BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

[11/2, 10:29 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO

Mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA

37

Ko da Mimi ta shigo ban saurare ta ba, ina tsaye bakin k’ofar dakin Ummanmu muna magana da ita.Simi-simi tazo ta shige dakinmu tana b’oye abu cikin mayafin ta, naji zuciyata bata yi min dad’i ba, futowa tayi ta tsaya kusa dani tare da fad’in “Shine kika tawo kika barni a hanya ko.”? Umma tace” nima yanzu nake tambayar ki tace ta barki a hanya, amma kun Dade gaskiya sai da kwalliya ta biya kud’in sabulu tunda gashinan lallai yayi kyau sosai.”

Mimi tace”wallahi kuwa Umma mun tadda ita tana yi wa wasu shiyasa.” Tace” abuncin Ku na kicin.”

Kicin din na wuce ba tare da na tsaya kallon Mimi ba, abuncin na dauko a kula nan rumfar Umma na zauna tare da bude food Fula’s din ina k’okarin zubawa. Jiki a sanyaye Mimi ta k’araso inda nake zaune duk ta damu ganin yanda na share ta.Umma ta mike ta futa tsakar gida tana amsa sallamar da ake yi.

Mimi ta kalle ni bakinta na rawa tace”kin San me Asma’u. “? Nace” sai kin fad’a.”
“Guy nan fa wayarsa ya bani had’addiya baki ganta ba, wai zai dinga kirana da ita…..gabana ne yayi wata irin fad’uwa!! Tuni naji abunci ya futa kaina na kalleta cikin dauriya tare da fadin” kin dace Mimi Allah ya kara k’auna” Mimi babu kunyar komai tace” ameen Ashe haka yake da saukin kai.”? Nace”Hummm”? Hirarsa kawai take min takasa cin abuncin nace “Mimi so ya hanaki ki ci abunci ko? Ki dai yi a hankali.” Dariya tasa cike da farin ciki, duk Wanda yasan Mimi a lokacin zai fahimci fara’ar ta da walwalarta ya k’aru.


Kai tsaye Company nasa ya nufa Wanda ake aiki tuk’uru ma’aikata iri-iri sai kai kawo suke, insha Allah yau za’a gama komai sai abunda yayi saura had’a wuta tare da fenti amma komai ya kammala kuma ma’aikata suna tsaye a kai. Yaji dad’i sosai da sosai ganin yanda sabon company shi ya koma tamkar Wanda aka dauko shi daga America aka dasa shi a gurin tsari da k’atuwar company ba’a cewa komai, nan ya zauna da tsofaffin ma’aikatan sa suka yi meeting akan yadda za’a tsaurara matakan tsaro a gurin, kuma dole za’a dibi sababbabin ma’aikata, Amana ya damk’awa Bashir Manager saboda yasan ya wuce chana gobe zuwa jini domin yaga wane irin cigaba a ka samu a can d’in.

Harabar gurin ya futo yana kewaya wa hannunsa goye a baya, tabbas zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana muzu ana shaho sai yayi

Wani ma’aikacin gidan talavition ne ya k’araso gurinsa a nutse yace.” Ranka ya Dade dama tun d’azu muke jiran futowar ka, mun dad’e a waccan rumfar muna zaman jiran ka.”
Kallon gurin da yake nuna masa yayi sai ya gansu a zazzaune su kusan hud’u. Cike da mamaki yace.” Me zaku yi min kuma.”? Ma’aikacin yace.” Ranka ya dad’e ‘yan tambayoyi zamu yi maka a gurguje.” Girgiza kansa yayi ya rasa me yasa suke bibbiyar sa, yace.” Muje can d’in” wata k’atuwar rumfa suka nufa wacce take kewaye da wasu had’addan kujeru na silver gurin hutawa ne an kammala tsaf hatta da tayel an saka a gurin fenti ne kawai ya rage, kujera suka gyara masa ya zauna sannan kowa ya sai ta na’urarsa. Cikin nutsuwa d’aya daga cikin ‘yan jaridun ya fara kwararo masa tambayoyi kamar haka.”

“Yallab’ai dama muna son Karin haske ne daga gurin a game da labarin da muka samu sati d’aya daya wuce shin da gaske bayan wannan company da ake aikin sa wai akwai wasu guda biyu a k’asashen waje? Yallab’ai muna buk’atar Karin haske akan wannan jita jita da jama’ar gari suke yi mussaman ‘yan kasuwa.”

Murmushi yayi kawai yana girgiza kan sa ta tabbata kenan duk abunda yake idanun mutane a kansa yake, shidai a iya sanin sa babu da Wanda sukayi zan can cewa zai bude company a america da Ingila sai Anthony sai granny su kadai ne sukan wannan maganar.

