BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Duk abunda yake faruwa tsakanin Mujahid da Asma’u a kan idonshi, yasan halin Mujahid akwai son matan tsiya gashi dai da auran shi, amma in yaga mata jikinsa har tsuma yake, yaji wani iri a zuciyarsa amma kallon da yaga Asma’u na watsa ma Mujahid din ya ji dad’i a zuciyarsa yace.” Mata masu daraja kenan.”

Mik’ewa nayi daga gurin ina waige-waige Su Munnu na can baya an had’u da samari ana hira da ciye-ciye ganin na mike yasa Maryam mik’ewa muka fara ratsa jama’a tafiya zamu yi tunda dai an gama ango ya kawo amaryar sa gida domin na tsani kallon da maza suke min. Aikuwa ido yayi caaaaa! A kanmu ni kaina a jikina nasan kallona ake yi, cikin sauri sauri nake tafiya inda sassaan jikina yake motsawa, sai tsaki nake.

Amjadu kuwa tun lokacin da ta mike tsaye ya karewa jikinta kallo kuma yaga yanda shatin jikinta ya futo ta cikin sharara din mayafin ta, sai yaji kamar ana soka masa kibiya a kahon zuciyarsa, mussaman. Yanda yaga maza da dama sun raja’a a kanta, gumi ya tsinke masa, lips d’insa ya tura a baki yana ji kamar ya hadiyi zuciyarsa ya huta da wannan bakin ci, Mimi ya kalla a sace ya ga Sam ita babu wani abun assha da dinkin ya futo mata dashi, ya rasa wace iri ce Asma’u me karuwan jiki, ko wane irin kaya tasa sai sun tona mata asirin jiki. Innalillahi wa’inna’ilah raji’un. ” shine abunda yake nanatawa cikin zuciyarsa ko ya samu sassauci.

Ganin duk sun mike ne suna kokarin futa daga gate sai hakan yayi masa dad’i mutuka wayar sa ya dauka yana kiran Rambo yace.” Maza’a maida su gida shi da kansa zai kawo Mimi gida aikuwa haka aka yi, muna kokarin shiga mota ne sai ga Muhajid ya k’araso gurin, hade da kure ni da ido yana sakin wani murmushi, yace.” Asma’u.” Nayi mamakin yanda ya San sunana haka, babu yabo babu fallasa nace.” Na’am ya kake.”?
Murmushi yayi Wanda na lura hakan d’abiar shi yace.” Lafiya amma ba Lou ba, tunda na ganki na rikice na gigice na dimauce na rasa nutsuwa ta, Asma’u ina kaunar ki fisabillah.” Ya k’arashe maganar sa har da kwantar da kansa, Su Munnu kuwa dariya suke masa, yace.” Ina da mata da yara biyu ni ma’aikacin lafiya ne, ina aiki a nasarawa hospital ina fata zaki so ni kar kice na miki tsufa.” Yanayin barkwancin sa da yanda yake da sakin fuska da wasa da dariya yasa na saki fuskata nace”Ashe dai ka sani ni kam kayi min tsufa bazan auri me mata ba.” Marairaice fuska yayi hade da fadin “Don Allah kinji. ” sai na tsinci kaina da sakin dariya har fararen hak’ura na suka bayyana Wanda yayi dai-dai da zuwan Amjadu gurin Hannunshi rike da na Mimi, ina ganinshi na dauke kaina da sauri gaba na lugude, ko kallonmu bai yi ba nida Mujahid ya fara magana dasu Rambo Wanda suke kokarin saka mutane a mota, Ina jin Mujahid nace “Aboki nifa nayi mata a gurin nan gaskiya naji dadin wannan ranar wallahi na tsinci dami a kala.”
Babu yabo babu fallasa ya kallemu dani dashi yayi wani killer smile As’usuel ya sosa kanshi tare da fadin”Kayi dace Aboki amma bakayi gaggawa ba, kuwa.” Mujahid yasa dariya tare da fadin” Wane irin gaggawa kuma in tsaya kallon ruwa kwad’o yayi min k’afa.”
Kamar babu abunda yaje damunsa ya sanya dariya tare da fad’in”OK ni babu ruwana wallahi kai da Madam.”! Mujahid din yace.” Shareta ai ba da ita kadai zan zauna ba.” Shiru yayi masa ya cigaba da magana da Rambo, ko da wasa ban kalli shi ba sai ma sauri da nayi na bude motar na shiga.

