nayi INA saura shi yanda yake wani magana a zafafe nace k’ila da yana kusa duka na zai yi.

“Kinji ko baki ji ba.”! Yafad’a cikin tsawa! Raina ya b’aci sosai amma ganin granny dake zaune idanunta a kaina yasa nace ” Naji.” Tsaki yaja ya kashe wayar sa.

Mimi ta karb’i wayar jikinta a salube domin da ita da granny din duk sunji irin tsawar da yake buga min.

Granny tace”Rabu dashi don Allah kinji Ina ce shi Mujahid din abokinsa ne kuma makocin sa, ne don zai taimaki iyalinsa sai ya hana kan wane dalili.”?

Tace ‘kira shi a wayar yazo ya duba ta Allah yasa bai futa aiki ba.” Nace”A’a tunda yace kar ayi to a barshi granny kibar maganar Mimi ta tashi kawai muje a sibiti kamar yanda ya fad’a.”

K’wafa tayi tace”Sai kuje Allah ya tsare nasan dai ta tsuniyar gizo bata wuce koki Allah ya raba Lafiya sai kun dawo.”
Ta fadi maganar tana gyara zaman ta cikin kujera.

Abun mamaki muna futa sai ga motar Mujahid ya futo, tsaf cikin shirin futa aiki.
Da sauri ya tsayar da motar kusa damu, fuskarsa a sake ya leko da kansa yana yi min wani irin kallo na so yace.” Me yasa baki fada min zaki zo ba.”?

Murmushi nayi kurrum, dauke kansa yayi ya kalli Mimi tare da fad’in”Madam yane da’alama babu Lafiya domin ga alamu nan na gani.”

Nace”Aikuwa asibiti zamu je.” Murmushi yayi yace.” Shine baki Sanar da ni, ba, Ku shigo muje.” Nace”A’a kaje kurrum.” Fuskarsa ya b’ata yana kallona yace.” Bana son gaddama Asma’u don Allah Ku shigo mu tafi.”

Mimi da tsayuwa gurin ta gagare ta saboda jiri ta bude motar da sauri ta shiga, kallon ta. Nayi ina girgiza kaina, saboda kar ya fuskanci wani Abu yasa na bude motar na shiga na zauna kusa da ita yaja motar muka tafi

Rambo da doh da suke tsaye suna kallon duk abunda yake faruwa suka koma gurin zaman su, dama sun taso ne saboda su cika umarnin ogan su.

Rambo ya dauki wayarsa ya fara Neman numbar ogan shi. Bugu guda ya dauka, inda yake akwai hayaniyar mutane yasa yace da Rambo ya kashe wayar zai kira shi anjima Rambo ya kashe wayar kamar yanda ya fad’a, doh yace.” Tunda ka kira zaka yi masa bayani ya kawo uziri shikkenan nasan ko kayi masa baya ni daga baya zai gamsu, Rambo yace.” Ni tsoron fad’an mutumin nake ji, akwai abunda na fuskanta game dashi da yarinyar nan.” Doh yace.” Nima haka Asma’u yana masifar sonta, Allah bai kaddara matar shi bace.” Rambo da doh-doh suka dinga gulmar ogan nasu.

Asibitin nasarawa muka nufa, ba tare da b’ata lokoci ba, Mujahid ya sanya nurse ta dauki fitsarin Mimi a wata ‘yar kwalba domin auna shi, muna zaune a ofis din sa, Sam yak’i duba marasa Lafiya wai lallai sai ya sallame mu, Kusan mintuna talatin sai gata ta shigo fuskarta a sake tace.” Dr sakamako ya nuna positive tana dauke da ciki na sati biyu.” Dr Mujahid ya saki murmushi yace.” Alhmdullahi dama abunda nake tsammani kenan. “
Nurse ta futa tana ‘yar dariya, ni da Mimi kuwa kallon juna muke yi, nace “Mimi Allah ya sauke ki lafiya.”
Gani nayi idonta yayi rau-rau za ta fara kuka, saurin dauke kaina nayi daga kanta.