Gyara zaman sa yayi sosai yayi gyaran murya alamun zai fara magana, duk suka matso da lasifik’an su, Yace.” K’warai kuwa ba jita-jita bace gaskiya ne maganar jama’ar gari tabbas ina shirye-shiryen bude company guda biyu d’aya a America daya a Ingila sati mai zuwa za’a gudanar da bukin budewar a can kamar yanda za’a gudanar anan, ina yi wa ‘yan kasuwa albishir da cewar duk me sha’awar futa waje yayi odar kaya to ya je company mai suna A’A ABUL ABBAS MAI NASARA, babu shakka zai samu duk wani na’uin kayan idai ya ka sance Wanda d’an adam yake sanyawa a jikinsa ne, kamar kayan mu na hausawa k’ananun kaya suit da sauran su akwai b’angaran kayan mata ko wane iri ne, takalma na maza da na mata duk company zai kawo kan farashi me sauk’i , sannan duk abunda company na kasashen waje zai kawo a kwai shi a wannan company nawa

D’an jaridar yace.” Sai tambaya ta biyu Yallab’ai, ina fatan samun amsa a gurin ka, kamar yanda muka samu wannan amsa ta farko munji kuma mun gamsu.”
“Shin Wai kana da aure Ku kuwa? Da yawa mutanan gari suna yi maka kallon Mai lyali Yallab’ai muna son mu samu wannan amsar daga bakin ki.” Murmushi ne ya sub’uce masa, ya d’an Sosa kansa kamar yanda ya saba yace.” A’a bani da aure a yanzu a sali ma ban shirya yin sa ba, tunda a halin yanzu bani da budurwa da na tsayar a matsayin wacce zan aura, to amma shi aure lokaci ne dashi idan yazo ko da matar a hannu ko babu A lokacin sai Allah ya kawo ta ayi ina fatan daku da jama’ar gari da duk wani me kaunta zaku taya ni da addu’a kan Allah ya zab’a min mace ta gari.”

D’an jaridar yace.” Insha Allahu Yallab’ai zamu taya ka da addu’ar Neman zab’in Allah ubangiji Allah ya baka mace ta gari tare da ‘yaya masu albarka, mungode mutuka da bamu lokacin ka daka yi Allah ya kara maka suttura da daukaka ya kare ka daga sharrin masu sharri.”

Hak’ika Amjadu yaji dadin addu’ar da Dan jaridar nan yayi masa, amsa da “Ameen suma ameen nagode K’warai da addu’a.”
Nan suka had’a na’urorin su cike da murnar samun nasara yau sun same shi ba tare da sun kai ruwa rana ba.”

Sai bayan sallah magariba ya bar company din hankalinsa kwance ganin komai ya kammala, tun a mota kira yake shigowa wayoyin sa, ko d’aya bai d’auka ba, draving din sa kawai yake yi saboda ya san dai bai wuce jama’ar sa ba masu son jin ta bakin sa, tunda ko wace kafar sadarwa ta jahar kano a labaran ta na yamma ta sun sanyo jawabin sa, shine dalili kawai hatta da gidan television na NTA kano suma sun hasko shi cikin labaran su na k’arfe shida, yana ji a jikinsa kamar akwai wani babban al’amari da zai same shi anan gaba.
Kai tsaye gidan granny ya nufa domin yayi mata sallama.


Governor ne da gaggan ‘yan kasuwa wad’anda suka ci suka ts dakai marasa tausayin na k’asa dasu Wanda Kansu kawai suka sani. Masu bakin ciki ga duk wani Dan kasuwa da ya sauke farashin kayansa, a cewar su talaka ba abun tausayi bane. Su biyar ne a dakin meeting din gidan gomnati wato government house suna tattaunawa game da yanda zasu b’ulluwa Amjadu domin dukaninsu saurari jawabin sa, na yau, hankalin su yayi masifar tashi sosai jin wai har company biyu ya bude a kasashen waje bayan company shi nan Lallai ya zama dole su San yadda za’ayi su rusa shi.

Alhaji Sunusi mai leshi ne Yace. ” Ni ina gani kawai mu hada baki da ma’aikatan sa mu Sakar masu KUDI Sosai mu fada musu bukatar mu. Cewar muna so su sanya algus da mugunta a ko wace irin adduga da zasu sarrafa, a company ta inda duk kayan da za’a futar a company su zama marasa k’wari da karko kunga daga nan Jama’a zasu gane sai su fara guduwa.”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button