Ina kallonshi ya rungume kafad’un Mimi a jikinshi lokaci-lokaci yana sumbatar goshin ta, hade da yi mata magana k’asa-k’asa, da sauri na kauda kaina dama tsautsayi ne yasa na kalleshi, Yanzu kuwa Allah Allah nake motar ta tashi mubar gurin.

16/November/2019
[11/17, 1:56 PM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO

MALLAKAR_ BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI

54

Sai ya tabbatar da motocin su sun tashi sannan yaja hannun Mimi suka bar gurin, cikin sauran abokan sa ya koma masu hoto suka dinga d’aukar shi da Mimi sai sunkuyar da kanta take cike da kunya shi kuwa rumgumeta yake jikinsa fuskar sa a sake, ‘yan jaradi ma ba a bar su a baya na sai da suka zo ganin k’waf tare da d’aukar amarya da ango hoto da vedio walima tayi kyau sosai kuma ta k’ayatu, k’arfe 11:30 gurin yayi sauki jama’a duk sun a watse a gajiye yake sosai amma babu yadda ya iya dole ya maida Mimi gida. Hannunsa rike da nata babu um bare umum suka shiga mota tare Doh! Yazo da sauri, sai ya daga masa hannu alamun a’a baya ya matsa, yana d’aga masa hannu yaja motar suka futa daga Estate din.. Sai da ya hau kan kwalta sannan ya kalleta a fakaice yace.” Momy kin gaji wannan idon naki akwai bacci a cikinsa.”? Mimi tayi kasa da kanta tana wasa da hannunta tace.” Wallahi na gaji sosai hankalina yayi gida.” Cike da tsokana yace.” Da har ina cewa kinzo kenan baza ki koma gida ba.” Kauda kanta tayi cike da kunya, hira sama-sama suke yi da ita kamar wasu surukai har suka Isa badawa yayi parking a inda ya saba, kallonta yayi da lumsassun idonsa saurin dauke kanta tayi, ya saki murmushi tare da fadin “Kije ki huta kinji ko gobe ina jiran ki, kiyi min tanadi me kyau.” Kofar motar ya bude mata hade da sumbatar hannunta guda, Mimi ta futa a hankali tana d’aga masa hannu, motar yaja ya bar gurin, dake da wutar NEPA a unguwar yasa matasa basu watse ba. Mimi ta tsallaka ta shiga lokonsu cikin sauri

Hira muke da su Munnu amma hankalina da tunani na nakan Mimi gamin har k’arfe goma sha biyu saura bata shigo gidan nan ba, Umma ma ta leko dakin kusan sau uku tana tambayar ta shigo, aunt Hauwa ce ta kwantar da hankalin ta, tunda dai tana gurin mijinta,Ni da Munnu hirar muke Mimi ta shigo da sallama, duk muka bita da kallo, ‘yar dariya tayi tare da fadin’Meye daga shigowa ta zaku zuba min ido.”? Tsaki naja ina d’an hararata nace.” Mimi dubi lokaci fa ke ko tsoro bakya ji, bakya ce masa dare yayi.” Maryam dake danne-danne a waya tace “Wane irin tsoro tana tare da mijinta.” Munnu tace “Nima dai abunda na gani kenan.” Tab’e bakina nayi kawai ina kallonta ta tsallako har inda nake zaune k’amshin turaran sa ya buge ni, domin duk jikin Mimi k’amshin masifaffan turaran sa take, d’an rungume ta da yayi, sai naji zuciya babu dad’i wani irin kallo nake mata cike da zargi ina tunanin ko wani Abu ya shiga tsakanin ta dashi, tunda nasan halinsa ba hakuri ne dashi ba, mik’ewa nayi na futa daga dakin domin ji nayi wani irin fleelings na taso min jin k’amshin turaran sa sai na dunga tuno da salon soyayyar shi, Uwar dakin Umma na shifa duk mutane kwance a rumfa na tsallake su, kwanciya nayi kan gadon ta, gefan aunt Hauwa wacce take bacci sosai nasan gajiya ce.” Lumshe idona nayi ina addu’ar kar Allah ya dora min tashin sha’awa ta a wannan daran nasan zan shiga mugun hali ga jama’a a gidan.


Shima bashi bangaran damuwa da tsanani gajiya su suka dame shi, don haka yana shiga part dinshi yayi wanka ya futo parlor ya kwanta kan doguwar kujera lokaci guda bacci ya dauke shi, mai cike da mafarkai bar katai.


Washe gari da kuncin zuciya na tashi har ‘yan buki suka so su gane ganin naki walwala kamar jiya yasa suka dame ni da tambaya dole na sake na cigaba da wurda da mutane kamar yanda na saba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button