BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Shi ko Amjadu gida ya koma lokacin sai da ya kara Wanka ya futo daure da towol a jikinsa gefan gado ya zaune cikin dauriya domin bai gama zubar da sperm din nasa gaba ga daya ba, tun da suka had’u da yarinyar sha’awa take taso masa akai-akai yanzu haka mamar shi daure wa kawai take, Hibbah tayi masa wasa sosai yanda zai gamsu amma ji yake idan ba sex yayi ba zai samu nutsuwa ba, baya bukatar kowa a lokacin sai Yarinyar ko meye dalili oho.
Shine abunda yasa ya tsallake Hibbah ba tare da ya biya mata bukatar ta ba saboda baya cikin nutsuwar sa.
Stytem d’insa ce a kan cinyar sa, suna magana da Anthony, sai wajan k’arfe daya da rabi ya kwanta.


Da shiri zuwa karb’o din kunan mu muka tashi, amma sai mun fara zuwa gurin saloon tukkuna, ni da Mimi sama-sama muke yi domin har yanzu tak’i sakin jikinta nice ma mai k’okarin yi mata magana, tana amsawa babu yabo babu fallasa.

Ina zaune gefan katifar mu ina shafa mai Mimi na band’aki tana Wanka naji kakar wayar ta. Kallon wayar nayi ba tare da na dauka ba, abunda na gani an rubuta ya bani mamaki My heart beat da sauri na dauki wayar ina dubawa, gabana na fad’uwa numbar nake bi kamar ina karantawa kamar wata shashasha, tabbas shine, maganar ta sub’e min daga bakina, katsewa wayar tayi ko minti guda bai ba ya k’ara kira.
Naji kamar in dauka wata zuciyar tace min kar ki dauka babu ruwan ki. Ji nayi bazan iya hak’ura ba dannawa nayi tare da aje wayar kan katifa bayan na bude muryar.

Muryar shi naji mai cike da amo gami da sauti yayi sallama. Gabana ya tsananta fad’uwa
“Hello momyna kina juna” naji ya fada murya a lankwashe.. Kamar in kashe wayar sai dai na fasa,
Wannan murmushin nasa naji Yayi yace.” Ku kuna tare da ‘yar Uwar ki tayi miki kwarjini kin sa yin magana, domin na lura tsoron ta kike ji.” Shiru babu amsa, yace.” Ok Momy hope kin tashi lafiya domin itace babbar abun tambaya a gare ni. Yawwa bayan haka kuma INA son in fad’a miki zan je Chana yau insha Allah kiyi wa d’anki addu’a.” Cikin taushin harshe yake maganar. ” k’it!! Naji wayar ta tsinke, kura mata ido kawai nayi ina kallo Tare da tunanin maganganun da ya fada, Mimi lafiyar ta abun tambaya ce a gare shi, wato ya manta dani tunda ya gama latse ni ya San wacece ni, yanzu kuma Mimi yake so ya yaudara, Sam! Yanzu na dawo daga rakiyar guy nan.
Man shafawar na jefar kasa kwanciya nayi kan katifar wani irin Abu yazo ya tsaya min a mak’ogwaro na, lokaci guda Naji ruwan hawaye ya cika idona, k’okarin mai dasu nake inaaa!! Sai da suka zubo, hannu NASA na goge su da sauri domin kar ta shigo ta gani tunani nake yays za’ayi na hana Mimi kula shi, domin na lura tayi mugun nisa a gurin son shi.
Mimi ta shigo da sauri tana fad’in”Asma’u goma da rabi tayi kin ga har rana ta sauko k’asa.” Nace” ni ai na gama ke nake jira.” Kayan ta ta dauko tana sanyawa cikin sauri. Ni kuma na mik’e na futa daga d’akin.

Sai da mukaje saloon sannan muka karb’o d’in kunanmu sunyi bala’in kyau sosai sun matse ni dama haka nake so ko ina ya futo zam!zam! Dake Allah yayi min yalwar gashin kai bakikirin dashi, sai ya kara mik’ewa sosai da a ka gyara shi, abunda be dame ni ba kenan kwalliya da gashi amma gobe dole in tsula tsiyata son raina
Gidan aunt Hauwa muka wuce, muka tarar tayi bakuwa kawarta ce aunt Zainab tun ta k’uruciya nan muka zauna muna kallo muna hira aunt na soyo mana wainar fulawa wacce taji kwai da yaji me dad’i aikuwa na samu abunda nake so tuni na zage ina ci.

