BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Mai citta ya gyara zama hade da sakin murmushin mugunta yace.” Wannan shawarar taka tayi kyau kuma itace abar d’auka dole zamu San yadda mukayi mu jone da ma’aikatan nasa idan muka jik’asu da kudi kome ye zasu yi ko ya kuka gani.”?
Duk suka yi na’am da haka, nan taro ya watse ko wannen su cike da farin ciki.


Tana zaune a parlor kamar ko da yaushe me aikin ta Iyami na zaune a gefanta tana bata labarin garin su, yayi sallama ya shigo parlor, Iyami dattijiwa mai kirki ta dinga yi masa sannu da zuwa had’e da tsokanar sa, zama yayi cikin kujera yana gaishe ta, ta amsa da fuska a sake, da sauri ta nufi kicin domin ta kawo masa abunci.

Granny ta kalle shi babu yabo babu fallasa tace”K’ato me k’irar damu dawa kana tafiya gotai-gotai da kai babu iyali kai ko kunya baka ji, ka kai munzali amma ka tsaya shirme.”

B’ata fuskarsa yayi yace. ” zan can kenan daga zuwa sai maganar aure wai a kanki nake ne.” Granny tace.” Yo ni in a kaina kake ai da tuni ka kashe ni. Dube ka don Allah kamar zaka ji babu jiki a murd’e ai kai kam matarka zata fad’awa ‘yan garinsu.”
Gyara zaman sa yayi yana dariya kasa-kasa yasan halin kakar tasa da sakin magana ko wace iri ce ita babu ruwan ta, kafin yace wani Abu yaji tace” ka fad’amin in baka da lafiya sai in baza ma nema maka magani ko kauyen su Iyami muka je nasan za’a samo maka maganin k’arfi, ina amfanin girman jiki da k’wanji babu fus!! Uhum? Irin Ku ne matayen Ku suke shan takaici a zahiri dai gaku maza a bad’ini kuwa sai takaici.” Ta k’arashe maganar ta tsakanin ta da Allah.
Gyara zamansa yayi da k’awataccan murmushi a fuskar sa yace.” E dama na kasa fad’a miki bani da lafiya don Allah ki shiga k’auyika ki nemo min maganin k’arfi kinji.”!! Granny ta kalleshi da hankalinta a tashe tace”Yanzu kai k’ato da kana fama da wannan lalurar ka zauna sai dai kaci ka sha ka nemi kudi? Au! Ko da naji shiyasa ko wace mace aka kawo maka sai kace bata yi maka ba, tom yanzu yaya kake ji a jikinka shin kana sha’awar mace sa’i da lokaci ko A’a.”!? Granny ta tsarashi da tambaya hankalinta duk ya tashi.
Kamar gaske yace.” Kwata-kwata bana jin sha’awar mata, amma ina ganin a haka zanyi auran da kike so nayi.” Tace” innalillahi u ni ‘yasu! Amma yaron nan kaso kacuci kanta…..Iyami Iyami Iyami.!” Ta dinga kwala wa mai akinta kira.

Yace.” Nifa ba cewa nayi kiyi min taron dangi ba, uhumm ke kad’ai na fad’awa damuwa ta.” Hararasa tayi tace”Naji kana maganar zaka yi aure a haka Uwar me zaka tsinanawa matar taka, abunci da madara kawai zaka bata bukatar ta kuma waye zai biya mata.”! Cike da tuhuma tayi masa tambayar.” Dariya yake sosai yace.” Ai Irina zan auro kinga bani da matsala .”
“To baka isa ba ehe! Nima ai ina son ‘yan yara, a gaba, ni kawai zaka cuta.’!!! Tsakanin ta da Allah take maganar, Iyami ta shigo parlor da sauri take fadin” Hjy kira kike ko.”? Granny tace”Iyami zama bai kama mu ba, k’ato babu lafiya.” Iyami ta kalleshi cikin rawar baki tace”Mai gida babu lafiya Ashe? Allah ya kawo sauk’i.'” Yace.” Ameen Iyami ai tace”Zata shiga ta futa ta samo min magani.” Iyami tace”Hjy meye yake damun Shi ne.” Granny tace”Iyami je ki cigaba da aikin ki zamuyi maganar idan anjima.” Iyami ta mike da jiki a sanyaye. Kallo ya bita dashi yana kumshe dariya.
Ita kuwa granny surutai kawai take masa tare da yi masa fad’a ya zauna cuta yaci k’arfin sa, saboda yana so ya zama lusarin namiji.
Aikuwa tana tsaka da fad’an ta taga an hasko shi a TV tashar CTV kano mutane kewaye dashi yana jawabi.
Tace.” Duba ka gani k’ato dubi yanda Allah yayi maka kwarjini da daukaka ta jama’a kudi duk kana da su. OO ni! ‘Yar nan Allah kar ka jarrabe mu da abunda baza mu iya ba.” Granny ta fashe da kuka sosai! Cike da mamaki yake kallonta, ganin da gaske kukan take yasa ya rungume ta a jikinsa yana rarrashinta tayi shiru yasan ko ya fad’a mata da wasa yake ba yarda zata yi ba ganin yadda duk ta tada hankalinta yasa yace.” Granny kiyi hakuri ki daina kuka don Allah zan yi aure in haihu, ina ganin ma yanda nake jin k’arfi a jikina in dinga bada k’wayayen ‘yan biyu ko uku , ki kwantar da hankalin kinji kiyi shiru kiji wani.”Shiru granny tayi tana share hawaye tsakanin ta da Allah.
Wayarsa ya ciro daga aljuhu yace.” Bari in kira miki ita Ku gaisa.” Tace”wacece kuma”?
A hankali yace “My wifi mana.”
“Meye wifi.”? Ta tambaye shi dariya yasa yace.” Matata mana.”? Sakin fuska tayi tace” ‘yar albarka ta yarda zata aure ka da lalurar ka ko.’? Gyad’a kansa yayi kamar gaske, yana laluban numbar Mimi, sai da ya kira sau uku ba a d’auka ba, shi da in yayi kira sau d’aya baya sake wa, yau gashi yayi uku, yana shirin yin na hud’u.

