BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

26/11/2019
[11/26, 9:01 PM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO

MALLAKAR_ BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI

64

Sosai Jahid yaji babu dad’i saboda yana k’aunar Asma’u tsakani da Allah kuma sam baya kaunar yaji wani ya fad’i mummunar magana a kanta, kokarin mik’ewa yake Amjad din ya mai dashi ya zaunar, gyara fuskar shi yayi babu alamun wasa yace.” Karfa kayi magana ta wata fahimta ta daban, ba wai na fad’i wannan maganar bane domin ranka ya b’aci ko kuma kaji wani fargaba a game da k’udirin ka kan yarinyar kace zaka janye auran ta. No kawai na fad’i iya abun da nasa ni a kanta, kuma kasan ko wane mutum Tara yake bai cika goma ba, amma hak’ika ka cancanci yabo da godiya a gare ni abokina babu abunda zaka nema a gurina na kasa yi maka shi, misali kace min in baka Baby Aysha zaka had’a ta da Salim ka rike min, wallahi babu abunda zai hanani in baka saboda nasan Maman Salim macace da take da nutsuwa gami da tarbiyya sai ince maka ma kusan halayen su d’aya da Mimi Allah ya jikanta, amma maganar In bawa Asma’u baby ka aje ta gefe guda a halin yanzu babu ita.” Jahid ya Dan ji sanyi a ransa, amma duk da haka bai hak’ura ba saboda kwata kwata baya son b’acin ran Asma’u yace.” Yanzu idan Allah ya kaddara auramu da Asma’u zaka bamu ita ko ? Tunda kana ganinta a kusa dakai sai kayi mata tarbiyar da kake so.” Amjad yayi Dari hade da Sosa kansa yace.” Mai zai hana kuwa zan baku wannan nasan muna kusa kuma kai ma zaka samin ido sosai.” Jahid yaja tsaki tare da mik’ewa tsaye yace.” Baza ka fasa ba kenan ? Ni kaga tafiya ta.” Amjad ya mike tsaye shima yana dariya ya rufa masa baya. To kafin suyi sallama ma sai da suka d’an jima a tsaye sannan suka rabu, dama kuma tun Asali cikin makotan sa, sunfi shiri da Mujahid din saboda saukin kansa.


K’arfe takwas dai-dai Mujahid ya kirani a waya cewar gashinan a waje yana jirana, a shirye nake saboda nasan da zuwan sa, cikin motarsa na same shi, Duk sanda zai zo gurina da sabbin kaya a zuciya nace Jahid ba dai gayu ba, budewa nayi na zauna sosai ya sakar min murmushi tare da fad’in “Yau kin futo da Wuri.”
‘Yar dariya nayi nace”A shirye nake dama ya maganar mu da kai.” Fad’uwar gaba yaji amma dake namiji ne sai ya dake yace.” Kya bari mu gaisa ko.”?

Rife fuska ta nayi da tafin hannuna ina dariya, shima dariyar yake yace.” Ke kinfi baby Aysha rigima ma.” Bude idona nayi har yanzu da murmushi a fuskata nace”Wallahi na damu na ga babyn ne.” Yace.” Kina da gaskiya amma kin san me.”? Girgiza kaina nayi, yace.” Babanta ya hana wallahi yace ki Bari tukkuna muyi aure zai bamu ita.” Raina a bace nake kallon Jahid din nace”Ban gane ya hana ba.”? A hankali yace.”Shima baya so tayi nisa dashi a yanda na fahimta yana kallonta baby ne yaji sanyi a ransa duk lokacin da ya tuna matarsa.
Nace.” Jahid abun da bangane ba shine, shi kad’ai ne yake da hakki da yarinyar? Mu da muke a matsayin iyayen ta bamu da amfani kenan Jahid gani ba ci ba, dama baby ‘yar shi waye yace ba tashi ba.”! A zafafe na k’arashe maganar.
Jahid ya gyad’a kansa ya San zai fuskanci haka daga gurin ta, yace.” Matsala ta dake saurin d’aukar zafi kiyi wa magana ta kyakyawar fahimta mana.” Cikin takaici da jin haushin sa nace”Na lura kamar bakin Ku d’aya Jahid baka San yanda nake ji ba Wallahi tallahi tunda naji kuna fadin baby suna kama da Mimi naji ina mugun kaunar ta.” Cikin rawar murya ta karasa maganar, cike da tausayin ta yace.” Kiyi hakuri dai yanzu dai kar kiyi min kuka Jahid UA fad’a cikin rarrashi. Nace”Wallahi na saki jiki zangan ka da tare da ita.” Cikin shagwaba take maganar,Jahid yaji kamar zai suma a gurin hannunsa na rawa yace.” Bari kiga hotonta hankalin ki ya kwanta, nima dai kin kusa bani nawa babyn ko.”?

