BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Shiru nayi ban ce komai ba
A hankali naji ya ambaci Sunana Asma’u wani iri naji a jikina ya iya fad’ar sunana.
“Uhum.”!! Abunda nace kenan.
Yace” Malama ki bude baki kiyi min magana ko in kashe wayata meye wani Uhumm.!? Nace “Me kace to? Nifa ban ji abunda kace ba.”
Tsaki yaja yace.” Baza ki ji ba dama fitinanniya kawai.”
Kitt!! Ya kashe wayarsa
A hankali na aje wayar ina tab’e bakina ko banza na samu sassaucin abunda nake ji.
Mimi sahorama tana can tana bacci ko motsi ta kasa yi

Amjadu yana sane ya kashe wayar shima saboda yanda ya fara jin Jikinsa ya sauya joystick dinshi ta mike sosai wata irin sha’awa ta bujoro masa, yasan haka zai kwana cikin mawuyacin hali.

Haka suka kwana suna juye-juye sai dab da asubah bacci ya dauke su, cike da mafarkin jununsu.


Umma da Wuri ta futa Unguwa don abun kari ma mu muka Dora ni da Mimi
Kowa sabgar gabansa yake yanzu dukanmu mun rage sakewa da jununmu.
Tare muka karya da muna hira sama-sama Mimi ta kalli gurin kwanciyata taga rigar Amjadu.
Tace”Asma’u waccan kamar…. Kafin ta karasa nace”Eh rigarsa ce ya bani na kare jikina da ita jiya dare yayi kafin in shigo gida ga shegen karanan yayi ta yi mun haushi. “
Fuskarta ta sauya tare da dauke kanta tace”Har nayi bacci ina sauraron shigowar ki.”
Ina sane nace “E Wallahi unguwa na raka shi.
Kallonta tayi fuskarta a hade ta tab’e bakinta.. Nace.” Jiya kina bacci ya kira wayar ki.”
“Meya sa baki tashe ni ba.”?
Nace” Shine yace”A k’yale ki ki huta, shine mukayi hira sai kusan k’arfe daya na dare na kwanta.
Wani irin kishi ya bujoro wa Mimi mik’ewa tayi taje ta kwanta kan katifar ta
Kallon ta nayi cike da Mamaki nace”Mimi kishi kike dani ko.”?Cikin wayancewa tace”Wane irin kishi zanyi dake Asma’u. “?
Nace” Gashinan daga magana kin je kin kwanta ko abincin ma kin kasa ci.”
Murmushi tayi tace”Ji nayi bakina babu dad’i tunda naji kin ambaci Amjad gabana yake fad’uwa.wani irin nauyi k’irjina yake min.”

Nace.”Mimi ya zama Dole fa ki ragewa kanki damuwa soyayyar da kike nunawa. Mutumin nan fa akwai matsala domin zata ita kai ki ta baro kuma duk sanda ya fahimci son da kike masa wulakanta ki zai yi, Sam! Ba’ayi wa Namiji haka.”
Lumshe ido tayi tace”Asma’u wani irin nauyi nake ji cikin zuciyata da ina iya hak’ura da guy nan da na hak’ura na bar miki shi Wallahi saboda na fahimci kamar yafi sonki dani.”
Nace”Ki barmin shi ko in bar miki shi, Amjadu Mijin ki ne ki kwantar da hankalin ki.” Shuru tayi ba ta sake cewa komai ba.
Minti goma tsakani wayarta tayi kara dauka tayi tana lumshe ido na na tabbatar da cewar shine ya kira ta, mik’ewa nayi na fuce daga dakin domin bana son inji hirar da zasuyi ballantana i n shiga damuwa.

Sai bayan Sallah la’asar Umma ta dawo gidan, jikinta duk babu k’wari tace” Asmau Zuba min ruwa inyi Alwala a hanya la’asar tayi min.”
Da sauri na zuba mata na mik’a mata ina nazarin ta, har ta shige band’aki

Dakinmu na shiga jikina a sanyaye a zuciyata nace Akwai matsala gaskiya tunda naga Umma ta shigo gidan nan jikinta babu k’wari.

Kusan Rabin awa da shigowar ta ta kwala mana kira. Ni da Mimi muka amsa a nutse muka Isa Rumfar, tana zaune da carbi a hannunta tace”Duk Ku zauna muyi magana.”
Zama mukayi ko wacce da Abunda take saka wa.