Mimi na band’aki a lokacin ta kuma b’oye wayar bayan katifar mu, ina shigo wa naji ringing din waya, dube-dube nake sam ban ganta ba, in da nafi jin karar tayi yawa nan na nufa na janye pillow da ta kare wayar dashi, ina dauka kiran yana katsewa, wayar na rik’e a hannuna ina dubawa cike da mamaki! Tabbas wayarsa ce, ga k’amshin sa nan jikin wayar domin hanci na ya Riga ya gama sanin k’amshin sa.
Wani kiran ne ya shigo kamar kar in dauka sai kuma wata zuciyar tace”dauki kije abunda zai je da Mimi, dannawa nayi na bud’e speaker sosai na aje ta kan kati far. Muryar sa naji yo yana fad’in”Ungo wayar gatanan Ku gaisa, kafin in an kara Naji muryar mace, macen ma ba yarinya ba, dattijuwa me kamali. Motsin Mimi naji a tsakar gida, da sauri na k’wala mata kira ina fadin”Mimi kizo an kira wayar ki.”!!!!!!! Granny da shi kanshi uban gayyar suka yi sak! Yayi wa muryar ta farin sani saboda tana da saurin baki kuma bata kaurara murya tana da zaki don haka Ku cikin mata dubu ta shiga zai iya gane muryar ta.

