BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Kuka nasa saboda tausayin ta tabbas so bala’i ne hannunta NA rike dake yin wani irin karkarwa nace”Mimi zan sanya ki a adduata in sha Allahu, kinga na farko ke kika cuci kanki d’azu da Umma tayi miki maganar Aminu sai ki nuna rashin amincewar ki, tom kinga daga baya baza kije mata da wata magana ba.
Zan cigaba da taya ki addu’a Ubangiji Allah ya yaye miki ya zab’a miki mafi alkairi.”
Sosai take kuka ina rarrashinta
Sai kuma naji ta fara wani irin tari!! Na mike da sauri na dauko mata ruwa
D’ago ta nayi na fara bata,
Tana shan ruwan tana tari da idonta yayi jazur
Cire ledar ruwan nayi na bugun bayan ta.
Tare da yi mata sannu.
Dana ga tarin yak’i sauk’i futa nayi da sauri na dauko gishiri a kicin na zo na Dan gwala mata a baki.
Tafi minti goma tanayi sannan ya lafa.
Sai haki! Take.
Ruwan na mike mata ta karba ta sha kadan.
Nace “ki kwanta kiyi bacci zakiji sassauci.
Kwanciya tayi tana lumshe idonta
Sai dana ga bacci ya dauke ta sannan nima na kwanta ina sak’e-sak’e Cikin zuciyata.
Bacci ya soma fuzgata naji kiran waya
haetbeat tsaki naja na dauki wayar na kashe gaba d’ayan ta domin shi nake mutukar jin haushi a ganina duk shine ya jawo mana wannan masifar.
Tun farko da bai nunawa Mimi yana sonta ba, ina ganin duk haka baza ta faru ba.
Da tune-tune bacci b’arawo ya kwashe ni.


B’angaran Amjadu kuwa, tun bayan da Wakilansa suka zo suka Sanar masa da cewar An bashi guda cikin ‘yan Matan da yake so ya aura sai gaban shi ya fad’i ya tunini ko Mimi ce, shine dalilin da yasa ya tambaye su kud’in wacce a ka karb’a a cikinsu nan Kawunsa yace.” Asma’u yaji dadin haka don haka kafin su tafi sai da yayi musu kyauta ta mussaman.

Shirye-shiryen bude company ya kammala yau saura kwana biyu gari ya dauka kafufin yad’a labarai in ka bude zancan kenan Ranar Juma’a Biyu ga watan bakwai za’a bude shaharrarn company nan wato AmjaduAbulAbbas materials za’ayi bononza a ranar abun dubu daya Dari biya abun dubu goma dubi biyar. Mutanan gari sun kunzige kudinsu suna jiran ranar domin su je su kwaso garab’asa.


Washe gari muka tashi da jiki a sanyaye Mimi ta rame lokaci guda, shi ko Ya Aminu dama tunda Kawu Yunusa ya Sanar dashi cewar an fasa karb’ar kud’in Mimi ya watsake ko da ya tashi da safe tamkar Wanda bai yi ciwo ba, yanzu Mimi CE abun tausayi so ya tasa ta a gaba.

Da kyar na rarrashe ta ta Karya kummalo
Umma ta tsaya bakin kofar mu tana fadin “Menene wai naji kuna takkadama.”?
Zuciyata tace kawai ki fadawa Umma ko menene ko Allah zai sanya ta fahimta.”
Kaina a kasa nace”Umma ina ganin wa….Shiru nayi na kasa magana.
Umma tace.” Meye kika yi shiru.”?
Bakina na rawa nace”Umma don Allah Ya Aminu ya janye kudirin sa a kan Mimi akwai cutar wa a ciki, ya kamata Mimi a bata zabin zuciyarta Ya Aminu Namiji ne shi zai iya jure komai kinga Mimi ko yarinya ce mai karanci shekaru gata kuma mace.”
Shiru Umma tayi tana nazarin magana ta.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace”Kin yi gaskiya Asma’u ni ma zuciyata batayi na’am da haka ba, saboda ina gudun zagin jama’ar gari tunda duk sun San komai Da Aminu da ke da Mimi duk daya kuke a gurina babu Wanda zan ce nafi so, amma kina ji da bakin ki tace ta amunce da Aminu kuma ko jiya Kawun Ku ya maimata min maganar babu gudu babu ja da baya tunda sunyi magana da mahaifin ta a waya yace ya bashi wuka da nama, Babansu Munnu ma har dashi cikin maganar kin ga bani da ta cewa.”