NTA HAUSA muna tsaka da kallon wani najeria film kawai suka katse tare da nuno Amjadu a filin jirgi lokacin yana k’okarin hawa matattakalar jirgi ya tsaya yana magana da wani d’an jarida, tsakanin ni da Mimi ban San Wanda yafi shiga d’imuwa ba, lokaci guda naji wainar da nake fi ta fuce min daga rai duk dadin ta kuwa.
Yana sanye da wasu uban suit blue and white hade da necktie d’insa hannunsa daure da wani irin agogo na zallahr fata sai blue sai shek’i yake, k’afar sa sanye da takalmi rufaffafe black sai shaining yake, hannunsa rike da irin jakar nan ta matafiya.
Dan jarida bayan sun gama magana dashi sai ya juyo yana fuskantar TV din yace.” To masu kallon ga dai Amjadu AbulAbbas Wanda kuka fi sani daYoung millionaire, zai tafi k’asashe biyu domin gudanar da harkokinsa na yau da kullum domin kawo wa k’asar shi cigaba muna yi masa fatan dawo wa k’asar shi lafiya tare da nasarori, duk wani me kaunar sa, sai ya raka shi da addu’a Allah ya bashi sa’a a dukanin abunda ya sanya a gaba.
Yana gama maganar tashi
A ka d’auke shi, film din ya cigaba, aunt da kawarta suka dinga yi masa addu’a gami da fatan alkairi, Ni da Mimi kuwa babu Wanda yace.” Uffan! Har yanzu ko wacce ita tasan halin da take ciki.
Aunt naji tana fadawa kawar ta abunda ya faru kwanakin baya, Zainab tace”Ko sonta yake ne.”? Aunt tace ” Nima nayi tunanin haka wallahi amma sai naga kwata-kwata bai nuna alama ba, Zainab tace”ke akwai dai abunda yake faruwa wallahi tunda nake ban tab’a jin ance ya dauki budurwa ya kai ta tayi shopping ba sai akan Asma’u ina ganin son ta yake.”
Da sauri na kalli aunt Zainab nace”Bani yake so Aunt.” Duk suka kalleni nace”Wallahi kuwa Mimi yake so.” Mimi tayi saurin sunkuyar da kanta cike da kunya,
Aunt hauwa ta jawo ta jikinta tana dariya tare da fad’in”Kai Alhmdullahi kice wahalar mu ta kusa karewa dama nasan Mimi na ta shiga tsara ce babu namijin da bazai so ta ba farar mace alkyabar mata.. Wai!!!! Kice wata shekarar damu za’ayi aikin hajji.'”” Aunt Zainab dariya kawai take wa kawar tata ni kaina duk da halin da nake ciki sai da na dara ganin yanda aunt Hauwa duk ta gigice! Aunt Hauwa ba dai son kudi ba.

Nace”Aunt kinga ma wayar da ya bata.” K’okarin dauko ta nake Mimi tana kwace jakar sai da na Ciro na mik’awa aunt ta karb’a tana dubawa hade da rik’e baki take fad’in”Mimi wannan wayar si tafi dubu Dari.”” Lallai Juma’ar da zata yi kyau tunda ga laraba ake gane ta.”
Aunt Zainab ta karb’i wayar tana dubawa itama jinjina kai tayi tare da fadin” har wani kamshi wayar take lallai abun na manya ne, Mimi Allah ya dubi maraicin ki, idan kika shiga gidan nan kar ki manta damu don Allah.”
Cike da mamaki nake kallon su, ina mamakin son kud’in su lallai a duniya idan kayi kudi ka wuce komai Mimi tun kafin ta shiga gidan sun fara magiya.. Kallonsu kawai nake suna zolayar Mimi ita kuma tana wani sinne kai, cikin zuciyata nace “Kin had’u da aiki babba Mimi.


K’arfe goma da kwata mun fito cikin shiri kamar wasu taurari Munnu nan tazo mu tafi tare, munyi bala’in kyau mussaman ma ni suffa da b’oyayyan kyau na yau sun futo a zahiri saboda abunda bana yi shi nayi wato kwalliyar fuska, kamar wata Queen haka na zama muna sanye da material dinmu Wanda aka yi mana dinki duguwar Riga mai tattara daga baya daga gaba kuma yayi sama anyi masa wani irin yanke gege da gefe dogon hannu ne yayin da rigar ta kasan pitat gown ne gaba d’aya rigar take tayi matse ni tam!! Nishi ma da k’yar nake, gani da manya breast da uban hifs Sai da na sanya yari da sark’a na sannan na kalli mudubi, ni kaina nasan nayi kyau sosai, Munnu da Mimi suka saki baki suna kallona, nace” Meye wai!? Munnu tace.” Anya baza ki cire kayan kuwa ba kinga yanda suka matse ki, ke gaki tubar kallah.” Nace” lallai Munnu wallahi ko Umma yau baza ta hanani futa da kayan nan ba.Mimi tace” sai ki sanya hijabi idan muka je can ka cire,amma dai kin San gurin ya hada samari da ‘yan mata duk budurwar da take da saurayi zata gayyace shi yazo gurin.” Nace” Mimi ina ruwana wai don Allah Ku k’yaleni mana.” Ganin raina ya b’aci ya sa suka k’yale ni. Umma na zaune s rumfa tana kule-kulen ta muka futo takalemu a tsanake tace “kunyi kyau tamkar wasu amare,amma ke Asma’u meye kika sanya hijabi.”?
Nace” Umma dinkin ne ya matsani shine nace”idan na shiga cikin ‘yan uwana mata sai in cire.” Tace” haka yayi to Ku kula don Allah Ku tsare mutumcin Ku ana gama taro ku dawo gida kar Ku tsaya kad’e-kad’e da raye-raye.” Muka ce insha Allahu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button