Wani kiran na kara kwala wa Mimi tare da fad’in”Mimi wai ki ba kya ji ne, Habibin ki ne fa kiyi sauri kar ta katse…….. Muryar matar Naji tana fad’in” D’iyar arziki sanun ki kinji Ubangiji Allah yayi miki albarka nagode mutuka zaki auri jikana duk da lalurar da take damun sa….ko da yake naji yace.” Kema baki da lafiya, kuyi hakurin insha Allahu zamu shiga mu futa Dom……Kafin ta karasa naji yo muryar sa Yana fad’in”Nifa ba cewa nayi ki wani jawabi ba, cewa nayi Ku gaisa da My wife dina kin tsaya wani zance.”!! Ji nayi tace” Matsa ka bani guri don Allah , ai wannan yarinyar ta isa a jinin na mata saboda tayi jahadi…. Dariyar shi na jiyo Yana fadin”Sai kiyi ai.”” Ta cigaba da cewa”Allah yayi miki albarka kinji ko.” A hankali nace” Ameeen amma bani bace budurwar tashi tana band’aki ni Sunana Asma’u ita kuma Mimi in ta futo za’a..ban k’arasa ba Mimi ta shigo dakin. Nace.” Yawwa ga Mimi nan. wayar na mik’a mata na futa daga d’akin.
Kwata_kwata ban fuskanci komai ba Dan gane da maganganun da matar take,cikin zuciyata dai nake cewa”K’ila sunyi wata hira ne shi da Mimi tace mishi bata da lafiya, tom ni dai a iya sanina Mimi bata da wata cuta wacce bamu San da ita ba, asalima Mimi bata fiye yin ciwo ba, sai shekara-shekara take zazzab’in nan Wanda ake fama dashi.
Cikin zuciyata Naji tausayin ta, kuma nayi alk’awarin sai na tambaye wane ciwo ne yake damunta Wanda har ta kasa fad’ar shi a gida ta tafi waje tana yad’awa… Tsintsaya na dauka na hau share-share dama Umma bata nan taje suna sai mu kadai a gidan. Ta futo daga d’akin sai kace wata Mara gaskiya, kallonta nayi, ni yanzu tausayi take bani ganin yanda ta hada kanta da babban aiki. Sam yanzu na daina jin haushin ta, nace” Kun gama ne ” zama tayi kusa dani tare da fadin “Eh, Ashe kakarsa ce wai take so mu gaisa shine ya kira ni.” Cike da nazari nake kallonta nace”Mimi wane irin lalura ce dake da har kika kasa fad’ar ta a gida, kika fad’awa saurayi Wanda baki da tabbacin zai aure ki.”? Yanda na tsare ta da ido ina tuhumar ta sai ka rantse da Allah uwarta ce ni ko yayarta.
Cike da mamaki take kallona tace.” Ban gane abunda kike nufi ba.”? K’wafa nayi cike da takaici nace”dama baza ki gane ba, naji wannan matar tana fad’in”Zata je ta nemo miki magani dake dashi kuma kinyi jahadi tunda zaki aure shi.”
Ranta a d’an b’ace ta kalle ni tace”Kinga Asma’u ya zaki tasa ni a gaba kina min wata tambaya kamar wata uwata, ni babu wata magana da mukayi dashi. ” Nace” Ok k’arya nayi kenan.”!? Tab’e baki tayi tace”ke kika sani kuma” a hasale nace”To ki kiyaye wallahi duk inda kike tunanin wannan guy ya wuce gurin, naga soyayya ta rufe miki ido kina nema ki futa waje ki tona mana asirin gida, duk lalurar da ke damun ki nasan kika fad’awa Umma zata yi miki magani iya iyawar ta, ke da kanki Kin san kafin tayi min Abu tayi miki sau dubu me zai sa ki watsa mata k’asa a ido kije ki zauna kiyi tunani da kyau kafin kowa yasan abunda yake damun ki ita yafi kamata ta sani, amma……….Kinga Asma’u.!'” Mimi ta fada tare da D’aga min hannu a fusace ! Ta mik’e tsaye.
“Gwara ki nuna min cewar a gidanku nake zaune,Asma’u gwara kiyi min gori saboda ina zaune a karkashin inuwar Ku, amma ina so ki San wani Abu kin San dai nima ba daga sama na fad’o ba ina da Iyaye ina da dangi masu rufin asiri Ubana yana Raye a duniya sai dai kice ba a gari yake ba, tom insha Allah Allahu zan bar muku gida Asma’u kada wataran ki ce sai na biya Ku kud’in hidimar da iyayen ki suka yi min tun ina jaririya hakan ma na gode.” Dugu ta shige dakinmu tana kuka!!! Jikina ne yayi sanyi Mimi daga magana zata yi min wata fassara ta daban, tunda muke da Mimi mu kwana mu tashi guri guda bamu tab’a fad’a na cacar baki ba,ko mu fadawa junanmu munanan kalamai, nice dama mafad’aciya in taga na hau sai ta sauko ko ta maida abun wasa,Mimi bata tab’a gaba dani idan inayi ma dariya take min, tayi min magana har in gaji in sauko.
Mik’ewa nayi na bita dakin namu na tsaya bakin k’ofar shiga, ina kallonta tana ta had’a kaya tana kuka,
Babu yabo babu fallasa nace” Mimi daga magana zaki yi min wata fassara ta daban, har kike had’a kayan ki, Mimi kina da wani gidan ne bayan wannan? Baki da Uwa da ta wuce Umma kuma baki da ‘yan uwa sama damu, idan abunda na fad’a ya b’ata miki rai Allah ya baki hakuri.” Nafada ina shigowa d’akin….. Akwatin da take had’a kayan na d’auke ina fad’in”So kike yau Yaya Aminu ya kusa kashe ni a gidanan kenan? Ko so kike Umma ta tsine min.? Kiyi hakuri bazan k’ara yi miki magana irin wannan ba.”
Mimi mai saukin kai da saukin hali tace.” Kin kasa fahimta ta ne Asma’u amma na fada miki babu wata magana da mukayi dashi wai bani da lafiya, idan bani da lafiya sai kin Riga kowa sani tunda tare dake muke kwana muke tashi a daki daya.”
Domim a zauna lafiya nace”Nagane yanzu mybe shima yana tsokanar kakar tashi ne.” Ta goge hawayen ta tare da fadin ” ni ma nafi tunanin haka.” Akwatin na d’auke na mai da ita inda take, nace”Tashi mu shiga kicin kar Umma ta dawo kin ga magariba ta kusa.”
Mik’ewa tayi muka futa daga d’akin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button