Carbin ta aje ta kallemu tare da fadin “Babban al’amari ne yake tunkaro mu dani da Ku, ina so kuyi min adalci kuyiwa kanku a adalci bana son zumuncin Ku ya lalace saboda duk inda akace kishi to sai anyi shi ko ciki daya kuka futo
Yanzu daga gidan Yunusa nake Wannan yaron da yake Neman Ku da aure tun safe ya turo magabatan sa, da kud’in aure harda sadaki yace.” Nan da wata guda yake so, ayi komai a gama. Kawu Yunusa ya amsa musu hade da karb’ar dukiyar auran, kafin in futo daga gidan Aminu yaje da maganar shi ta cewar yana son auran ki.” Tafad’a tana nuna Mimi da hannu, a cewar sa tun kina yarinya yake sonki ya ki fada ne kawai saboda yana ganin baza ki fi k’arfin sa ba, sai Kuma gashi lokaci guda wanki hula na Neman ya kaishi dare.
Kawu Yunusa yace magana ta wuce tunda har ya bari aka karb’i kud’in auran ki. Sai dai yayi hakuri kawai. Yanzu halin da ake ciki yana babban asibiti na Malam Aminu domin fad’uwa yayi a gurin har na tawo bai dawo dai-dai ba.”
Umma ta k’arashe maganar ta zuciyar ta babu dad’i.
Nace”Umma me yasa Ya Aminu bai yi magana da wuri ba har sai da ya bari aka karb’i kud’in auran ta, to ai itama Mimin. Zata shiga wani hali
Kuma jiya mun gama magana da Amjadu cewar ya janye aurena saboda rashin dacewar haka, Mimi zai aura kuma daga baya azo ana kace nace.”
Umma tayi shiru fuskarta cike da alhini.
A hankali Mimi tace.” Umma ki kwantar da hankalin ki, Indai akan sona Yaya Aminu ya suma har ta kaishi ga kwanciya a asibiti insha Allahu ni zan share miki hawaye
Dama nike son Amjadu bashi ba Asma’u yake so tuntuni zuciyata takasa yardar min da haka, Umma zan auri Ya Aminu ki kwantar da hankalin ki.”
Umma ta share hawayen ta, tace”A’a Mimi bazan miki dole ba bayan an kawo kud’in auran ki saboda son kaina ince ban yarda ba ga Wanda nake so ki aura duniya sai ta zage ni mutanan gari su dinga fadin”Don bani na haife ki ba shiyasa nake miki bakin cikin shiga cikin daula bayan haka kuma zuciyar ki tana son Amjadu idan nayi haka ban miki adalci ba, dole Aminu shine zai janye kudurinsa.”

Kuka Mimi ta sanya hade da rungume Umma tana fadin “Wallahi Umma da gaske nake babu abunda zaki nema a duniyar nan ban yi miki ba, mutukar ina dashi, Na hak’ura da Amjadu zan auri Ya Aminu.”
Cikin kuka ta k’arashe maganar.

Rungume ta Umma tayi tana kuka, nima naji k’walla ta cika min ido nace”Umma yaushe zamu je asubitin .”? Je ki d’aura abunci da sauri ana idar da sallahr magariba sai muje.”
Mik’ewa nayi na nufi kicin.

7/November/2019
[11/8, 11:36 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO

Mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.

44

A gurguje na kammala dafa abunci shinkafa da faduka nayi wacce taji allayyahu da albasa, Bayan mun idar da sallahr magariba ne muna shirye-shiryen tafiya sai muka ji sallama Umma ta futo da sauri Yaya Aminu ne da Musa da Kawu Yunusa suka shigo, Umma tace”Kaddai an sallame shi.”
Kawu Musa yace.” Gashinan kina gani dama nace Zai farfad’o Suma yayi.”
Ya Aminu ya zauna kan tabarma hade da dafe kansa.
Nida Mimi muka futo muka tsaitsaya
Dariya nake wa Ya Aminu ganin yadda ya fyad’e lokaci guda.
Sallama Kawu Yunusa yayi suka tafi ni da Musa kuwa babu Wanda ya kula kowa.
Umma tace”Maza je ki kawo masa abunci.”
Kicin na nufa da saurina.
Mimi ta zauna gefansa tana yi masa ya jiki.
Abunci na kawo na aje gabanshi
Naje na dauko ruwa pure watar babu sanyi,yace.” Kije ki siyo min me sanyi.”
Umma ta mik’o min ashirin tare da fadin”Ki siyo guda hudu.

Hijab din Umma na zura na futa daga gidan da sauri

Ya Aminu bai ci abincin sosai ba ya aje cokalin ya mike ya bar gurin.
Duk muka bishi da kallo. Umma tace”Cuta ta samu manya .” murmushi nayi kawai
Mimi kuwa tashi tayi simi-simi ta shige dakinmu
Nida Umma bamuyi hirar arziki ba muka tashi
Ina shiga dakinmu na tadda Mimi ta juya baya tana Kuka harda shashsheka.
Cikin mamaki nace”Mimi kuka kike yi.”?
Banza tayi min
Da sauri naje na birkitota sai naga idonta yayi mugun ja sai ajiyar zuciya take.
Zama nayi kusa da ita hade da rike hannunta nace”Mimi nasan kin amsawa Umma ne domin ki kwantar mata da hankali.
Nasan bakya son Ya Aminu Amjadu kike so Mimi me zai sa baza kiyi wa kanki gata ba zaki jefa kanki cikin mummunan hali. Kinsan bakya son Ya Aminu me yasa kika amsawa Umma.”
Hannuna ta rike tamau! Naji jikinta sai karkarwa yake
Tace.” Asma’u na rasa yanda zanyi da zuciyata nayi-nayi incere son Amjadu abun yaci tura ji nake kamar zan mutu Mimi zuciyata tana azabtar dani kan abunda bazan samu ba, don girman Allah ki taya ni da addu’a zuciya tabar cutar dani, soyayyar da nakewa Amjadu Allah ya cire min ta gaba daya ta koma kan Ya Aminu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button