Mujahid kuwa dariya yake mata yana tsokanar ta, wai ko ta soma tunanin ranar haihuwa ne, ita dai bata ce komai ba.
Wayarsa ya dauka yana fadin”Ni zan fara yiwa mutumina albishir sai ya fara kiran wayar Amjadu, gabana ne ya fad’i nasan wata masifar ce,tunda mutumin nan yace babu ruwan sa, dani kar in kara shiga harkar shi, ya nuna baya so Dr ya duba mishi mata. Shuru dai nayi kawai INA l sauraron abunda zai biyo baya.

Mujahid da dariyar sa suka gaisa dashi, naji yana tambayar sa gida da sauran mak’otan sa, yace kowa Lafiya Lou sannan yace.” Dama na kira ne ka bani gurin albishir. ” yana dariya ya fad’i. Maganar. Sam bai kawo komai cikin ransa ba, kuma bai taba tsammanin za su bujurewa umarnin sa ba yace.” Kome kake so zan baka.”
Yace.” Madam na dauke da ciki insha Allah ka kusa zama dady yanzu na sanya aka duba ta.” Wani irin nauyi yaji a kansa, lokacin da Mujahid yake wannan maganar, Mimi na dauke da cikinsa, har yaushe daran yayi balle gari ya waye, dududu sau nawa ya kwanta da ita har ta dauki cikinsa. ? Shuru yayi Mujahid yace.” Kayi shiru ko baka murna ne.”

Da sauri yace.” Wane ni, kawai ina mamakin hukuncin Allah ne, nagode K’warai Aboki bani Madam din.” Mujahid yace.” Babu godiya a tsakaninmu domun mun zama daya dakai ina fatan alkarmu dakai ta dore har a bada.”

Mimi ya mik’awa wayar yana fadin “Ga mijin ki za kuyi magana dashi Mimi ta karb’i wayar jikinta a mace tunda akace tana da ciki tayi lak’was.
Muryarsa sama-sama naji yana fadin”Ya jikin naki.”?
“Bakinta na rawa tace” Da sauk’i. “
“OK Allah ya sawake ki kula da kanki.” Abunda yace kenan ya kashe wayar sa. Mimi ta mik’awa Dr wayar jikinta duk babu k’wari na dauka ma zai yi mata masifa sai naga a kasin haka, ni kaina banji dadin yanda ya ki nuna kulawar shi kan Mimi ba, ko wane namiji akai mishi albishir da matar shi na da ciki yana sakewa yayi ta murna, amma shi magana a cunkushe, Itama na lura bata ji dadin abunda yayi ba.

Dr Mujahid shine ya mai damu gida yana bayan ya hadawa Mimi magunguna dole yace ta zauna ta samu Hutu cikin ya danyi k’wari sannan.

Granny na zaune ita kadai a parlor tana kallo muna shigowa tace “Naji dadin dawowar Ku da ina zaune ni kadai kamar wata mayya, Dariya nayi na zauna kusa da ita cikin gajiya tace.” Ina fatan dai komai lafiya nasan dai ciki ne da ita.”

‘Yar Dariya nayi nace”Eh ciki gareta Dr ya bata magungunan Karin jini kuma ta kula sosai da jikinta.”

Wani irin farin ciki naga granny tana yi sai washe baki take yi tana fadin”Allah na gode maka ‘yar nan ubangji Allah ya sauke ki lafiya naji dadin wannan al’amari dole zama ya kama ni a gidan.”

Tausayi tsohuwar ta bani ganin yanda take murna da farin ciki. Na kalli Mimi wacce take ta b’oye k’walla ko ta mecece oho mata.

Bayan sallah azhar nayi musu sallama babu yanda basu yi dani ba kan in zauna in ci abunci naki zama.
Ko da na koma gida Umma har ta sauke nata,zama nayi rumfar ta ina ci muna hira nan nake fada mata Mimi ciki gareta, itama murna take sosai har da ‘yar kwallar ta.
Ni dai mamaki nake ko kwallar me suke yi oho.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button