Murmushi kawai nayi masa ina Allah-Allah ya mik’o min wayar in gani.. Da sauri na karb’a ina dubawa sosai baby Aysha take kama da Mimi sai da tafi ta haske kamar yanda naji suna fad’a ta murmure sosai da gani ma hoton tana jikin babanta aka dauka don ga jikin shi nan ya futo da hannunshi guda da ya rike ta, Dole in gane saboda manya manyan azurfan dake bisa yatsun sa.
Wayar na rungume a k’irjina ina sakin ajiyar zuciya nace”Jahid baby Aysha na kama da Mimi wallahi ka bani wayar nan yau ta kwana a hannuna in kwana ina kallonta kaji. ” dariya yayi yace.” Kece kin ki ki bude whatsp da sai na turo miki hoton.” Da sauri na mik’a mishi wayar nace “Bari in dauko wayar tawa ka tura min wsp din don Baby Aysha amma da na daina yi.” Dariya yake min har na futa daga motar. A tsakaice dai sai da Jahid ya bude min wsp dina da na rufe tun bayan rasuwar Mimi ya tura min dukanin. Hotonan baby Aysha, yace” kullum zai dinga d’aukar ta sabbin pictures Yana turo min sosai naji dadin haka na saki jikina sosai muka yi shirarmu nan yace insha Allahu a karshen wata yake so ya turo magabatan sa gurin Kawu Yunusa nace”Allah yasa nan mukayi sallama dashi ya tafi.

Ko da Umma taga hoton baby Aysha tayi ta mamaki sosai sai taji sha’awar ganin yarinyar a zahiri tace.” To tunda ya hamu ita ni zanje da kaina in duba ta ai hakan ba laifi bane.” Umma da kin kyaleshi dai komai abunda baby Dole ta nemi dangin uwarta wallahi.” Umma tace”Ai baza’ayi haka ba, domin bamu San munufar sa tayin haka ba, to koma dai menene abar shi da d’iyar shi yayi yanda yake so da ita.” Shiru nayi ina raya wani Abu a raina

Abunci naci nayi wa Umma sallama, kai tsaye dakinmu na nufa, na tube kayan jikina wata duguwar Riga na sanya a jikina mai uban kyau da tsada duk cikin kayan Mimi suke, hula na sanya a kaina na kwanta kan katifa, hade da rufe k’afafuna hotan baby na tsurawa ido ina murmushi nima wallahi na damu inga yarinyar a zuciya ta.

Wsp na shiga na d’ora pic dinta kan df na, wsp din dake amfani a waya ta mai Gb ne ya nuna min Amjad na online wata zuciyar tace kiyi masa magana kawai tunda gashi a onile da sauri na shiga gurin shi naga ya sauka akai. Yanzu Df shi na kamo da sauri ina dubawa, pic dinshi ne da baby Aysha ya d’aga ta sama yana dariya hat tada dimple dinshi sai da ya futo saboda dariya itama babyn dariya take naji sun bani sha’awa, zuciya ta tace min “Shi yana Cikin jin dad’i har da dariya gashi ga ‘yar shi hummm! Ai in da mutumci Amjad bamu cancanci haka daga gurin shi ba, message na tura masa kamar haka

” Duk d’an halak baya bance alkairi kuma tilas! Ace da mijin iya baba, duk talaucin mu, baby na tabbata sai ta neme mu, domin mune dai dangin uwarta.”

Tura masa nayi na kashe data ta, tsawon mintuna ashirin, na k’ara bud’e datar, ina dubawa naga har ya gani, sai naji wata fad’uwar gaba, messenges na cigaba da dubawa ina sauraron amsar sa, shiru kusan minti talatin kuma duk dubawar da zanyi sai inga yana online, bakin ciki da takaici suka ishe ni, abunda na tsana a rayuwa ta shariya guy nan yaga sakona zai wulakanta ni, lallai ya sanja sabbin halaye, ji nayi wasu zafafan hawaye na nema su kufce min. Kira ne ya shigo wayar tawa ina dubawa naga shine…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button