Nace “Umma kina da ta cewa mana don Allah ki sanya Ya Aminu ya janye magana…..kafin in karasa naji saukar Mari a kuncina Ya Aminu ne tsaye a kaina yana wani irin huci! Yace.” Kina so naci ubanki Asma’u, wato kina zu ga Umma kina zuga Mimi kan su bujirewa Bukatata ko me? Ni kinsan halin da Zan shiga idan na rasa ta, ko kinsan irin son da nake mata, mutukar ina Raye a duniyar nan bani da mata sai Mimi, dake da ita kuje kuyi abunda zakuyi akin gama ya Riga ya gama.”
Yana gama maganar shi ya fuce daga gidan a fusace!
Umma barin gurin tayi ni da Mimi mukayi shuru muna sak’e-sak’e
A hankali naji tace”Asma’u don Allah kar ki kara wata magana kan al’amarin nan, kinji tunda dai kince zaki taya ni addu’a tom na gode miki.”.
Murya na rawa take maganar
Nima naji zuciyata ta karye nace”Mimi sai dai idan gani nayi am d’aura muku aure da Aminu shine zan daina magana domin nasan ki nayi a banza ne, bakin alkami ya bushe, amma magana kan al’amarin yanzu na fara.”
Shiru tayi tans kallona.
Mik’ewa nayi na futa daga dakin zuciya nayi min zafi!

RANA BATA KARYA

Manyan attajirai da manya manyan ‘yan boko ‘yan siyasa masu mak’ami daban-daban Sarkin Kano sarkin Zazzau Sarki Katsina Jama’ar gari tsakunsu da kwarkatar su, sun hallara a wannan guri.

Hayaniya ce ta tsananta tare Da jiniya wannan ya tabbatar min da cewa me girma governor ne ya iso bani kadai ba, duk wani Wanda yasan da akwai dabi tsakanin Amjadu da me girma Governor sai da yayi mamaki, tuni jama’ar gari suka fara ihu!! Suna fadin abunda ransu yake so ga me girma governor.

Ko kunya babu me girma governor ya futo daga mota tare da jamarsa ya dinga ratsa jama’a Yana daga musu hannu hade da washe musu baki wai shi lallai ga governor tsagerun matasa masu goyon bayan Amjadu suka sanya ihu!! Da dariya suna fadin abun da yayi musu kan governor din, wasu na fadin”Ba mayi!!!! Sai da ‘yan sanda suka tsawa tar sannan hayaniyar ta lafafa, can gurin da aka tanadar wa manyan baki governor ya nufa, police na biye dashi a baya domin sun tsorata da irin ihun da jama’ar gari sukeyi,
Sai da suka ga ya zauna sannan suka koma gefe suka tsaya da bundigun su a hannu.
Can na hango Mai citta shida abokanan shi, sai zare ido suke.
Limamin babban massalacin jama’a na garin kano ne ya tashi ya bude taro da addu’a yayi karatun alkur’ani me girma sannan daya baya daya manya baki suka fara jawabi kowa yana yaba kwazo da jajircewa irin ta Amajdu
‘Yan jarida a gurin baza su kirgu ba, domin wasu jamar gari na gida kowa na gaban TV Wanda bashi dashi kuma kunne shi mak’ale da waya ko redio yana saurara.

Lokacin da Amjadu ya futo zai yi Jawabi Ihu!! Jama’ar gari suka sanya tare da fadin”Sai kayi fari me farar aniya ka iya ka huta AmjaduAbulAbas muna biye da kai insha Allahu 2004 taka ce sai ka zama shugabanmu.” Ihu! Kawai suke, sun hana aji bayanin da yake, da kyar jami’an tsaro suka shawo Kansu suka yi shiru.
Amjadu yayi jawabi me gamsarwa jawabin da ya ratsa zukatan al’umma Su Kansu manyan gurin sun jinjina masa kuma sunyi masa fatan alkairi.mai Martaba Sarki yaji dad’i sosai da samun hazikin Yaro a garin shi yana mutukar alfahiri da shi.

K’arfe goma sha biyu da rabi taro ya watse saboda ranar juma’a ce za’a tafi massalaci, nan Amjadu ya bada sanarwar cewa jamar gari suje massalaci su dawo bayan an idar da sallahr za’a bude company daga nan har zuwa goma na dare.

Haka akayi kuwa bayan an sakko jama’a sukayi ta tururwa company suna kwasar garabasa.Sai k’arfe daya na dare sannan aka samu saukin Jama’a.


Duk abunda yake faruwa a gari muna da labarin shi munji a redio Kuma mun gani a TV dake ranar sun bar mana wuta, abun mamaki Mimi yini tayi tana farin ciki.
Amjadu ya sha addu’a gurin Umma, aunty Hauwa ma ba abar ta a baya ba, kusan a dai-dai ta sahu guda tayo da kayan da bata koma gidan ta ba sai bayan sallahr Isha’i.
Ni ko tunda nayi masa kallon farko a TV ban sake kallonsa ba daga k’arshe ma tashi nayi na bar gurin naje na tsiri ninkin kaya ina tunin yanda Allah ya dauka kashi a duniya ‘yan da yake da kyauta da son talaka da yanda yake da farin jinin jama’a, yanda yake da ibada, amma yana aikata sabon Allah domin zina mugun aikine Wanda Allah ya hana shi, kawai sai na tsinci kaina da yi masa addu’ar shiriya naji wani irin tausayin shi, babu uwa babu uba ga makiya da d’umbun masoya gaba da baya, Allah ne kadai yasan abunda zai zama nan gaba, a fili nace”Ubangiji Allah ya kare ka daga sharrin ma su sharri Allah ya shirye ka shirin addinin musulunci yasa ka daina aikata zina.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button